Alhaji Is’hak Sarkin Fulanin Dankama da ke cikin karamar hukumar Kaita a jahar Katsina tsohon malamin kiwon lafiya ne wanda ya samu kansa a cikin harkar rubuce-rubucen littattafai musamman a harshen Hausa, har ya kai matsayin mataimakin shugaba na kungiyar marubuta ta ANA reshen jahar Katshina. Ya gaya wa Aminiya yadda ya fara wannan tafiya mai tarihi.
Aminiya: Makaranta za su so su san takaitaçen tarihinka?
Is’hak: Nidai an haife ni ranar 28 ga Febrairu na 1956 anan cikin garin Dankama. Na shiga makarantar firamare anan Dankama daga 1963 zuwa 1970. Daga nan sai na tafi Sakandire ta Alhudda-hudda dake Zaria a 1972-73 inda na dawo nan Katsina a GCK na kammala daga 1973-76. Daga nan sai na shiga makarantar koyon aikin jiyya ta Katsina daga 1977-80, sai kuma ta Kashi dake Dala ta Kano inda na samu kwarewa a fanni aikin gaugawa da hadari a 1985. Na zama jami’in kiwon lafiya tun daga karamar hukumar Katsina har naje a jaha a Kaduna har na kai ga na kasa kafin daga bisani na ajiye aikin.
Aminiya: Me ya baka sha’awar rubuce-rubucen Hausa?
Is’hak: Tsari ne na Allah. Tun ina firamare na fara sha’awar rubutu kuma na fara. Banda karatun da nayi na Hausa a firamare ba inda na yi karatun Hausa. Tun a wancan lokacin na cigaba da rubutun littattafai saidai ba kan ka’ida suke ba, saboda bansan ka’idar rubutun Hausa ba a wancan lokacin. Sai dai duk abin da aka gyaramin shikenan na rike.
Aminiya: Yaya zaka bayyana marubuci?
Is’hak: Kamar yadda mutane suka sani kowane marubuci akwai irin hikima da fasaha da kuma bukatar da yake so ya biya kan wannan fanni na rubutu. Wasu zaka ga fannin soyayya suke na su rubutun, wasu jarumtaka, wasu kuwa akan wakoki suka fi mayar da hankalinsu da sauransu. Dukkansu dai darasi ne da wani sakone suke so su isar ga jama’a kamar yadda mawaki yake isar da sakonsa ta hanyar waka. To na dauki marubuci a matsayin mai fadakarwa, nishadantarwa da kuma ilmantarwa.
Aminiya: Kai ina kafi mayar da hankali a naka rubutun?
Is’hak: Gaskiya ni nafi mayar da hankalina akan al’amurran da suka shafi rayuwar Bahaushe. Wadanda suka hada da al’adunshi da dabi’unshi da gine-ginanshi da duk wasu abubuwa na da suka shafeshi. Ganin cewa zamani yazo wadannan abubuwa an riga an fara watsi da su komin kyansu, a wasu lokuttanma kyamarsu ake yi. Shine nake so inyi anfani da wannan dama in bayyana su ta hanyar littattafai. Yanzu misali, in ba Fada kaje ba mutane da yawa acikin gari in kace su gaya maka sunayen babbar Riga sai kaga basu sani ba, kai hatta wasu dattawanma da zaka yi zaton sun sani sai ka taras kawai babbar riga suka santa da ita. Wanda yayi kokari ne zaice yasan Aska biyu ko hudu ko kuma yace tara. Akwai kuwa kalar babbar Riga akalla tafi kala goma sha uku. Kaga akwai Shafka,Windiya, Sace,Tsamiya, Mai asake da sauransu. Kuma har yanzu wadannan tufafi suna nan ana amfani da su a Fada, musamman gidan Sarki inda ake fi amfani da su.
Aminiya: To akwai wani abinda ya bambanta su?
Is’hak : Kwarai kuwa! Yanayin aikinsu ne ya bambanta su. Misali, Shafka. Ita aiki ne ake yi mata har kasa a gaba da baya. Wundiya kuwa babbar riga ce amma aikinta yanada wannan alamar “b”, tanada aljihu guda biyu a gicce, wato bangaren dama da hagu, akwai su da yawa. Haka Wando, akwai Tsala da Tumazagi, amma mafi yawan mutane a yanzu basu san sunayensu ba musamman matasa. Ganin yadda yadda ake kokarin barin irin wadannan abubuwa ne suke kokarin bacewa Bahaushe, shi yasa na dauki wannan fanni a wajen rubuce-rubucen da nike yi.
Aminiya: Kusan duk misalan da kabada sun tsaya ne a Fada bayan al’adar Bahaushe ba a Fada kadai ta tsaya ba.
Is’hak: Ba a Fada kadai ta tsaya ba. Misali, akwai wani littafi da na rubuta Jikkar Magori mai dauke da baituttuka 12. Baiti na farko na rubuta sunayen abincin Hausawa har kala 100. In kace Shinkafa ba abincin Bahaushe bace, amma da Tuwo, Waina, Kosai, danwake da sauransu sune abincin Bahaushe. Da yawa yanzu in kace,’Yarkumbu ko Danbagalaji kai koda Tuwon ruwa wasu basu sansu ba. Duk wadannan abubuwan suna neman su wuce sai in kaje cikin kauyuka kuma na nesa.
Aminiya: Ta yaya kake samun sanin wadannan tsofaffin sunaye da suke neman bata?
Is’hak: Wallahi zumma ce da kuma daukarwa rai. Ina da sha’awar abin don haka yasa duk wahalarsu bani ganinsu. Kamar littafin da nike cewa na rubuta na Kaura Ama sai da nayi tafiya har zuwa Agadas don neman bayani akan shi. Ni guri na in bada gudunmuwata ga al’adar rayuwata ga wannan zamanin na yanzu da na gaba mai zuwa. Daukarwa rai ne kawai, ba wani ya sanya ni ba,ba kuma wani ke biya na ba.
Aminiya: Kenan ka yiwa al’adar Bahaushe kyakkyawar fahimta
Is’hak: Kwarai da gaske. Al’adar Bahaushe tana da fa’ida sosai. Misali, na sani da wayona ina gani sai a tashi daga wannan garin a tafi zuwa wani garin, kamar ace daga Katsina a tafi Charanci ko wani garin domin karbo kudin Shara. Kuma ana yin haka ne ba don talauci ba, saidai don ita wannan karbar kudin Sharar wata hanyace ta sada zumunci. In kaje gidan dan-uwanka wajen karbarta har kwana ma sai kayi don ka karbi Shara. Kana ma iya kama shi ka daure in kafi shi karfi a kuma gaban diyansa da jikoki wanda hakan zai basu damar sanin wanene wannan? Ba kuma ci masa mutunci kayi ba ko don abin shi a’a, an fake da wannan Shara ne don ayi zumunci.
Aminiya: Menene Shara?
Is’hak: Ma’anar Shara wata diyya ce da ake biya a al’adar Bahaushe a tsakanin dan-mace da dan-namiji na wasa don a alakanta dangankatarsu. Mai kuma amsarta shine, dan-mace duk da cewa kowanensu zai iya bayarwa. Amma saboda nuna mafi rinjaye dan-namiji ne yafi ba dan-mace.
Akwai wani abin na al’adar ta sada zumuncin, wato zuwa wajen biki ko sabga. Za’a tashi daga Dankama ace zuwa Malunfashi, za’a kuma tafi da yara tare da Goran ruwansu, saboda wancan lokacin tafiyar kasa ce ake yi, akwana nan a yini nan. Kuma duk lokacin da ruwan goran ya tafi karewa ana zuba wasu saboda kasan yaro bashi da jimirin kishirwa. To a haka har aje gidan da ake wannan biki da kuma sauran ruwan nan na cikin gora. To wannan sauran ruwa shi za’a rika tarfawa kodai acikin Koko ko Ludayi ana rabawa sauran dangi suna kurbewa ba wai don maganin kishirwa ba, a’a, wannan ruwa da aka zo da shi shine bahashe yake kira da Ruwan Zumunci. Kuma wani abin alfahari ne ga al’adar Bahaushe.
Aminiya: Ya maganar Mu’amullar Bahaushe a rutudunka?
Is’hak: A da in kana da aboki yana da iko da ‘ya’yan da ka haifa. Yana iya cewa diyar da ka haifa ya ba wane kuma ta bayu. To yanzu kuwa ba aboki ba kai kanka da ka haifa baka da ikon cewa yarinya ga wanda ka bata. Kaga wadancan al’adu duk an janye su. Da in kaga yara suna fada ba tare da sanin ko na ina ne ba zaka bashu kashi akan wannan fada da suka yi don gobe kada su kara, iyaye in sunji labari su zo suyi maka godiya saboda ka aza yaran bisa turba mai kyau, yanzu fa, hakan na yiwuwa? Kaga dukkan wadancan abubuwa mu’amulla ce ta tarbiya wadda Bahaushe ke yi.
Aminiya: Ga al’alda, yaya dangantakar Bahaushe take ga saura
Is’hak: To ga al’ada ta Bahaushe kowa nashi ne, saidai in ka kyamaci kanka. Ka lura, mu dauki Inyamurai ko Yarabawa, yadda suke jin dadin zama da Bahaushe basu jin haka da ‘yan-uwansu. Bahaushe yana da karamci bisa ga al’adarshi. Amma in ba cutarshi kayi ba har ya gane to baya kyamar kowa.
Aminiya: To menene kake ganin ya jasa gushewar duk wadannan al’adu da dabi’un na Bahaushe?
Is’hak: Alhamdulillahi! Abinda ya jasa gushewarsu wani abu ne da aka yi na son zuciya da ake cewa zamani!zamani!!zamani!!! Komi kayi magana sai ace zamani ne yazo, wanda wannan abin an wuce shi. Misali yanzu, kaga zowan Bature ya kawo Keke, Mota harda Jirgin sama. Amma duk da wannan wadatar yau in aka ce salla ce Sarki dole sai ya hau Doki koda kuwa babu shi a kusa sai an nemo shi koda kuwa da rance ne.
Amma dubi yadda matasanmu suke yi, wai irinsu doguwar riga sai ga dattawa. To in ba’ayi hankali ba, za’a wayi gari su ma dattawan sun bijire sun koma ga wadannan kananan kayan. Kaga komin zaka ce zamani ai sai ka duba shin abinda ba naka ba yaushe ne zaka yi alfari da shi?
Ba zan manta ba an taba gayyatata a jahar Ananbara a jami’ar Auka za’a karrama ni, aduk taron ni kadai keda manyan kaya na Bahaushe, sai na zamo abin kallo. Wasu na burge su wasu kuwa suna ganina tamkar mahaukaci sadoda har Rawani nayi. Har wani Furofesa yayi mani tambaya akan hakan, nace dukkan taron nan babu wanda yayi shiga irin tawa yaya kuwa za’ayi inyi irin taku?
Aminiya: Me ka amfana da shi wajen wannan rubutu naka?
Is’hak: Gaskiya Alhamdulillahi domin naci riba fiye da tunanina. Farko dai nasan jama’a, inda ban iya zuwa ko yin magana da wasu, hanyar rubutu ta sa duk nayi wadancan abubuwa. Kai ba wai anan cikin gida ba hatta da waje irinsu Ghana, Kamaru da Nijar duk muna mu’amulla da juna ta hanyar wadannan rubuce-rubuce. Ga kungiya kuma wadda muke da ita ta marubuta kuma har mukami na rike a kungiyance don nayi mataimakin shugaban kungiyar a matakin jaha na tsawon wani lokaci.
Aminiya: Menene kake gani yakamata marunuta suyi la’akari da shi a yanzu?
Is’hak: To kaga dai kamar ni akida ta, ina so in jawo hankali akan yadda za’a sake farfado da al’adu na Bahaushe. Kasancewar babu inda zaka je kayi yekuwa shi yasa ta hanyar wadannan rubuce-rubuce na litattafai da kasidu nike ganin zata yi tasiri a wajen isar da sakonnin da mu marubuta muke so mu isar.
Aminiya: To akwai rawar da kake ganin gwamnati zata iya takaw a nana?
Is’hak: Gwamnati ce kau yakamata ta dauki nauyin wadannan abubuwa. Misali, akwai litattafai da ni kaina na rubuta wadanda kudin bugawar sunyi tsaye, kuma akwai irina da dama wadanda koda naira dubu dari aka ce su biya a buga littattafansu ba su da su, amma inda gwamnati zata rika bin irin wadannan littattafai tayi nazari akansu wadanda a karshe in taga amfaninsu musamman ga makarantu sai ta gurza su ta rarraba. Shi kuma marubuci a bashi abinda ya kamata a bashi na wahalarsa. A rika yin haka ka gani in ba’a cigaba ba dubi misali da littafin Magana jari ce, yanzu ina wanda ya rubuta littafin?