✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa zan tsaya takarar shugaban kasa- Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019. Shekarau…

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Shekarau wanda kuma tsohon Ministan Ilimi ne ya yi wannan jawabin ne a wata takarda da aike wa Aminiya, inda ya ce zai tsaya ne domin ya amsa kiran mutane.

“Kamar yadda kuka sani ne, tun bayan zaben 2015, mutane da kungiyoyi dabam daban suna kiraye-kiraye da in tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019.

“Na yi imanin cewa mutanen suna kira na ne saboda sun yarda kuma sun amince da ni bisa dan nasarar da aka samu a lokacin da nake Gwamnan Jihar Kano a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, da kuma lokacin da nake Ministab Ilimi a tsakanin watan Yuli na shekarar 2014 zuwa watan Mayu na shekarar 2015.

“Saboda wannan kiraye-kiraye da ake min da kuma girman aikin da suke kira na in yi. Na yi tuntuba mai fadi a duk bangarorin kasar nan, inda suke duba sannan kuma suka bani shawarar da ta dace.

“Ina mai farin cikin cewa, bayan na yi wannan tuntuba, na kara fahimtar cewa shiga siyasa da nufin amfanar da mutane ya wuce maganar jam’iyyar da kuma maganar lashe zabe kawai.

“Don haka na amince zan amsa kiran mutane, sannan kuma nan ba da dadewa ba kamar yadda dokokin jam’iyyata ta PDP ta kindaya, zan tsaya takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.” Inji Shekarau.