✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da zai faru a zaben dan takarar shugaban kasa na PDP

Mutum 14 ke zawarcin tikitin takarar shugaban kasa a PDP.

A ranar Asabar, 28 ga Mayu, 2022 babbar jam’iyyar adawa a Najeriya take fara gudanar da zaben fitar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023.

Kuna iya latsa nan don shiga shafinmu na kai-tsaye domin samun bayani dalla-dalla kan wainar da ake toyawa a wurin taron na PDP.

Tuni dai zababbun daliget da za su jefa kuri’a da kuma manyan baki suka fara isa wurin babban taron na kwana biyu da ke gudana a Filin Wasa na Kasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

’Yan kasuwa da masu goyon bayan ’yan takara ma ba a bar su a baya ba, inda suke ta baje hajojinsu na kayan sayarwa da allunan tallan ’yan takara a wurin taron.

A wannan karon, zababbun daliget, mutum 811, ne kadai za su kada kuri’a a zaben da mutum 14 ke zawarcin tikitin takarar.

Zababbun deliget din sun kunshi mutum daya daga kowacce daga kananan hukumomin Najeriya 774; sai kuma daliget na musamman (nakasassu) 37, daya daga Birnin Tarayya, Abuja, da kuma daya daga kowacce daga jihohin Najeriya 36.

’Yan takara

Masu neman takarar shugaban kasa jam’iyyar sun hada:

  1. Tariela Oliver, wadda ita ce kadai mace da ke zawarcin tikitin
  2. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar
  3. Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki
  4. Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim
  5. Gwamnan Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal
  6. Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohmmad
  7. Gwamnn Jihar Ribas, Nyesom Wike
  8. Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanel
  9. Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose
  10. Mawallafi kuma Attajiri, Cif Dele Momodu
  11. Charles Ugwu
  12. Chikwencdu Kalu
  13. Sam Sam Ohabunwa
  14. Mohammed Hayatu-Deen

Sai dai a safiyar ranar Asabar, Hayatu-Deen ya sanar da janyewarsa daga neman tikitin jam’iyyar.

Bisa yadda aka saba, akan jefa kuri’a a zaben ne jiha bayan jiha a jere, daga harafin A har zuwa harafin Z.

Gabanin gudanar da taron dai, jam’iyyar ta sha dage shi, kafin daga bisani ta yanke hukuncin gudanar da shi a ranar 28 zuwa 29 ga watan Mayun da muke ciki.

Kafin nan an yi fama da turka-turkar kan yankin da jam’iyyar za ta bai wa takarar a zaben 2023, wanda daga bisani ya ce duk mai su ya shiga, kowa farin jininsa a fisshe shi.