✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Shagari ya samu nasara a mulkinsa – Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai yana daya daga cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar NPN, wacce marigayi Alhaji Shehu Shagari ya mulki kasar nan a karkashinta. Kuma ya…

Alhaji Tanko Yakasai yana daya daga cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar NPN, wacce marigayi Alhaji Shehu Shagari ya mulki kasar nan a karkashinta. Kuma ya zama mashawarcin Shagarin a kan harkokin majalisa. A tattaunawarsa da Aminiya ya  ce duk da cewa jam’iyyarsu ba ta da rinjayen mambobi a majalisa amma hakan bai hana a samu kyakkyawar mu’amala da fahimtar juna tsakanin Shugaba Shagari da ’yan majalisar wancan lokaci ba.

 

Yaya alaka ta kasance tsakaninka da marigayi Alhaji Shehu Shagari?

Mun san juna ni da Shehu Shagari, muna gaisawa a duk lokacin da wani abu ya hada mu, duk da cewar muna jam’iyyu daban-daban saboda a lokacin ni ina Jam’iyyar NEPU shi kuma yana NPC. Sai dai alakarmu ta zamo mai karfi lokacin da aka barar da Janar Aguyi Ironsi daga mulki, aka soke jam’iyyun siyasa. Ganin cewa hadin kan ’yan Arewa ya raunana sakamakon siyasa sai Gwamnan Arewa marigayi Janar Hassan Usman Katsina ya kafa wani kwamiti mai mutum 15, inda aka dauko mutum biyar-biyar daga jam’iyyu uku da suka hada da NPC da NEPU da UNPC. Sai ya zamanto ni da Shagari muna cikin wannan kwamiti wanda muka rika gudanar da tarurruka. Wadannan tarurruka da muka rika yi a kai-a kai sai ya zamanto mun shaku da juna. Musamman sai aka yi dace ra’ayinmu ni da shi yana zuwa daya a abubuwa da dama.  Haka kuma lokacin da gwamnatin soja ta Yakubu Gowon ta hau bayan an samu sababbin jihohi sai aka nada kwamishinoni a jihohin. A can Sakkwato an nada Shagari kwamishina ni ma a Kano an nada ni Kwamishinan Watsa Labarai. Ana nan bayan Malam Yahaya Gusau ya sauka daga mukaminsa na Ministan Tattalin Arziki sai Gwamnatin Tarayya ta maye gurbinsa da Shagari inda daga baya aka canja masa ma’aikata ya zama Ministan Kudi. Ni kuma nan Kano sakamkon rasuwar Umaru Gumel wanda shi ne Kwamishinan Kudi sai aka ba ni mukaminsa. To wannan mukamai da muka rike na ma’aikatun kudi ya kara karfafa dangantakarmu muka kara samun shakuwa domin mukan gudanar da tarurruka a koyaushe.

Ana tunanin alakarku da Alhaji Shehu Shagari ne ya sa ya janye ka zuwa Jam’iyyar NPN, me ke gaskiyar wannan batun?

Zan iya cewa ba haka ba ne, domin kamar yadda na gaya miki tun a baya an riga an rushe jam’iyyun NEPU da NPC da sauran jam’iyyu. Daga baya lokacin da aka dage takunkumin siyasa sai ni da Shagarin da wadansu mutane da suka fito daga jam’iyyu daban-daban muka kafa Jam’’iyyar National Mobement wacce daga baya ta narke ta koma NPN. Haka  a wancan kwamiti da muka rika haduwa mun tsayar da cewa idan za a sake yin siyasa mu ’yan Arewa za mu shiga jam’iyya daya don mu samu hadin kai. Duk da cewar ’yan Kudu ma sun shiga jam’iyyar. Babu Jam’iyyar da ta samu karbuwa a kasar nan kamar NPN, domin duk sassan kasar nan kowa ji yake jam’iyyar tasa ce.

Abin da zan iya cewa dai shi ne, waccan alakar da muka samu ta yi tasiri kwarai inda muka fahimci junanmu. To bayan an tsayar da shi takara ya sanya ni a cikin kwamitin yakin neman zabe, inda muka rika bin jihohin kasar nan wajen nema masa kuri’a. Bayan ya yi nasarar zabe an kafa gwamnati sai ya ba ni mukamin mataimakinsa kan bin da ya shafi majalisa. Kasancewar ana samun gibi na fahimta tsakanin bangaren gwamnati da na majalisa ya sa aka kirkiri wannan mukami, wanda har yanzu ana ci gaba da amfani da shi. Wannan ya samo asali ne sakamakon tsarin gwamnatin Shugaba Mai cikakken iko wanda ya saba da na baya na Firayi Minista. A da shugaban gwamnati da ministocinsa duk ’yan majalisa ne don haka babu wata matsala wajen tafiyar da gwamnati.

Yaya za ka bayyana salon mulkin Alhaji Shehu Shagari a wancan lokaci?

Zan iya cewa Alhaji Shehu Shagari ya tafiyar da mulkinsa bisa kawo sababbin tsare-tsare na tafiyar da gwamnati. Wannan kuwa ya samo asali ne sakamakon gogewar da yake da ita a lokacin da ya rike mukaman minista daban-daban har guda bakwai. Shagari ya taba rike mukamin Ministan Daukar Ma’aikata da Horar da su da Ministan Al’amuran Cikin Gida da Ministan Masana’antu da Ministan Sufuri da Ministan Ayyuka da Ministan Tattalin Arziki da kuma Ministan Kudi.

Daga cikin abubuwan da ya bullo da su a ci gaban gwamnati a lokacin mulkinsa sun hada da taron Shugaban Kasa da ministoci na mako-mako, inda ya sanya duk ranar Laraba yakan zauna da dukan ministocinsa a tattauna, sabanin mulkin baya wanda Shugaban Kasa yana zama da ministocin da suke da wasu matsaloli a ma’aikatunsu ne kawai, a kuma lokacin da ya samu dama. Wannan abu da ya bullo da shi ga shi nan har yanzu ana yi.

Haka ya kafa Kwamitin Dattawa ko shugabannin jam’iyya, inda yake yin taro da su a duk mako. A ranar Litinin Shuagabn Kasa zai gabatar musu da abin da zai gabatar a taronsa na ranar Laraba da minstoci don haka a nan za a yi masa gyare-gyaren da suka dace kafin ya je ya gabatar.

Kin ga a wancan lokacin duk da cewa Jam’iyyar NPN ba ta da rinjaye a majalisun biyu na dattawa da na wakilai, domin kashi daya bisa uku take da shi, amma sai ya zamanto a tsawon shekara hudu da muka yi sau biyu rak muka kai kuduri majalisa aka yi watsi da shi. Daga baya shi ma mun gane kuskuren daga wurinmu yake, wanda daga baya mun gyara kuskuren kuma majalisar ta zartar da shi. Wannann kuwa ya samo asali ne sakamakon kyakkyawar alaka da ake samu tsakanin bangaren gwamnati da majalisa. Kasancewar lokacin da ka tashi zaben shugabannin majlisa Shagari bai nuna zabinsa ya yarda kowa nasa ne domin a yi aiki tare. Ya bar wa ’yan majalisa su zabi shugabansu da kansu. Kodayake shi Shagari yana da ilimin zaman majalisa domin ya zauna a majalisa tsawon shekara 12.

Da a ce shugabannin yanzu za su dauki wannan dabarar da ba za a samu matsala tsakani ba. Bai kamata Shugaban Kasa ya damu da wanda zai shugabanci majalisa ba. Wannan shi yake jawowa idan wanda Shugaban Kasa bai goya masa baya ba ya samu shugabancin ya rika ba Shugaban Kasar matsala wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Yaya za ka bayyana halayen marigayi Alhaji Shehu Shagari?

Shi dattijo ne domin ba ya magana biyu kuma shi kaifi daya ne, idan ka zo da magana ba ta daidai ba zai gaya maka cewa ba ta yi daidai ba tare da kawo maka dalilansa masu gamsarwa. Idan ka yi kuskure zai nuna maka kuskurenka amma ba da fada ba. Haka ko kana aiki a karkashinsa ba ya tilasta ka ka yi abin da ba ka da ra’ayi a kansa. Ya iya zama da mutane, domin shi ba ya hamayya ko jayayya da mutane. Wannan ya sa mutanen da suka zauna da shi suke yabonsa. Haka yana da basira da kaifin hankali hakan ya sa yake da fahimtar al’amura na siyasa da tafiyar da gwamnati.

Wace shawara za ka ba ’yan siyasa musamma a wannan lokaci da zaben 2019  ke tunkarowa?

Sha’anin siyasa na da da yanzu akwai bambanci. A da kishin kasa ne yake sanya wa mutane suke shiga siyasa tare da neman mukamai don su taimaka wa al’ummarsu. Amma yanzu an mayar da siyasa hanyar kasuwanci da neman kudi. Mafi yawan ’yan siyasa suna neman mukamai ne don su azurta kansu da dukiyar gwamnati. Shi ya sa ki ga rigima ta yi yawa a cikin siyasa har ana kaiwa ga kashe-kashen juna da sauransu.

Kasar nan ba za ta gyaru ba sai siyasar kasar nan ta gyaru, ita kuma siyasa ba za ta gyaru ba sai masu siyasa sun gyara halinsu ya zama cewa siyasa suke tsakani da Allah da kuma kishin kasa ba don neman azurta kansu ba. Idan sun samu mukamai su ga yaya za su bayar da gudunmawa wajen ciyar da kasa da yankunansu gaba. Idan har siyasa ta gyaru to za a tsaya a yi wa kasa aiki. Duk kasashen duniya da aka ga sun gyaru sun ci gaba, to ’yan siyasar kasar ne suka gyara su, misali irin su kasar Koriya.