Rabiu Rikadawa fitaccen dan wasan Hausa ne da ya ga jiya ya kuma ga yau, sai dai a yanzu an fi sanin sa da suna Baba dan Audu. A tattaunawarsa da Aminiya, jarumin ya bayyana yanayin ci-gaban da aka samu a fim da sauransu.
A baya an san ka da Dila, yanzu kuma an fi sanin Baba Dan Audu, ko za ka bayyana mana yadda ka samo sunan Dila?
Yadda aka samu Baba Dan Audu haka aka samo Dila. Dukansu suna ne da aka samo daga fim, wato awar da na taka a fim. Kamar shi Dila lokacin NTA Kaduna, a lokacin babu tashoshi da yawa.
Lokacin ina aiki da DITV, lokacin tashar ce kadai ke sanya dirama. A lokacin ni ne forodusa, ni ne darakta kuma ni ne ma tsara labari, sannan kuma ni ne babban jarumi.
Sunan shirin ‘Komai tsawon dare’ da ake nunawa duk Lahadi da 8 na dare. To lokacin NTA ba ta yin dirama, sai ya zama kalubale a wajenta, inda ta kirkiri dirama na barkwanci. Lokacin sun ce suna son abu kamar Tom and Jerry. Sai aka nemo wani babban mutum Dan Asabe Abdullahi Kayar Bushiya, ni kuma dan karami.
Sai ni da Moda da Hauwa Gamawa da shi Dan Asaben muka zauna muka fitar
da tsarin, muka tsara labarin. Nan muka zauna muka amince mu yi fitowa ta farko a matsayin gabatarwa, tunda sabuwar dirama ce, sai mu sanar da kanmu ga kowa. Haka abin ya faru.
Bayan an gama sai aka ce ni ne zan fito a matsayin Dila, Dan Asabe Abdullahi a
Kurungu, Moda a matsayin Alhaji, sai
na ce ni ba zan fito a matsayin Dila ba.
Na ce matsalar ita ce ina aiki da DITV, ina gabatar da shirye-shirye ciki har da dirama, yaushe zan saki wannan in tafi ina wata diramar? Kuma kar
su sa aikinsu ba na nan.
Haka muka rabu da su, lokacin babu waya. Na tafi gida sai ga forodusoshinsu guda biyu George Agbese da marigayi Kasimu Muhammad suka zo gida suka same ni cewa lallai hukumomin gidan sun ce ni ne suke so in fito a Dila, na fada musu matsalolina, sai suka ce idan ba ni da lokaci, za a iya dagawa har in samu lokaci. Ka ji yadda na samu sunan Dila.
A Dila duk inda aka fito maka sai ka samu nasara, amma Baba Dan Audu ya shiga hannu har fursuna aka kai shi?
Rawa ce guda biyu daban-daban a shirye-shirye mabambanta. Yaya za a iya a kama Dila? Ka san Dila kuwa? Ai Dila ba zai yiwu a kure shi ba. Babu marubucin da zai yarda ya yi rubuto a ce an kure Dila, ba zai yiwu ba. Ko mafarauci ban yi tsammanin akwai wanda ya tava kama Dila ba.
A Labarina kuma wata rawa ce daban. Da Dila din ne na ci gaba da ba zan shiga hannu ba ko a nan din.
Wannan shiri ka fi so a cikin wadanda ka yi?
A matsayina na jarumi ba ni da wanda na fi so. Fim ba rayuwarka ba ce, rayuwar wani ce za ka hau ka zauna domin isar da sako. Idan ba ka hau matsayin ba da kyau, ba za ka iya isar da sakon ba.
Misali, a ce na fito a matsayin wani dattijon jarumi kamar Malam Musa Abdullahi, sai aka ga ina yi kamar wani dattijon misali Balarabe Jaji. Don haka, ya kamata jarumi ya zama zai iya taka kowace rawa da kyau. Sai dai abin da mutane suke so. Wasu suna son ganin ta a matsayin zaluntar ka a fim in ka fito a mai hakuri.
Wani kuma yana son ganin ka a matsayin azzulumi, wani kuma malami. Shi dai kawai ana son jarumi ya zama zai iya fahimtar me zai yi, ya yi kuma kokari ya fitar da abin da ake bukata.
Kun ga jiya da yau. Yaya ka yi wajen canja salon tafiya da zamani?
Duk dai fim ake yi har yanzu, a kullum duk jarumin da zai iya shiga kowane irin fim, to zai iya komai. Ba ma dirama ta da a yanzu, ko Masana’antar fim ta Bollywood ta Indiya aka kai ka, idan har kai jarumi ne, to za ka taka rawar da ta
dace kuma ku isar da sakon. Kawai dai abin da ake so shi ne ka fahimci sakon, ka iya isar da shi. Sai dai a da
yawanci sakonni ne na gwamnati na jawo hankalin jama’a, yanzu kuma an fi mayar da hankali kan abin da mutane za su karba.
A Labarina ka fito a matsayin mai tsananin son kudi. Wasu za su ce ko dai Baba Dan Audu mai tsananin son kudi ne da gaske?
Shi Baba Dan Audu za ka ga mutum ne da ya yi shekaru a Saudiyya, ya dawo kasar ba tare da ya shirya ba. Mutum ne kawai da aka koro shi daga Saudiyya, babu kudi kuma babu tsammaninsu. Zuciyarsa ba ta kasar da ya dawo, tana can kasar da ya baro.
Tunaninsa yaya za a yi ya koma saboda zama bai ishe shi ba. Saboda haka, zai rika yin komai domin ya samu damar komawa saboda a can ne yake da nutsuwa. Ka ga ba shi da aikin komai, matarsa kanta da yake ya dade a can ba ya mata wani aike ta gaji da shi.
Kuma mutumin da ya zauna a Saudiyya kusan shekara 20 ko 30 ya saba da cin kaza da madara da sauransu, yanzu kuma ya dawo Najeriya naman miya yanka biyu sai an yi dace. Ka ga dole ba zai samu nutsuwa ba idan ba ya samu yadda zai dan samu nutsuwa kamar yana can din ba.
Ana koma Youtube yanzu. Yaya za ka kwatanta yanayin karbuwarta?
Youtube ya fara farfado da fim. Rayuwa canjawa take yi. Daga nan zuwa can. Lokacin da aka koma daga VHS zuwa CD, an sha wahalar gaske.
An yi gumurzu kamar masana’antar za ta rushe. Haka kuma ana kan CD, sai rayuwa ta sauya zuwa yanzu da za a koma intanet. Nan shi ma aka tsaya kamar za ta rushe, amma yanzu shi ma an fara samun fahimta. Yanzu akwai jarumai da suka yi shuhura a Youtube da dama da ba su da fim ko daya a CD. Kuma an san su sosai. Ita duniya kullum matsawa take yi.
Shin kana da kira ga jarumai masu tasowa?
Mu dai wasu muka kalla da muka san hukuma da malamai da sauransu duk san yarda da su. Daraktoci da forodusoshinmu duk masana ne. Kuma suna horon mu mu kara ilimi. Amma yaran yanzu yawanci sun fi biye wa kyalkyali.
Muna cikin tafiya ne da aka dawo CD harka ta koma wajen ’yan kasuwa, wani zai je ya sayar da gonar gado, wani kuma dan kasuwa ne zai nemi jari sai ya fado ya yi fim. Ka ga shi wanda ya dauki nauyi, babu abin da ya sani sai riba.
Haka muka bar wancan tafiyar. Sai dai mu kalli fim din Indiya. Sai a ce je ka kalli fim kaza, kai ne za ka fito a matsayin wane. Ka san rigimar da suka yi da wane, haka muke so ku yi. Ana cikin haka ne sai Allah Ya kawo masana daga jami’a.
Misali Farfesa Abdullahi Uba Adamu, tsohon Shugaban Jami’ar NOUN. Sai ya rika ba mu shawarwari. Sai dai ya tabbatar an samar da damar da mutum zai iya yin karatun fim ya yi digiri a BUK. Amma har yanzu yaranmu na yanzu su nawa ne suka je suka koyo harkar? Sun fi son su samu ubangida kawai su fado a rika sa su a fim.
Yaya za a yi a gyara?
Kawai a nemi ilimi kuma a sa ilimi a ciki. Kullum maganata ke nan a rika sa ilimi a cikin lamarin. Jahili ba ya samun nasara a ko’ina.