Kamar yadda a kullum ba a gajiya da neman ilimi a makaranta, to haka a zamantakewar aure ma ba a gajiya da neman ilimin yadda aure zai yi karko har a samu zuri’a mai yawa kuma ingantacciya. Sau da dama a wadansu lokutan mata kan shiga tasku a gidan aure, domin sukan rasa ta yadda za su faranta ran mijinsu. Burin kowace mace a ce ta zama akalar farin cikin mijinta. Na sani an yi rubuce-rubuce kan yadda mata za su mallake mijinsu, masu iya magana sun ce tunatarwa ba ta kadan, tana kuma amfanar wanda ya yi amfani da ita. Don haka a wannan mukalar na tsakuro wa mata wadansu muhimman abubuwa 10 da za su taimaka musu wajen faranta ran mijinsu. Sau da yawa mata kan yawaita korafe-korafe a kan mijinsu, amma ba su yin wani yunkuri cikin hikima don sauya mijinsu daga wadannan halayen da suke korafi a kai ba. Ga wadannan abubuwa 10 kamar haka:
1 Jima’i:
Hanya ta farko da mata za su faranta wa mijinsu ita ce, ta bangaren jima’i. Sau da yawa mata babu ruwansu da nuna wa mijinsu suna bukatar jima’i, akwai abokina da ya fada mini ya shekara fiye da 10 da yin aure amma matarsa ba ta taba neman ya sadu da ita ba, kullum idan har suka yi jima’i to shi ne ya neme ta, hakan ya sanya ya daina jin dadin jima’in domin ba ya ganin matarsa tana shaukin jima’in, hakan ya sa ko ya sadu da matarsa ba ya jin gamsuwa. Don haka idan mata tana son ta rika faranta wa mijinta, to ta rika nemansa, idan ba za ta iya kai tsaye ba, to ta kirkiro hanyar aika dan sako. Mace za ta iya aika dan sako ta hanyar sanya tufafin mai daukar hankali, mace za ta iya aika dan sako ta hanyar kissa da kwarkwasa da kuma kisisina. Motsa gabobi ga mace kan iya tura dan sako cikin kankanen lokaci. Mata su rika ba da kansu ga mijinsu a duk lokacin da ya bukaci hakan, kada su rika azabtar da shi don ya bata musu rai, su ce tun da ya yi musu abin da ba su so, to shi ma ba zai samu abin da yake so ba. Mata su rika tarairayar mijinsu, ta hanyar nuna musu shi dan lelensu ne, hakan zai sanya shi farin ciki. Ga matan da suke aiki kada bayan sun dawo gida maimakon su lura da mijinsu sai su rika yin aikin ofis. Ko su rika korafin sun gaji. Kada su bari mijinsu ya je aiki ya dawo gida.
2 Tsabta: Mata su kasance masu tsabta, tsabtar jiki da ta muhalli. Ku rika tsabtace gidanku, kada ku bari datti ya rika kaka-gida a gidanku. Ku share ko’ina, sannan ku sanya turaren kamshi. Ku mayar da gidanku wurin da mijinku zai rika tunaninsa ko da yana wurin aiki. Ya rika dokin dawowa gida, domin ya san zai samu kwanciyar hankali da natsuwa.
3 Amincewa da bukatun miji: Ku kasance kodayaushe masu amincewa da bukatun mijinku. Ku rika tunanin wane abu ne mijinku yake so wadanda ba ku yi ba, sannan ku rika tunanin abubuwan da idan kuka yi masa zai ji dadi. Kada ku hana shi bukatar saduwa, ko kin yi masa girki mai lagwada. Idan ransa ya baci har yana muku fada ku kaskantar da kanku, sannan ku samu hanya mafi hikima wajen sanar da shi abin da ya faru. Kada ku rika daga murya idan kuna magana da mijinku zai rika jin kun raina shi. Idan har ya fahimci kuna biya masa dukkan bukatunsa to zai ji dadi a ransa.
4 Yarda da miji a matsayin shugaba:
Mata su yarda mijinsu shi ne shugaba, sannan su rika ladabi da biyayya da kuma da’a ga miji, hakan zai sanya ya rika jin farin ciki a zuciyarsa. Kada mata su manta cewa, Manzon Allah (SAW) a cikin wani Hadisi ya ce “Da zan umarci wani ya yi wa wani sujuda da na umarci mata ta yi wa mijinta sujuda.” Don haka yi wa miji biyayya kodayaushe zai sanya ya rika samun farin ciki mai dorewa a rayuwar aure.
5 Kwalliya da ado:
Kamar yadda tun a lokacin da ba ku yi aure ba, kuke rangada masa kwalliya da ado idan zai zo wurinku hira, Yi wa mijinku ado da kwalliya kafin ya dawo daga wurin aiki zai sanya shi farin ciki. Ku yi wanka, ku yi kwalliya, ku fesa turare mai kamshi, hakan zai sanya mijinku natsuwa da jin dadi da kuma farin ciki.
Mu kwana nan