✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa Rahama Sadau ta nemi afuwa

Fitacciyar Jarumar Fina-finan Hausa na Kannywood Rahama Sadau ta nemi afuwar Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II…

Fitacciyar Jarumar Fina-finan Hausa na Kannywood Rahama Sadau ta nemi afuwar Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II bisa mummunar fitowar da ta yi a wani faifan bidiyon waka wanda ya jawo mata kora daga masana’antar fina-finan Hausa na Kannywood a bara.

Jarumar ta mika sakon neman afuwar tata ne ta kafar watsa labarai ta gidan Rediyon Rahama inda ta dauki alkawarin ba za ta sake aikata kwatankwacin kuskuren da ta yi ba, tare da neman afuwar masoyanta da kuma abokan aikinta bisa abin da ta aikata ba daidai ba.

“Sunana Rahama Sadau ina so na yi wasu bayanai akan abubuwan da suka faru a baya wanda ya bata ran mutane masu yawa. A wancan lokaci na yi shiru ne don ba na son yin magana a lokacin da abin yake kan zafinsa. Ina bayar da hakuri ga duk wanda bai ji dadin abin da na aikata ba

musamman Sarkin Kano da Gwamnan Kano da abokan aikina a masana’antar fim din Hausa da duk wanda bai ji dadin lamarin ba”

Rahama Sadau ta kara da cewa “idan aka sami faruwar wani abu mara kyau, ba wai kawai ga Rahma Sadau ba, ga duk wani dan fim, abin da muke bukata shi ne goyon baya da kuma karfin gwiwa ta yadda za a kira mu a nuna mana kuskurenmu domn mu gyra amma ba wai a je na gulmarmu a kan abin ba. Ina amfani da wannan dama waje rokon kowa ya yafe min kan

abin da ya faru, insha Allah ba zai sake faruwa ba”

Idan za a iya tunawa Kungiyar ‘yan  fim xin Hausa ta MOPPAN ta yanke hukuncin korar jaruma Rahma Sadau daga masana’antar fim din Hausa a ranar  2 ga watan Oktobar shekarar 2016 bisa zargin ta da laifin mummunar shiga a wani faifan bidiyon wakar Hausa tare da mawakin nan

mazaunin garin Jos wato ClassiQ.

Wannan neman afuwa da jaruma Rahama ta yi ta ba mafi yawan masoyanta mamaki duba da irie-iren maganganun da aka ce jarumar ta yi bayan korar tata, domin kafafen watsa labarai da dama sun rawaito cewa jaruma Rahama ta bayyana cewa korar da aka yi mata ya zama wata kafa

da ta bude mata kofofi a harkar sana’arta ta fim.

Idan za a iya tunawa kwanaki qalilan bayan korari tata jaruma Rahama wani fitattce mawaki ya gayayce ta kasar Amurka inda ta fito a wani fim, yayin da ta dawo kuma sai ta fara fitowa a fina-finan kudu na Nollywood inda ta fito da wani fim mai suna ‘TATU’ Wannan ne ya sa mutane ke tunanin cewa kwararriyar jarumar ta fi qarfin fitowa a finafinan Hausa.

Wani babban masoyin Jarumar mai suna Michel . ya bayyana cewa “ abu ne mai kyau da jarumar ta nemi afuwa ta wowa ta ci gaba da yin fim a gida, amma sai dai ina tsoron hakan zai iya zama matsala ga ayyukan da take yi a wajen Kannywood. Kun san lokacin da aka kore ta ta sami

damarmaki masu yawa har ma a wajen kasar nan. Ta fito a fim din gida na Nollywood haka kuma wani ya  gayayce ta zuwa kasar Amurka, ina tunanin idan ta dawo za a ba ta ta roka zuwa tana fin a sauran wurare?

Fitaccen jarumi Ali  Nuhu wanda yake da hannu a batun neman afuwar da Rahaman ta yi ya shaida wa Jaridar Aminiya ta wayar tarho cewa ta nemi afuwar ne don kanta duba da yadda ta gano cewa ta yi kuskure kasancewar dan adam ajizi ne. “ A matsayinmu na manya a wannan

masana’anta hakkinmu mu dora na kasa da mu a kan hanya, don haka na yi ruwa na yi tsaki a cikin batun neman afuwar tata. A rayuwa yana da kyau ga mutum ya gyara tare da neman afuwa a yayin da ya aikata abin da bai dace ba. Rahama ta yi kokari wajen neman afuwa tare da

alkawarin ba za ta sake maimaita kwatankwacin laifinta ba. A yanzu haka ma ta rubuta takardar neman afuwa ga Kungiyar MOPPAN wanda na yi imanin shugabannin qungiyar suna kan tattaunawa akan lamarin” Inji Ali Nuhu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da jaruma Rahama Sadau ke tsintar kanta a cikin rikici ba, domin ko a baya an yi lokaic da ta zargi Adam Zango da kin sanya ta a fim dinsa na ‘DUNIYA  MAKARANTA’ sakamakon rashin samun  hadin kanta ga bukatarsa ta neman yin lalata da ita,

lamarin da ya jawo cecekuce a wanann masan’anta har ma Kungiyar MOPPAN ta dakatar da ita a wancan lokaci kafin daga bisani ta dawo bakin aiki.

Haka kuma an taba samun jarumar da fitowa a cikin wani fim da ba a tace shi ba wato “ANA WATA GA WATA” inda aka smau fim xin ya shiga kasuwa ba tare da tacewa ba lamarin da ya jawo  Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dauki tsattsauran mataki na cewa dukkanin mutanne da ke da  hannu a cikin fim su gurfana gaban kotunta ta tafi da gidanka.