✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da yake tsakanina da Hadiza Gabon – Naziru

Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka, yana daya daga cikin fitattun mawaka a duniyar wakokin Hausa, a tattaunawarsa da Aminiya…

Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka, yana daya daga cikin fitattun mawaka a duniyar wakokin Hausa, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana dalilin da ya sa ya fara waka, kalubalen da yake fuskanta da kuma batun soyayyar da ke tsakaninsa da shahararriyar jaruma Hadiza Gabon. Ga yadda hirar ta kasance:                                  

Ko me ya ja hankalinka har ka fara waka?

Babu wani abu takamaimai da zan ce shi ne abin da ya sanya na fara waka, amma dai abin da na sani shi ne, na fara waka tun ina dan shekara bakwai, a lokacin da na fara waka babu dakin yin kidan waka a Kano. A lokacin ina yin wakoki a gaban mutane ne, wato yayin lokutan taruka. Ko a lokacin ina tuna yadda mutane suke cewa ina burge su. A haka na ci gaba har na kawo yanzu da mutum ba zai iya kirga adadin dakunan kidan wakoki a Kano ba.

A wani lokaci za a ce ka fada harkar waka gadan-gadan?

Na fada harkar waka gadan-gadan ne a shekarar 2000, inda a yanzu komai za a iya cewa ya zama tarihi.

Akasarin wakokinka sun shafi na sarauta ne ko ga attajirai, inda suke salo da irin na marigayi Shata, wadansu kuma irin na dan kwairo, ko me ya sa ka dauki irin salon wadannan mawaka?

Na lura cewa mawaka ba sa son yin wakoki irin na wadannan mawaka da ka ambato, inda hakan ya sanya ire-iren wakokinsu suke neman bacewa. Amma a zahirin gaskiya irin wakokinsu suna da matukar wahala, ba wai na ce kwata-kwata ba a irin wakokinsu ba ne, amma duk wanda ya yi irin wakokinsu zai san cewa lallai ya yi waka, domin irin wakokinsu suna da wahala, dalili kuwa wakokinsu ba irin kowace waka ba.

Ga shi yawancin wakokinka ga attajirai ko masu sarauta kake yi wa, ko yaya dangantarka take da wadanda kake yi wa wakoki?

Ina da kyakkyawar dangantaka tsakanina da su, yawancin mutanen da na yi wa waka ma za ka samu akwai sanayya ko alaka tsakanina da su, sannan ba na kiran su in rika rokonsu, wato in rika cewa a yi mini wannan, ko a yi mini wancan.

 Ba wai na ce ba sa yi mini ba ne, amma dai su da kansu suke ganin ya dace su yi mini abu, ba wai in roke su ba. A gaskiya ba na rokon mutanen da na yi musu waka kudi ko wani abu, amma idan sun ba ni ina farin ciki, kuma in gode musu, ina yi musu godiya har a cikin waka, za a ji na ce an ba ni kaza da kaza.

Abin da nake so mutane su sani ma shi ne, ba na yi wa mutum waka face na san mutum, na san halayensa, na san abubuwa da dama a kansa, haka kawai wai wani ya ce in yi wa wani waka ba tare da na san mutum ba, to ba na yi, ko an ce in yi wa mutum waka ma, sai na yi bincike a kansa, domin duk abin da zan fada a waka idan an bincika to a samu gaskiya ne.  Yawancin wadanda nake yi wa waka wadansu sun dauke ni dan uwansu, ko kuma dansu. 

A hasashenka kana ganin ka yi wakoki kamar nawa?

A gaskiya na daina kirga yawan wakokin da na yi, don haka ba zan iya cewa ga adadin wakokin da na yi ba, amma idan hasashe aka ce in yi, to zan iya cewa ina da wakoki kamar 300. 

A cikin wakokin da ka yi zuwa yanzu, wacce ka fi so, kuma me ya sa?

Na fi son wakar ‘dan Adalan Mubi’ da kuma ta ‘Sardaunan Dutse’, saboda duk abin da aka ji na fada a wakokin to na gan su, wadansu kuma na ji su. 

A kwanakin baya an ji ka yi wa Gwamnan Jihar Kano waka, inda haka ya sauya daga irin jigon wakokin da kake yi, wato na sarauta ko ga attajirai, ko me ya kawo hakan?

Batu na gaskiya shi ne, bai kamata mawaki ya tsaya da salo daya kawai ba, ya kamata ya rika sauyawa daga lokaci zuwa lokaci, hakan ne zai sa ya zama cikakken mawaki. A wannan kokacin zan mayar da hankalina ga wakokin siyasa, kuma a yanzu na fara da Ganduje ne, inda saura za su biyo baya, amma zan yi wakokin siyasa ba tare da cin mutunci ko kazafi ba. 

Ina batun jita-jitar da ake yadawa cewa Ganduje ya ba ka miliyan 50 tukwuicin wakar da ka yi masa?

Wannan ba gaskiya ba ne, jita-jita kawai mutane suke yadawa, ba ta da tushe ballantana makama, na dai san mun zauna da wakilan Gwamna Ganduje mun yi yarjejeniya cikin sirri, ni dai ba zan bayyana abin da aka ba ni ba, domin yarjejeniyar ba ta ce haka ba. Amma idan daga bangaren Gwamna sun bayyana ni dai ba zan bayyana ba. 

A yawancin hotunanka za a gan ka dauke da gashi mai yawa a kanka, ko hakan yana taimaka maka da basira wajen waka ne?

Ko kadan ba haka ba ne, tara gashi a kaina ba shi da alaka ko taimaka mini da basira wajen wakokin da nake yi. Sai dai a zahirin gaskiya ba ni da isasshen lokaci, yawancin za ka same ni ina aiki, ko halartar taruka, inda hakan ya sanya ba na samun lokacin wajen zuwa aiki, ko kuma samun lokaci don mai aski ya zo gida ya yi mini aski, hakan sai kawai na yanke hukunci tara gashi, hade da kuma gyara shi. 

Duk da shaharar da ka yi da kuma nasarorin da ka cimma, zuwa yanzu wadanne kalubale kake fuskanta?

kalubalen dai bai wuce yadda kabilarmu ta Hausa suka saba yi ba, wato martaba wani na waje fiye da na su na cikin gida ba, a Arewa an fi daukaka baki, hakan ne ya sa ake yi wa mawaka wani irin kallo, wasu ma suna yi mana kallon mutanen banza ne, ko wadanda ba su da ilimin addini, inda hakan ya sa ake mana mummunan kallo, duk da cewa a yanzu irin mummunan kallon da aka yi mana ya ragu, amma dai har yanzu muna fuskanta wannan kalubalen.

Na yarda ni mawaki ne, to sai me? Na aikata babban alkabi’i ne? Ban yi zina ba, ban yi sata ba, ban yi shirka ba, amma duk da haka ana yi mini mummunan kallo, wannan ba adalci ba ne.

Wani lokaci ko yanayi ne ka fi so don rera waka?

Ba ni da wani takaimaman lokacin da na fi jin dadin rera waka, kowane lokaci zan iya waka. Wani lokaci ma idan har an yi kidan waka, to ba na daukar fiye da minti 30 na kammala wakar, wani lokaci kuma nakan yi kwanaki kafin in kammala waka, wani lokaci ma ina cikin aiki, idan na ji wakar ba ta yi mini yadda nake so sai in fita daga dakin kidan waka. Amma ka ga wakar Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi mai suna ‘Mata Mu dau Turame’ ba ta dauke ni fiye da minti 30 na kammala ta ba, kuma ka ga yadda ta yi tashe. 

Ko kana da wani shiri na komawa da akalarka ga wakokin fina-finan Hausa a nan gaba?

Ba ni da wani shiri har yanzu, amma idan za ka iya tunawa a baya na yi wakoki ga fina-finai irinsu ‘Wani Gari’ da sauransu, duk da cewa yin wakokin fina-finai ba salona ba ne, zan iya yin waka a fim, amma sai na tabbatar da ingancin fim. Ina so in yi waka a babban fim wanda ya kunshi babban kasafi, labari mai karfi da inganci da kuma fitattun jarumai. Ina da tsari ba kowane irin biri da gadar fim zan yi waka a cikinsa ba, domin idan na yi hakan kamar na watsar da basirata a banza ne. 

Wane abu ne yake sanya ka farin ciki idan an zo batun harkar waka?

Nakan ji dadi idan wakata ta fadakar, ta nishadantar, ta kuma wa’azantar ko ta fa’idantar da masu sauraro. 

Abin da yake sa ka bakin ciki fa?

Shi ne mutane su rika saba wa Allah, kiri-kiri suna ganin abu ya dace, amma su kekasa kasa su rika aikata mummunan aiki. 

Me za ka ce dangane da jita-jitar da ake yadawa cewa an sa ranar aurenka da fitacciyar jaruma Hadiza Gabon?

Gaskiya muna soyayya, kuma muna son juna, tana da kirki da tausayi, sannan tana kyautata wa mutane musamman ma na kasa da ita. Mutum ba zai ce ya yi asara idan yana soyayya da ita ba. Amma a zahirin gaskiya ba a sa ranar aurenmu ba, komai na Allah ne, idan Allah Ya kaddara za mu yi aure, to babu makawa sai mun yi auren, amma a yanzu dai ba mu kai ga batun sanya ranar aure ba.