Mamallakin Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea, Roman Abramovich ya mika tayin sayen kungiyar Valencia da zarar an kammala sayar da kungiyarsa ta Chelsea.
Kungiyarsa ta Chelsea ce ta bayyana hakan cikin wani sako da ta wallafa ranar Litinin a shafinta na Twitter.
- An kama shi yana lalata da gawar buduwarsa da ya kashe zai yi tsafin kudi
- Yadda matar aure ta samu digiri mai daraja ta daya a fannin Lissafi a Jami’ar ABU
Tun cikin watan da ya gabata ne dai Abramovich ya sanya kungiyar ta Chelsea a kasuwa, biyo bayan takunkumin da Amurka da kuma Birtaniya suka kakaba masa, saboda yakin da kasarsa Rasha ta kaddamar kan makwafciyarta Ukraine, wanda kuma ake ganin yana da alaka ta kut-da-kut da shugaba Vladimir Putin.
Rahoton tayin sayen kungiyar Valencia da ke gasar La Liga da attajirin na kasar Rasha ke shirin yi, ya zo ne bayan da aka alakanta shi da yunkurin sayen kungiyar Goztepe da ke gasar kwallon kafa ta kasar Turkiya.
A makon da ya gabata, wasu rahotanni suka ce Roman Abramovich ya shiga mawuyacin hali tun bayan da gwamnatin Birtaniya ta kwace kadarorinsa a makwannin baya, sakamakon mamaye Ukraine da kasarsa Rashan ta yi.
A watan Maris da ya gabata ne Hukumar gasar Firimiyar Ingila ta tsige Roman Abramovich daga shugabancin Chelsea biyo bayan takunkuman da gwamnatin Birtaniya ta kakaba masa.