Bayan dawowar ayarin Musulmi daga wurin Sarki Rustum na Farisa, sai ya zamo babu wata mafita face gwabza yaki. Ga shi kuma rundunar Farisawa tana da mayaka masu dimbin yawa da kayan yaki da kuma dadadden tarihi na kwarewa a yaki. A daya bangaren kuma ga Musulmi lullube da imani kowa yana kwadayin ya yi shahada, ga su jarumai kuma gwanayen yaki domin rayuwarsu ta sauya tun daga bayyanar Musulunci. Don haka babu abin da yake gaban rundunar Musulmi illa ko su yi shahada ko su ci nasara domin daukaka addinin Allah. Allahu Akbar!
Daga nan sai yaki ya kankama inda aka fafata yaki har tsawon kwana hudu, kuma kowace rana tana zuwa da salonta da kuma matsalolinta. A farkon yakin dai Sa’adu yana cikin lalurar rashin lafiya. Wannan rashin lafiya ta hana shi shiga yakin tsundum har ba zai iya ba su gudunmawa mai girma ba, sai ya hau rufin wani gida yana ba da umarni gwargwadon hali, wato yana gwada musu dabarun yaki. Rana ta farko ta kasance mai matukar wuya ga Musulmi, inda Farisawa suka rika samun galaba a kansu, saboda suna amfani da giwaye masu karfi da suka ci nasarar kutsawa da su cikin ayarin dawakin Musulmi inda hakan ya sa dawakin suka razana matuka.
Amma a rana ta biyu, lamarin ya sauya, inda nasara ta fara karkata ga Musulmi. Rundunar Musulmi ta rika harin idanuwan giwayen da mayakan Farisa ke haye a kansu, tana harbin idanuwan da kibiya. Kuma suka dage suka karya kandagarkin da mayakan Farisawa suka yi don fakewa suna kai hari ga Musulmi. Wani dalilin nasarar da Musulmi suka samu shi ne karin gudunamwar mayaka da kayan yaki daga Umar (RA) da ya turo daga Madina. Sababbin mayakan kuwa suna karkashin dan uwan Sa’adu ne da ake kira Hashim bin Utbah bin Abu Wakkas da kuma Alka’ka’a bin Amir daya daga cikin mayaka masu jarumtaka a rundunar Musulmi, (Allah Ya yarda da su). Saboda jarumtar ka’a’ka’a bin Amir (RA) har ma Sayyidina Abubakar (RA) wata rana ya ce, duk rundunar da ta kunshi Alka’aka’a bin Amir insha Allahu ba za a samu galaba a kanta ba. Shi ne kuma ya taryi wani daga cikin shugabannin rundunar Farisawa da ake kira Haris bin Sabi’an, nan da nan kuma ya gama da shi.
A rana ta uku ma dai an ci gaba da fafata kazamin yaki a tsakanin bangarorin biyu, kuma kamar yadda sakamakon yakin ya fara nunawa sai taimakon Allah sa’annan da jarumta da kyakkyawan tsari na ayarin Musulmi ya kai su ga nasara. Jagororin mayaka irin su Alka’aka’a da Amir bin Madi Kharab da kaisu bin Makshun (RA) suka yi matukar nuna jarumta. An kuma ci gaba da fafatawa har cikin daren kwana na hudu na wannan yaki.
A rana ta karshe, an wayi gari da yanayi na iska, sai aka dace wani Musulmi ya hango Sarki Rustum na Farisa da kansa a kan wata giwa yana ba da umarni ga mutanensa ana ta yaki, sai Musulmin nan ya auna idon giwar Sarki Rustum ya dirka mata kibiya. Nan da nan ta yi kasa ta fadi da Sarki Rustum, Hilal bin Kamah (RA) wanda yake kusa da shi, sai ya yi maza ya raunata Rustum kuma nan take ya mutu.
Mutuwar Sarki Rustum ita ta bude kofar samun gagarumar nasara. Mayakan da suke tsoron Sarki Rustum wadanda kuma a yanzu ba su wuce mutum dubu hudu da suka saura ba, sai suka nemi sulhu, suka kuma bayar da sharudda biyu na mika wuya ga Musulmi. Wadannan sharudda su ne a bar su su yi yarjejeniya da duk wanda suke so, sannan Musulmi su rika biyansu albashi mai yawa domin su yi yaki. Sa’adu (RA) ya amince da wadannan sharudda a matsayinsa na jagora, wannan ya sa rundunar tsaron Sarki Rustum suka karbi Musulunci. Haka kuma wata runduna da aka daure cikin sarka domin kada su gudu daga filin yaki su ma suka mika wuya ga Musulunci. A nan aka mayar da sauran mayakan Farisa fursunonin yaki, sauran kuma suka tsere. A wannan fage Farisawa sun yi asara mai yawa wadda ta zartar asarar mayaka dub bakwai da Musulmi suka yi a wannan yaki.
Umar (RA) ya samu labarin nasara:
Bayan kawo karshen yakin kadisiyya inda Musulmi suka samu gagarumar nasara, sai Sa’adu (RA) ya rubuta wa Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (RA) labarin wannan nasara da aka ci. A cikin wasikarsa Sa’adu ya ce: “Allah Ya taimake mu mun samu nasara a kan abokan gabanmu. Wadanda suke da mayaka masu yawa da tarin kayan yaki. Sun hadu da abin da ya cancance su. Musulmi sun yi musu kofar rago sun samu nasarar korarsu cikin hamada. Musulmi dai sun samu gagarumar nasara, koda yake sun yi asarar wadansu daga cikin manyan jarumansu. A filin yaki Musulmi suna karatun Alkur’ani cikin dare, sannan da rana suna ci gaba da fama. Ba za a ce wadanda suka rasu sun fi wadanda suke raye yanzu ba, face alfarmar shahada da suka samu.”
’Yar Nu’uman bin Munzar ta zo ga Sa’adu:
’Yar Nu’uman bin Munzar wadda babanta shi ne Sarkin Al-Hara abokan tarayyar Farisawa, sai ta zo ga Sa’adu bayan gama yakin kadisiyya. A lokacin da ta shige zuwa wurin Sa’adu sai ya ga alamu fatara da galabaitya sun lullube ta. A da kuwa tana cikin daula ga zinari da azurfa da siliki kewaye da ita. Saboda haka a lokacin da ta gabatar da kanta ga Sa’adu (RA) sai ya tuna wani zance na Manzon Allah (SAW) inda yake shawartar Musulmi cewa idan suka ga mutumin da a da yake cikin wadata da alfarma ya koma cikin kunci da wahala to su kyautata masa. Don haka sai Sa’adu ya yi mata kyakkyawar tarba kuma ya yi mata kyauta mai yawa. Daga baya aka tambaye ta game da irin karbar da Sa’adu (RA) ya yi mata, sai ta amsa da cewa ya kyautata mata kwarai da gaske.
Sa’adu ya dangana har zuwa Madd’in:
Bayan kammala Yakin kadisiyya, Sa’adu ya so Musulmi su dan sarara su huta domin sa samu damar yin jinyar raunukan da suka samu. Amma a daya bangaren mayakan Farisawa da suka tsere sai suka sake tattaruwa a gabas da Kogin Tigris (Tikiriti) da ke Irak a yau. Wani Bafarise ne aka samu labarin ya tattara mayaka masu yawa tare da yin tsare-tsaren yadda za a yi yakin Madd’in. Wannan shiri ya dauki dukan bangarorin kimanin shekara biyu suna yi.
Musulmi sun kira wannan wuri da Madd’in ne saboda ya tattara garuruwa bakwai wadanda suke kusa da juna, amma kuma ba gari daya ne kamar yadda suke zato ba. To bayan Sa’adu ya kammala dukan shirye-shiryensa na yaki, sai ya dakata domin jirar umarnin Khalifa Umar bin Khaddabi (Allah Ya kara masa yarda). Daga samun wannan umarni kuma sai Sa’adu ya auka wa mayakan Farisawa da yaki bayan ya kira su zuwa ga Musulunci sun ki.
Ya fara da bangaren Yamma na kogin ya kuma samu nasarar fatattakarsu. Sai dai lokacin da suke tserewa sai mayakan Farisawan suka karya gadar da suke ketarewa ta kanta zuwa daya bangaren domin hana Musulmi tsallakawa zuwa gare su. Sai Sa’adu ya dakata na dan wani lokaci domin shirya hanyar da za a iya ketarawa zuwa ga abokan gaba. Daga karshe dai aka samu wuri marar zurfi sosai aka yi shawarar haurawa ta wurin, kuma maimakon a haura gaba daya, sai Sa’adu ya zabo jarumai aka kasa su gida biyu domin tunkarar wannan aiki mai matukar kasada. Wadannan jarumai ne suka sadaukar da kawunansu domin ceton sauran Musulmi.
Sa’ad (RA) ya nada Assum bin Amru ya jagoranci runduna ta farko, yayin da ya nada Alka’aka’a ya jagoranci runduna ta biyu. Wadannan rundunoni biyu sun samu nasarar tsallake kogin a kan dawakansu, kuma dawakan sun haura kogin ne tamkar suna tafiya a doron kasa
A lokacin da mayakan Musulmi suka tunkari mayakan Farisawa, sai suka ji matukar tsoro. A nan ne jagoransu mai suna Yazdijir ya samu nasarar tserewa da sauran jama’arsa bayan sun debi abin da za su iya diba na kayayyakinsu, inda suka gudu.