✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abu hudu da za a tuna Obadiah Mailafia da su

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, malamin jami'a, dan siyasa, mai sharhi.

A ranar Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021 ne tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, ya rasu.

Mailafia, wanda ya rasu a Asibitin Kwararru na Gwagwalada, Abuja bayan rashin lafiya, ya kasance marubuci kuma mai sharhi a kan al’amura.

Ga wasu abubuwa hudu da ba za manta da shi ba:

  1. Dambawarsa da DSS

A baya-bayan nan dai Mailafia ya yi ta tashe a kafafen yada labarai tun bayan wata hira da ya yi da wani gidan rediyo kan sha’anin tsaro a  yankin Arewacin Najeriya.

Tun a watan Satumban 2020 ake dambarwa tsakanin hukumar tsaro ta DSS da Mailafia bayan wata hirar da aka yi da shi a rediyo, inda ya zargi wani gwamna a yankin Arewa maso Yamma da zama kwamandan Boko Haram.

Zargin nasa wanda ya hada da cewa ’yan bindiga suna safarar makamai  a lokacin kullen COVID-19 kuma suna hadin gwiwa da Boko Haram domin tarwatsa Najeriya, har su fara bin manyan mutane gidajensu a birane suna garkuwa da su, ya tayar da kura matuka; A kan haka ne DSS ta fara gayyatarsa, matakin da ra’ayoyi suka bambanta a kai.

Daga baya ya fito ya ba wa ’yan Najeriya hakuri da cewa ba shi da hujja kan zargin da ya yi, a kasuwar kauye ne wani wanda suka hadu ya ba shi labarin abubuwan da ya fada a hirar da aka yi da shi a rediyo.

  1. Mataimakin Gwamnan CBN:

Mailafia ya kasance Mataimakin Gwamnan CBN kuma mamba a Majalisar Daraktocin bankin daga 2005 zuwa  2007.

A matsayinsa na babban jami’i mai kula da tsare-tsaren kudade a wancan lokaci, Mailafia shi ne wanda ya jagaronci sauyesauyen da aka yi a bangaren banki daga 2005 zuwa 2006.

A lokacin shi ne babban mai kula wa CBN da  tsare-tsaren tattalin arziki da kuma bincike ta tattara alkaluma.

Bugu da kari shi ne wakilin CBN a Bankin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya da sauran hukumomin kudade na kasa da kasa.

  1. Malamin jami’a

Obadiah Malafai ya kasance malamin a jami’o’in kasanshe waje inda har shugabanci ya yi.

Shi ne shugaban farko na Sashen Cinikayyar Kasa da Kasa a Kwalejin Kasuwanci na Regents da ke Landan daga 1998 zuwa 2000.

A 1990 zuwa 1995, Obadiah Mailafia ya kasance lakcara kan tsimi da tanadi da siyasar kasashe masu tasowa a Kwalejin Plater da ke karkashin Jami’ar Oxford.

Ya zama mataimakin farfesa a 1995 zwau 1996 a Kwalejin New England da ke Arundel, kafin daga bisani ya zama lakcara a fannin kasuwanci a kwalejin kasuwanci ta Richmond karkashin Jami’ar Amurka da ke birnin Landan a 1997 zuwa 1998.

  1. Dan takarar Shugaban Kasa:

A shekarar 2019, tsohon Mataimakin Gwamnan na Babban Bankin Najeriya shi ne dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar ADC.

Sai dai bai kai labari ba, inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kayar da shi da ma sauran ’yan takara a zaben wanda shi ne na farko da aka kayar da jam’iyya mai mulki.