A ranar Asabar da ta gabata ce magoya bayan Jam’iyyar PDP suka ziyarci tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamixo suna buqatar ya fito takarar Shugaban Qasa a zaven shekarar 2019. Wakilimmu ya samu tattaunawa da Alhaji Sule Lamixon a gidansa da ke garin Bamaina jim kaxan bayan kammala ganawa da baqin nasa inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi siyasa da harkokin qasar nan:
Yallavai Kotun Qoli ta ce wajibi ne a riqa zaven qananan hukumomi a Najeriya, to amma akwai bayanan da suke nuna cewa ba za a yi zaven qananan hukumomi a Jihar Jigawa ba, sai a watan Yuli yaya kuke kallon al’amarin?
Tunda yake lamari ne na jiha muna da shugabanci a jiha a matakin jam’iyyarmu kuma sun yi bayanai masu gamsarwa. Duk da yake Kotun Qoli ta yanke wancan hukunci, waxanda suke kan madafan iko a qananan hukumomi a jihar nan a yanzu kowa ya san ba a kan daidai suke ba haram suke ci kuma ita suke aikatawa. Kuma ina son ka sani in dai mun dawo kan mulki su ma sun san a cikin ruwa suke domin za mu tuhume su kuma jam’iyyarmu ta yi bayani na gaskiya saboda matakin da aka xauka na qin yin zaven ya sava wa doka da odar da ta kafa masu riqe da madafan iko a qananan hukumomin jihar.
Yaya za ku shiga zaven idan aka ce za a yi kuwa?
Batun maganar shiga zave ai tuni jam’iyya ta yi magana a kan haka, kuma ta yi maganar da ta dace ta bakin shugaban jam’iyyarmu na jiha.
Wane mataki ne kuke shirin xauka idan kun sake dawowa kan mulki a shekarar 2019?
Ka san kowane mutum a Najeriya yana da qa’idarsa da irin al’adarsa, kuma ka sani duk wanda ya yi savanin haka shi ma ya san in mun dawo za mu tuhume shi. In ka duba yanzu ba Buhari ne yake hisabi ba, ai hisabi Buhari yake yi ko? Komai ka yi in kai ba xan APC ba ne, sai a ce ka yi savo. Kana ganin abin da ake yi yanzu ya dace? Komai muka yi sai a ce ba mu yi daidai ba, yanzu ayyukan da muka yi shi ne yake dubawa yake yi mana hisabi. Wallahi magana ta gaskiya mu idan muka hau mulkin Najeriya ba maganar wariya a cikin tsarinmu duk wanda ya sava wa doka za mu hukunta shi, ba maganar PDP kake yi ko APC ba, aiki za mu yi tsakani da Allah ba nuna bambancin siyasa ko qabilanci ba, wannan shi ne adalci.
A kwanan baya ’ya’yanku da ke Majalisar Jihar Jigawa masu wakiltar Gwiwa da Gwaram sun sauya sheqa zuwa Jam’iyyar APC har Gwamna ya amshe su a zauren majalisar dokokin jihar yaya kake kallon lamarin?
Da farko dai sai in ce musu su sauka lafiya, domin kamar xanka ne ya ce ya bar ka, yaya za ka yi da shi? In ka duba a baya Jam’iyyar PDP ce ta yi tallarsu a matsayin ’ya’yanta a mazavunsu, ita ce ta saya musu fom na shiga takara kuma ta ba su kuxin tsayawa su sayar da kansu a wajen jama’arsu. Kuma ita ce ta xauki nauyin waxanda suka je suka yi gadin akwatunan zave domin ganin an kare mutuncinsu a lokacin zave a tabbatar sun kai ga nasara. Da suka yi nasara, aka yi qara muka bi muka tabbatar da matsayinsu a gaban shari’a. Ka san duk vacin rai, uba ba ya la’antar xansa duk da yin hakan akwai takaici da ciwo. Saboda shi jininka ne su ma duk inda suka shiga ’ya’yanmu ne kuma duk xan da ya bar gidan ubansa ya ce zai dawo ai gidansu ne ba ruwan kowa da shi mu mun san za su dawo.
Ke nan ba su da laifi Gwamna Badaru ne mai laifi da ya amshi baquncinsu?
Ina tsammani an yi bayani a kan haka, a lokacin da Jam’iyyar PDP ta yi wani taro a hedikwatarta a makon jiya. Duk masu faxa a ji sun yi bayani a wajen taron bayanai masu gamsarwa, domin magana ta gaskiya akwai muhallin siyasa da muhallin mulki. In da ake yin mulki ba a yin sha’anin siyasa a wurin, ba a haxa siyasa da mulki wuri xaya idan sun haxu kuwa babu shakka akwai matsala, kuma za a iya jin kunya.
Majalisa ba wurin taron siyasa ba ne abin da Gwamna Badaru ya yi a Majalisar Jihar ya sa a ko’ina sai dariya ake yi mana. Saboda magana ta gaskiya babu yadda za a ce Shugaba Buhari ya amshi masu canja sheqa a zauren majalisa ko kuma a ce wani daga cikin gwamnonin PDP ya aikata irin abin da Gwamna Badaru ya yi, amma saboda a Jihar Jigawa akwai jahilcin siyasa shi ne kawai akayi haka.
Mun xauki mataki domin mun gama tattaunawa da lauyanmu mun rubuta wa Gwamna Badaru da Shugaban Majalisar Jihar Jigawa da waxancan ’yan majalisa takardu uku, xaya daga cikin takardun muna neman Hukumar Zave ta Qasa (INEC) ta ba mu izini da tsarin dokkokin da za mu bi na janye waxancan ’yan majalisa. Xaya takardar jam’iyya ta rubuta wa Gwamna Badaru ne ya fito ya nemi afuwar jama’ar Jihar Jigawa kan mayar da zauren Majalisar Dokokin dandalin siyasa, yayin da xaya takardar aka rubuta wa Shugaban Majalisar a kan laifin gayyato Gwamna Badaru zuwa zauren majalisar domin amsar waxanda suka sauya sheqar. Shi ma laifi ne da ya sava wa tsarin majalisa babu inda doka ta ce shugaban majalisa ya gayyato Gwamna zuwa majalisa don amsar masu sauya sheqa domin majalisa ba zauren siyasa ba ne.
Kuma mun aika da kwafin wasiqar zuwa fadar Shugaban Qasa da ofishin Shugaban Majalisar Wakilai da jami’an tsaro da Kwamishinan Shari’a da na ’yan sanda na Jihar Jigawa. Domin ba za mu bari mai irin waxannan halaye ya ci gaba ba a matsayin shugaba.
Saboda Gwamna ba ya zuwa majalisa idan ba kasafin kuxi zai karanta ba ko idan wata matsala ta taso ba ko kuma majalisar ce ta hango wata matsala take da burin a warware matsalar shi ne za ta gayyaci Gwamna, amma ba don wani taron siyasa ba.
Abin da Shugaban Majalisar ya yi laifi ne da ya sava wa dokar qasa domin babu inda aka tava yin haka sai a Jihar Jigawa.
Idan kuma ba a yi gyara ba, mu ma za mu je majalisar mu yi taro a zaurenta mu karrama ’ya’yanmu a cikin zauren majalisar tunda dai zauren majalisar ya zama dandalin yin siyasa. Za mu yi taron ne a matsayimmu na ’ya’yan Jihar Jigawa tunda dai dokar qasa ta ba mu damar mu yi taro mu karrama ’ya’yanmu a cikin zauren majalisar.
Na gode wa shugaban jam’iyyarmu da ya yi tunanin rubuta waxancan takardu domin ya nuna ’ya’yanmu sun san doka kuma sun qware a harkar siyasa muna yin koma a kan doka ba ma taka doka.
Yaushe za ku janye ’yan majalisar?
A yanzu muna jiran Hukumar INEC ne ta ba mu qa’idojin janye su daga majalisar, sai mun samu qa’idojin ne za mu yi aiki da dokar kuma yanzu haka muna yin bayanai ga xaukacin ’ya’yan Jam’iyyar PDP da suke qananan hukumomin biyu, muna tattaunawa da shugabannin mazavun yankunan, kuma za mu gana da jama’a masu katin zave a yankunan domin dawo da su gida, shirye-shirye sun yi nisa domin dawo da su gida.
Yaya batun tsayawarka takarar Shugaban Qasa na ga jama’a na tururuwa zuwa gidanka suna kiran ka fito takarar, shin ka amsa ko kuwa?
Duk abin da jama’a suka buqace ka, ba kai ne ka nema ba yana da kyau ka amsa kiran jama’a kuma ina godiya ga Allah da jama’ar suka ga na dace in fito neman mulkin qasar nan ba don na fi kowa ba, a’a sai don Allah ne Ya ga na dace a ce ni ne nake shugabancin Najeriya. Fatana Allah Ya yi mana zavi mafi alheri, domin abin ba wayona ba ne ko wata dabara, al’amari ne daga Allah, a kullum burinmu da fatanmu Allah Ya sanya mu a kan daidai, kada Allah Ya bar mu da iyawarmu.
Waxansu na kallon qaqaba muku Alhaji Modu Sheriff a matsayin Shugaban Jam’iyya da Kotun Xaukaka Qara ta yi a Fatakwal tamkar zagon qasa ne ga jam’iyyar daga jam’iyya mai mulki yaya kuke kallon al’amarin?
Na sha faxi cewa mai hamayya da kai balantana yanzu shi ne yake mulki kuma yana ganin zai faxi a zave ba zai bar ka ba. Sun san sun yi wa jama’a qarya sun zagi PDP, sun ce mu ne Boko Haram, mu ne muka lalata qasa duk wani sharri sai a ce mu ne, mu ne varayi kai kana zaton za su je masallaci su yi mana Sallah raka’a biyu su ce Allah Ya yi wa PDP albarka ne? Saboda haka a ganina abin da suke yin nan shi ne ya kamata su yi, su sanya mu cikin tsauri mu kuma shi ne zai qara mana kwarjini, shi zai qara mana martaba a idon jama’a. Domin qarfin azabar da suke gana mana ne zai sa mu sami daxin daraja.
Yaya batun cewa za ku fice daga jam’iyyar saboda wancan hukunci?
Ina son ka gane idan suna yin haka ne domin su matsa mana, to shi ne abin da Malam Bahaushe yake faxi suna gudun qaddara kuma duk mai gudun qaddara yana tare da ita saboda haka idan suna tunanin sun yi haka ne domin su ruguza mu su daina kansu suke rusawa wannan alama ce da ke yin nuni qarshensu ya zo sun zo daf da rushewa.
In na fahimce ka kana nufin kuna cikin PDP babu inda za ku ke nan?
Ina so ka fahimci wani abu, siyasa aikin xa ne mai ’yanci ba mai ci-da-ceto ba, kuma jama’a su sani tun kafin a yi daram a ka yi kwanxi, tun kafin a yi Modu Sheriff ko Maqarfi muke cikin PDP, mu ne muka kafa ta. Saboda haka wannan rigimarmu ce ta cikin gida babu ruwanka mu duk ’ya’yan PDP ne kuma su ma ’ya’yanta ne kowa ya san haka. Saboda haka babu ruwanku kuma za mu tabbatar mu nyi maganin matsalarmu.
To me kuka tattauna a taronku na Abuja da kuka yi?
Ina ruwanka?
Wai saboda magoya baya na san za su so su ji ina aka kwana kan tafiyarku?
Ai da su da mu muka yi taron kuma me kake son ka ji? Mun tattauna ne a kan matsalarmu a kan abin da ya damu jam’iyyarmu a cikin gida da abin da ya damu jama’ar qasa domin ’yan Najeriya sun banu saboda mulkin da ake yi a Najeriya ana yin sa ne a kan alqawari a kan mutunci a kan gina qasa da zumunci. Amma an wayi gari mulkin ya zo an samu rarrabuwa a tsakanin ’yan Najeriya mu-ya-mu muna qin junanmu a gari xaya muna yin gaba da junanmu a qaramar hukuma xaya, a jiha xaya, a qasa xaya ba ma qaunar junanmu. Tsakanin Kirista da Musulmi da ’yan Kudu da’ yan Arewa da Fulani da Hausawa. A ko’ina masifa ce ana ta yin gaba da juna saboda haka wannan alama ce ba a yin gaskiya a aikace. Iyakacin gaskiyarmu a fatar baki ce kawai shugabancin a wajen ’yan qasa ya rataya ne a wuyan shugabanni da wanda yake son Buhari da wanda ba ya son Buhari kowa yana da hakki amma yadda Gwamnatin Tarayya take tafiya ba daidai ba ne an kauce wa tsarin da aka yi alqawari.
Daga Umar Aqilu Majeri, Dutse