✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na goyi bayan Buhari – Farfesa Utomi

Aminiya ta samu tattaunawa da fitaccen dan siyasar nan kuma kwararre a fannin tsimi da tanadi, Farfesa Pat Utomi inda ya warware zare da abawa…

Aminiya ta samu tattaunawa da fitaccen dan siyasar nan kuma kwararre a fannin tsimi da tanadi, Farfesa Pat Utomi inda ya warware zare da abawa kan wasu batutuwa da suka shafi siyasar kasar nan da kuma alakarsa da Shugaba Muhammadu Buhari da dalilan da suka sa ya goya masa baya a zaben da ya gabata:

Ka yi wa Buhari kamfe a lokacin da yake yakin zabe, me ya ba ka sha’awa ka shiga tawagarsa?

Sha’awata ta kawo canji a siyasar Najeriya wacce za ta inganta rayuwar talaka ita ce ta sanya na yi masa kamfe kuma wannan ra’ayi na kawo canji ya samo asali ne tun farko a lokacin ina dalibi a Jami’ar Nsukka. Ni mutum ne mai yaki da rashin adalci, haka rayuwata take. Idan kuka koma tarihina lokacin ina Kwalejin Loyola da ke Ibadan, na kasance mafi kankata a ajinmu amma kuma ina fada da manya da suke cin zalin dalibai. A rayuwata na tsani rashin adalci shi ya sa nake yakarsa. Haka dabi’ata take, har lokacin da na dawo daga karatu a kasashen waje inda na yi karatun digirin digirgir. Na yi imanin zan iya kawo canji a duniya baki daya, shi ya sa a digirorin da na yi a fannoni da dama da suka hada da fannin aikin jarida da siyasa da tsimi da tanadi da sauransu, su nake hadawa ina fassara duniyar da ke kewaye da ni. Kuma da haka na yi nazari na ga ya dace mu canja gwamnatin da ta shude, abin bai zo da sauki ba.
Ba karamar gwagwarmaya muka yi ba.A baya na tsunduma cikin gwamnati ina dan shekara 27 a gwamnatin Shagari. Sai dai gwamnatin ba ta yi tsawo ba, amma kuma haka ya koyar da ni darasi a rayuwa. Idan ba ka kan matsayin da za ka kawo canji kada ka damu. Shi ya sa na ce ba zan shiga gwamnati ba sai a matsayin da zan iya kawo canji, tuni na gano haka a rayuwata. Daga nan sai na fahimci cewa lokaci ya yi da za mu kawo canji a kasar nan. Yayin da na fahimci cewa gwamnatin Jonathan ta zo karshe sai na fara tunanin cewa za mu yi nasarar kawo canji da nake tunani. Kuma abin sai ya kasance wani iko na Ubangiji domin idan da mutanen nan sun ci gaba da mulki da abin zai kara tabarbarewa, to shi ya sa ka ga na shiga yi wa Buhari kamfe.

Wasu jaridu sun ruwaito cewa ba a sanya sunanka a jerin wadanda Buhari zai nada ministoci ba, kuma wasu na zargin cewa burinka shi ne ka yi aiki a gwamnati Buhari, me za ka ce kan haka?
kasar nan tana ba ni mamaki, ni da na tsaya takarar Shugaban kasa, me suke nufi da ina da burin na kasance cikin gwamnatin wani. Na yi takarar shugabancin kasar nan ne don na kawo canji, to me za su ce yayin da marigayi Shugaba ’Yar’aduwa ya neme na karbi mukami amma na ce masa ba na bukata? Kuma me za su ce game da gayyatar da gwamnatoci suka rika yi mini, wannan zancen shirme ne, ina mai tabbatar maka da cewa ban damu ba, ana damawa da ni ko ba a damawa da ni?

To, idan Buhari ya yi maka tayin mukami za ka karba?
Idan aka bukaci na yi abin da ya dace, ba komai zan yi ba, domin idan ka bukaci in yi wani abu wanda a ganina ba zan bayar da gudunmawa ba, zan gaya maka cewa na gode a kai kasuwa, daga gefe ma zan iya bayar da gudunmawata.

Mutane na zargin cewa ka soki lamirin gwamnatin Shugaba Jonathan kuma ka soki tsare-tsarenta na tattalin arziki amma kuma kai kanka lamarinka a baki ne kawai, ba ka aiwatar da abubuwan da kake fadi, me za ka ce kan haka?
Me kake so na ce a kan haka? Abin da nake son in yi a aikace?

Abin da muke nufi shi ne abubuwan da za ka yi idan aka nada ka mukamin a gwamnatin Buhari?
Idan na samu dama za ka gani.

Kwamitin mika mulki na Joda ya ce gwamnatin da ta gabata ta bar basussuka masu yawa kuma ta barnatar da kudi. Kana ganin wannan ba wani tarko ne aka dana wa Buhari ba don ya kasa cika alkawuran da ya yi wa ’yan Najeriya ba?

Ba sai ka zama kwararre ba sannan za ka fahimci cewa abubuwa sun tabarbare a kasar nan. Bari in ba ka misali. Farashin mai ya ragu zuwa kasa da Dala 50 ga kowace gangar danyen mai, hakan ya sa muka shiga dimuwa, domin ni da kai mun san ba a biya albashi na watanni ba amma a shekarun baya akwai lokacin da farashin mai ya dawo dala 10 a kowace ganga lokacin mulkin Sani Abacha amma gwamnati ba ta rude ba, kuma duk da haka Abacha ya bar biliyoyin daloli a asusun ajiyar kasar nan. A ra’ayina yadda mutane suke tattauna batutuwa a kasar nan shi ya janyo kwararru ba sa son shiga tattaunawar da suke yi. Shi ya sa ka ga mun tsaya a wuri daya mun kasa ci gaba. Ina karanta musayar ra’ayin da matasa suke yi a kafofin sadarwa, za ka ba su damu su ilimantar da kansu ga duk wani abu da ya shige musu duhu ba, wani lokaci sai ka ga sun tashi sun zagi kowa da kowa, ka ga haka zai cutar da rayuwarsu. Shi ya sa kasar nan tana bukatar tsabtatacciyar kafa da mutane za su rika bayyana ra’ayinsu. Mutane suna da ’yancin bayyana ra’ayinsu, amma ya kamata su daina zagin jama’a. Je ka duba rubuce-rubucen da na yi a jaridu da mujallu ban taba zagin wani ba, zan soki ra’ayin mutum amma ba zan zage shi ba, don haka cin mutunci ne. A nan Najeriya ne mutane suke cewa ka ce kaza, ka ce kaza ka cika sukar lamirin jama’a. Akwai lokacin da nake rubutu duk mako a jaridar banguard shekaru da dama da suka wuce mai lakabi ‘Ra’ayin Tunani’ ina rubuta wani a mujallar Business Concord duk ranar Juma’a da jaridar Guardian, sai wani abokina ya ce min kai kadai ne a Najeriya, kai ne Mataimakin Darakta a kamfani kaza kuma a lokaci daya kana rubutu a jaridu da mujallu kusan uku ya kamata ka daina. Ni kuma tunanina shi ne ina bayar da gudunmawata ce amma ban san cewa ina takura wa jama’a ba sai na daina. Bayan wata uku sai jama’a suka fara cewa Pat Utomi ya karbi kudi ya daina magana. To me suke so mutum ya yi? Sai suka fara cewa ya kamata in ci gaba da rubuce-rubucen da nake yi. Ya kamata’yan Najeriya su fahimci irin dabi’ar da za su rika yi, wasu sai suka rika ce min ka koyi yin biris da maganganun jama’a. Akwai mutane da saboda ba sa son su bata wa wani sai ka ga sun bar wata shawara a cikinsu, ita kuma al’umma sai da shawarwari take ci gaba.

Wata guda ke nan da rantsar da Buhari a matsayin Shugaban kasa, amma har yanzu bai nada ministoci da za su taimaka masa jagorancin jama’a ba, ka damu da haka kuma mene ne ra’ayinka kan matasa wa sabuwar gwamnati ta nada ministoci?
Akwai bambance-bambance wajen tunkarar matsaloli. Idan da a ce ni ne Shugaban kasa zan fuskanci abin ta wata hanya, amma ni ban san dalilan da suka sa ya zabi ya yi haka ba. Ban samu damar jin dalilin da ya sa ya yi haka ba. Amma tabbas a ganina dalilin da ya sa ya yi haka shi ne na daya bayan kwana uku ko hudu da rantsar da shi, an yi rika yada jawabin da ya yi a kafafen watsa labarai don kowa ya ji bayanin inda gwamnati ta sa gaba a fannoni da dama har zuwa kusan kwana 30 kuma daga bisani aka rika sanar da tsare-tsaren da ake so a yi. Wani dalili shi ne akwai matsaloli da yawa da suke bukatar agajin gaggawa, wannan shi ne yadda nake fahimtar abubuwa.
Mutane irin su Femi Falana sun damu da yadda Buhari yake hulda da kasashen Yamma musamman wadanda suka fi karfin tattalin arziki. Kana ganin kuskure ne gwamnatin ta yi aiki da kasashen Yamma ko ta tsaya a ’yar ba-ruwanmu kamar yadda aka san ta?
Femi abokina ne, amma muna samun sabani a wasu batutuwa saboda bambancin inda muka fito. Abu ne da ke cikin tarihi ko lokacin da nake jami’a ba na ra’ayin wasu jam’iyyu da akidu. Ni Jam’iyyar Dimokuradiyya ta Kiristoci nake sha’awa. Haka muka taso shi ya sa ra’ayina ya bambanta, amma akidar daya ce, ita ce ta taimaka wa talaka. Lokacin da na dawo daga karatu a kasashen waje na rika shiga tattaunawa a wurare da dama har aka rika kirana da sunaye daban-daban. A lokacin Ayu ya zama shugaban majalisa ni kuma ina shugaban cibiyar kasuwanci, sai Ayu ya kira ni cewa yana so ya gana da masu kamfanoni, nan take na tara masa mutum 300. Aganina shi ne ciyar da mutanenmu gaba, ta iya yiwuwa Femi yana da matsala da haka, amma ni ba ni da wata matsala da haka kuma wannan ba ya nufin cewa ni da Femi ba mu hada ra’ayi daya ba na burin ganin an inganta rayuwar al’umma. Ina tunatar da jama’a irin wadannan abubuwa ina kawo musu misali lokacin da aka nada Enrikue Fernando Cardoso a matsayin Ministan Waje na Brazil kuma tsare-tsaren da ya kawo su ne suka kawo wa kasar ci gaban da ta samu, a yanzu Brazil tana daya daga cikin kasashe mafi girman tattalin arziki a duniya, yanzu ba lokacin cacar baki ba ne lokaci ne a aiki a kasa.

Shin kai dan Jam’iyyar APC ne?
Tun ranar farko na fito daga kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ne na shiga Jam’iyyar APC.

Majalisar Dokoki ta shiga rudani saboda rikicin shugabanci, me wannan ke nunawa kuma ta yaya gwamnatin Buhari ya kamata ta tunkari batun?
Ita gwamnati kamata ya yi ta kasance ta kowa da kowa kuma yana da muhimmanci wadanda za su jagoranci majalisar su kasance masu akidar canji don kada ya zamo an yi wa ajandojin gwamnati tarnaki. Domin idan ya kasance wadanda suke shugabancin majalisar ba su daga cikin wadanda mutane suka zaba su kawo musu canji, to ka ga lamari ya baci. Ina da ra’ayin cewa ya kamata jam’iyya ta yi wani abu ta duba ajandar kasa, ba ta wani mutum shi kadai ba. Ba ni da wani kaidi ga wadanda suke jagorancin jam’iyya, amma idan ka kauce wa ajandar gwamnati, to, fa za a fada cikin matsala babba. Saboda haka babbar matsalar da take damun kasar nan ita ce sanya siyasa a cikin lamura har ta kai siyasar ta dauke hankulan jama’a. Saboda haka kamata ya yi a mayar da hankali wajen cika alkawarin da aka yi na kawo canji a kasar nan amaimakon a tsaya ana bata lokaci wajen sanya siyasa a batutuwa.