Dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna a zaben 2019 Isa Muhammad Ashiru ya ce dole gwamnati ta tashi tsaye domin shawo kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Ashiru ya yi kira ga gwamanatocin jiha da ta tarayya da su cika alkawarin da suka dauka na kare rayuwa da dukiyoyin al’umma.
“Asarar rayuka da dukiyoyin al’umma ta yi yawa a Arewacin Najeriya, musamman a Kudancin Kaduna.
“Babban abun damuwar shi ne mutane sun fidda rabon gwamnati za ta iya kawo karshen kashe-kashen da ake yi”, inji shi.
Ya kuma ce ya kamata gwamnati ta dauki matakin gaggawa da zai kawo karshen matsalolin tsaron da suka yi kakagida a Arewacin Najeriya.
“Gwamnatin Kaduna kuma ta dauki shawarar mutane na zama da wadanda abun ya shafa domin kawo karshen rikicin da ke faruwa a kudancin jihar.
“Su kuma mutanen da abun ya shafa su rika kawar da kai da hakuri da junansu, domin taimaka wa gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya.