✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin kunya

Wata rana a wurin aiki ne na ci wake mai yawa fiye da kima. Da na koma gida sai mijina ya tarbe ni da murna,…

Wata rana a wurin aiki ne na ci wake mai yawa fiye da kima. Da na koma gida sai mijina ya tarbe ni da murna, ya ce mani: “Abar kaunata, yau zan ba ki mamaki da daren nan, a wajen cin abinci.” Don haka sai ya samo kyalle mai duhu ya daure mani idanuwa, ya jagorance ni zuwa kan kujerar teburin cin abinci, ya zaunar da ni. Har ya kama kyallen zai kwance mani ido, sai wayarsa ta kada. Sai ya ce bari ya tafi ya amsa wayar, idan ya dawo zai kwance mani daurin kyallen idona. Ina zaune sai cikina ya fara murdawa, domin kuwa waken da na ci ya bata mani ciki. A tsammanina, tun da mijina bai kusa da ni, sai na karkace kafa daya na burka tusa mai kara kuma mai dan karen wari. Na dauki hankici na fara fifita saboda warin ya kau da sauri, kafin mijina ya dawo. Cikin nawa ya sake rudewa, sai na saki jiki na burka tusa har sau uku kuma masu kara da wari, fiye da ta farko. Babu abin da nake sauraro sai muryar mijina daga nesa yana ta magana a waya. Ni kuwa domin in samu sauki sai na yi ta sakin tusa ba kaukautawa, ina jin dadi sosai, cikina yana washewa. Da na ji mijina ya gama magana a waya kuma yana shirin dawowa wajena, sai na ci gaba da fifita, domin in kori warin tusar da na yi ta burkawa. Da ya dawo sai ya ba ni hakuri, ya ce mani: “Ina zaton dai ba ki bude idonki ba tun da na tafi.” Ni kuwa na ce ban bude ba ko kadan. Daga nan mijin nawa ya kwance mini kyallen idona. Abin mamaki da kunya, sai na ga abokan mijina su bakwai a zazzaune a kujerun gaban teburin abinci. Sun tottoshe hancinansu da hankici saboda warin tusa ta!”
Daga Zainab Usman