A gobe Asabar 4 ga Satumban bana, Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya domin sake yin amfani da wannan na’ura da aka inganta domin yin amfani da ita a zaben kananan hukumomin jihar.
Ashekarar 2018, Jihar Kaduna ta kasance jiha ta farko da ta yi amfani da na’urar yin zave ta zamani a zaben kananan hukumomi a Najeriya. Hakan ya sa Najeriya ta zama kasa ta biyu da ta cim ma wannan nasara a Afirka.
Ga abubuwa tara da ya kamata a sani dangane da wannan na’ura ta zabe da yadda ake sarrafa ta:
Da farko ita wannan na’urar zabe ta zamani an samar da ita ce domin taimaka wa wurin gudanar da zabe da kirga kuri’u a cikin sauki.
Ana amfani da ita ce ta kwamfuta da aka hada da Intanet wato na’ura ce ta EBM wanda take kididdigar kuri’u da zarar an kada su. Na’urar EVM an shirya ta ce ta yadda take dauke da akwatin ajiye kuri’a a cikinta da zarar an jefa kuri’a sai ta wuce cikin akwatin kurum.
Kowane mutum zai kada ko za ta kada kuri’arsa ko kuri’arta ne kai-tsaye a na’urar ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna, Dokta Saratu Binta Dikko-Audu, ta ce na’urar EVM an tanada ta ce domin tabbatar da ingancin zabe kuma tana da sauki a kan yin amfani da hannu wurin kirge.
Shin ko doka ta amince a yi amfani da na’urar?
Gwamnatin Jihar Kaduna a shekarar 2018 ta musanya Dokar Zaben mai lamba 10 ta shekarar 2012 da Dokar Zabe ta shekarar 2018 domin ba da damar yin amfani da sabuwar na’urar a zabe a jihar.
Sashe na 16 sakin layi (3) na dokar jihar ya bai wa Hukumar Zabe ta Jihar damar yin amfani da kowane salo wurin tantance masu zabe da kada kuri’arsu.
Dokar cewa ta yi, “Tantancewa da kada kuri’a zai kasance ne ta hanyar yin amfani da na’urar zamani da kuma katin kad-rida a yayin zabe.”
Yadda ake amfani da na’urar EVM
A lokacin da ake gwajin na’urar a ’yan kwanakin nan, Shugabar Hukumar Zaben ta ce na’urar za ta fara ne da bude shafin zaben Shugaban Karamar Hukuma ga duk wani mai kada kuri’a ya zabi alamar jam’iyyar da yake so, ko take so ta hanyar latsawa.
Daga nan hoton alamar jam’iyyar zai fadada domin mai kada kuri’a ya latsa alamar ‘eh’(ok) ko kuma alamar a’a (cancel).
“Idan ka latsa ‘eh’ (ok) a kan na’urar shi ne alamar kada kuri’arka sannan ta hagu nan wannan shafi ta inda ka latsa ko dangwala alamar jam’iyyar da ka zaba tikitin abin da ka zaba zai fito ya fada cikin akwatin ajiye kuri’a.
“Irin salon da za ka yi amfani da shi ke nan a wurin zaben kansila,” inji Dokta Audu.
Shin ko na’urar EVM tana amfani da katin PVC?
Jihar Kaduna ba ta yi amfani da katin zabe na dindindin (PVC) a shekarar 2018, a na’urar ba, sai dai a wannan karo an samar da manhaja da za a yi amfani da PVC din.
Shugabar Hukumar Zaben ta ce jami’in zabe a kowace rumfar zabe zai ba da damar yin zabe amma fa kowane mai kada kuri’a zai yi amfani ne da katinsa na PVC wurin bude shafin domin samun damar zabar alamar jam’iyyar dan takararsa.
Me zai faru a ranar zabe?
Zaben kananan hukumomin 23 a Jihar Kaduna za a yi shi ne a ranar 4 ga Satumba 2021 (gobe) kuma ana bukatar masu zabe su je rumfar zabe dauke da katinsu na PVC.
Jami’in zabe a kowace rumfa ne zai shirya na’urar a gaban wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro da masu zabe.
Dokta Saratu Binta Dikko-Audu ta ce tantance masu zabe za a yi shi ne da hannu ta hanyar yin amfani da rajista.
“Mataimakin jami’in zabe a rumfar shi zai duba rajistar zabe tare da katin zabe kafin ya shigar cikin rajistar sannan a sanya wa mutum alama a dan yatsarsa bayan ya kada kuri’arsa,” inji ta.
Kawar da shakku kan kada kuri’a fiye da daya a lokaci guda
Akwai shakku da ake samu cewa mutum yana iya kada kuri’a fiye da sau daya a lokaci guda kamar yadda wadansu suka koka a lokacin zaben kananan hukumomi a shekarar 2018 a jihar.
Sai dai Hukumar Zaben ta ce an inganta na’urar domin tabbatar da ingancin zaben ta yadda zai yi wuya mutum ya kada kuri’a fiye da daya.
Shugabar ta ce hatta alamar tawadar da ake diga wa mutum a dan yatsa za ta hana su damar sake zuwa wata rumfar domin kada kuri’a.
Ta kara da cewa “Da zarar mutum ya yi zabe na’urar za ta dauki bayanan katin zabensa.
“Don haka, za ta hana shi sake yin amfani da wannan kati domin sake kada wata kuri’ar daga baya.
“Don haka, a wannan karo mun dakile damar jefa kuri’a fiye da daya a lokacin zaben.
“Duk wanda yake tunanin zai iya amfani da katinsa wurin kada kuri’a fiye da sau daya to ya sani hakan ba zai yiwu ba. Saboda na’urar ba za ta dauki bayanansa ba,” inji ta.
Shin zaben Shugaban Karamar Hukuma ko na Kansila za ka iya yi kurum?
Idan mai jefa kuri’a yana ganin zabe daya kurum zai yi babu matsala.
A cewar shugabar abin da kurum ake bukata a wurin mai zabe shi ne ya latsa alamar a’a (cancel) da ke jikin na’urar.
“Na’urar za ta tambaye shi da gaske ba ya bukatar sake zabar wani dan takara sai ya latsa alamar ‘eh’ ko (ok) shi ke nan.
“Koda ka yi kokarin sake tura ko sa katin zabenka na PVC na’urar ba za ta ba ka dama ba. Har sai jami’in zaben ya zo tare da wani da zai kada tasa kuri’ar,” inji ta.
Yadda za a aika da sakamakon zabe
Hukumar Zaben ta ce an samar da yarjejeniya da kamfanonin sadarwa ta yadda za su inganta karfin sadarwarsu (network) a ranar zaben.
Amma idan aka samu akasin haka a ranar zabe a wasu wurare, na’urar za ta iya aijiyar sakamakon cikin kwakwalwarta har sai an samu inda yake da network sai ta aika.
Hukumar ta ce akwai wata hanyar aikawa da sakamakon zaben ta hanyar yin amfani da ‘memory’ din na’urar EVM a saka shi a filashi sai a tura zuwa ma’adana.
Dokta Audu ta kara da cewa za a iya cire takardar da aka jefa daga cikin na’urar a kirga domin samun sakamakon zaben.
Magance rikicin sakamako ko kirga
Shugabar ta ce a karshen zaben jami’in zabe a rumfar zai fito da wata takarda daga jikin na’urar da take dauke da duk kuri’un da aka kada domin bai wa duk wani wakilin jam’iyyar da ke wurin da jami’an tsaro da dukkan wadanda suke a wurin har karshen zaben.
Wannan yana nufin kowa zai samu sakamakon da ke a hannun jami’in zaben.
A inda aka samu sabani ko shakku a kan sakamakon, to ana iya bude na’urar EBM din kafin a bar rumfar zaben domin a duba a tabbatar da sakamakon ta hanyar yin kirge.