✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa taurarona ke kara haskawa —Ali Nuhu

Ali Nuhu ne farkon tauraro kuma jarumi da ke yin fim a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood da ya tsallaka ya zamo tauraro a…

Ali Nuhu ne farkon tauraro kuma jarumi da ke yin fim a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood da ya tsallaka ya zamo tauraro a masana’antar shirya finafinai ta kasa wato Nollywood.

A baya-bayan nan ne kamfanin samar wa matasa aiki tare da ba su shawarwari na ‘Joberman’ ya yi hira da Ali Nuhu ta bidiyo inda ya bukaci tauraron yi wa matasa bayanin hanyoyin da ya bi har ya yi nasara sana’arsa ta fim.

Aminiya ta kawo muku hirar kamar haka:

Abin da ya ja hankalina zuwa harkar fim

Tun ina karamin na taso da shauki da kaunar sana’ar fim, domin tun ina cikin kuruciyata nake son kallon talbijin.

Tsabar kallon talbijin ne ma ya sa ban iya kwallon kafa ba, saboda ba ni ma da lokacin fita na yi wasan kwallon, sai kallon talbijin a gida.

Ka ga ko ce maka matashi bai iya kwallon kafa, za ka yi mamaki me yake yi a gida musamman a wancan lokacin.

Idan na ga masu karanta labarai a talbijin suna matukar burge ni, ina sha’awar abin da suke yi kwarai, haka su ma masu yin wasan kwaikwayo a talbijin suna ba ni sha’awa.

Daga nan ne hankalina ya karkata a harkar fim tun ina karami, a wannan lokacin mutane da dama na fada min cewa ai fim ba sana’a ce da mutum zai dogara da ita ba, ba sana’a ce ta dindinin ba. Haka suke kushe ta, ta yadda za su sauya min tunani.

Amma ni ban damu da abin da suke cewa ba, sai na kudurce a zuciyata cewa wannan ne abun da nake so, kuma abin da zan yi ke nan.

Abin da na sa a gaba shi ne yadda zan yi na cimma wannan manufa na kuma inganta ta, saboda kaunar da nake wa harkar.

Don haka na yi wa harkar kaykyawan shiri domin ita ce sana’ar da na rika nake kuma dogaro da ita a rayuwa, don haka na tabbata na yi mata kyakkyawan tushe.

Ali Nuhu
Na yi karatu  a  Jos don na sami makamar aikin fim

A lokacin da na kammala karatuna na yi jarabawar shiga jami’a ta JAMB, na samu gurbin karatun a tsangayar hada magunguna (Pharmacy) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Amma na ki zuwa can, saboda na gano a wancan lokacin garin Jos ne cibiyar shirya finafinai a Arewa, don haka na kudurce a raina cewa Jos za ni na yi karatu domin na hadu da kwararrun masu shirya fim su sa ni a fim dinsu.

Da mahaifina ya ji matakin da na dauka sai ya ki yarda, domin yana ganin na samu gurbin karatu kai tsaye da zan yi Digiri a Pharmacy a ABU —ya yi min hangen cewa wannan karatu ne mai mahimmanci.

Ni kuma dalilina na kin karatun shi ne a ABU ba zan samu damar haduwa da kwararru a harkar fim ba, don haka na so zuwa Jos domin a lokacin ita ce cibiyar masu shirya fim a Arewa.

Mahaifina ya ce idan na je Jami’ar Jos zan koma baya domin sai na faro daga matakin share fagen shiga jami’a saboda a jarabawar da na yi ba Jami’ar Jos din na cike ba.

Ni kuma na gwammace na koma baya domin na cimma burina na shiga harkar fim, a haka mahaifina ya hakura, ya yarda na tafi Jami’ar Jos, inda a lokacin karatuna na hadu da kwararrun masu shirya finafinai na wancan lokacin.

Nakan je gidan Talbijin na Kasa da ke garin Jos domin neman sanin makamar aikin wasan kwaikwayo.

Ali Nuhu tare da iyalinsa

 

Na yi ta shiga Legas daga Ibada don neman makamar aikin fim

Bayan na kammala karatun Digirina na farko a Jami’ar Jos sai na yi sa’a nan ma aka tura ni bautar kasa garin Ibadan, jihar Oyo.

Nan ma sai na samu dama a duk karshen mako ina shiga Legas.

Akwai dandalin da ke tara kwararru masu shirya fim da ‘yan wasa a unguwar Surulere, nan ma na kan je duk karshen mako a nan ma na shiga.

An shirya fim da ni akalla sau uku kamar yadda na yi a Jos, da haka na yi wa sana’ar tawa kyakkyawar turba.

 

Mahaifina ya sama mini aikin gwamnati, amma na ki karba’

Bayan na kammala bautar kasa a Ibadan, har na fara sana’ar fim a Kano, sai mahaifina ya sama mini aikin gwamnati a wata ma’aikata amma na ki karba.

Sadda na dawo Kano ina da abokai biyu, Rabiu Ibrahim da Hafizu Bello, suna so su shirya wani fim na kansu kowannensu, sai suka shigar da ni ciki, suka bukaci na ja ragamar aikin fim din.

A lokacin ne mahaifina ya samo min aikin gwamnati, amma na ce masa a’a, domin kudin da zan samu a fim din ya fi abin da za a rika biya na a wata, don haka na ce ni fim zan yi, ba aikin gwamnati ba.

Lamarin ya zama gagarumi domin har sai da mahaifiyata ta shigo ciki ta yi ta ba wa mahaifina hakuri, har ya hakura.

 

Masana’antar fim na ba wa kasa gudunmawa

Tabbas masana’antarmu ta fim ta ciri tuta wajen ba wa kasa gudunmawa, wannan ne ya  sa hankalin gwamnati ya karkata a kan masana’artar domin duk abin da ka ga gwamnati ta mayar da hankali a kai, to akwai amfanin da take samu a ciki.

Kazalika masana’antar fim masana’anta ce da ta samar wa jama’a da dama ayyukan yi da abin dogaro da kai, domin a kasar nan akwai mutane da dama da ke amfana kai tsaye da masana’antar baya ga gudunmawar da ta ke bayarwa ta fuskar nishadi da bunkasa al’adunmu.

A baya mutane sun dauka masana’antar fim waje ne na marasa ilimi ko wadanda suka kasa yin karatu, wannan ba haka ba ne.

Masana’antar kanta waje ne na yin ilimi da kwazo tare da nuna bajinta, don haka idan kana da kwazo da hazaka, ko ba ka yi karatu ba, za ka iya zuwa ka nuna baiwarka a kuma amfana da ita.