Wata gidauniyar kasa-da-kasa mai cibiya a kasar Birtaniya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin Najeriya don shawo kan manyan matsalolin da ke hana yara miliyan 10.19 zuwa makaranta a kasar.
Bayanai sun tabbatar da cewa a kasashen nahiyar Afirka Kudu da Sahara, Najeriya ta fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
A shirin Najeriya a Yau mun yi nazari a kan wannan matsala da yadda za a magance ta.