Matar tsohon shugaban ’yan tawayen Biyafara, Ambasada Bianca Ojukwu, ta bayyana dalilin da ya sa ta mari matar tsohon Gwamnan Jihar Anambra mari.
A ranar Alhamis ce dai Bianca ta mari Misis Ebelechukwu Obiano, ana tsaka da bikin rantsar da Farfesa Charles Soludo a matsayin sabon Gwamnan jihar.
- Kannywood: Lawan Ahmed zai tsaya takarar dan majalisa
- Duk abin da muke yi ’yan sa-kai ne suka koya mana – Turji
Lamarin dai ya jawo cece-kuce matuka, musamman a shafukan sada zumunta na zamani, inda hatta sabon Gwamnan sai da ya nemi afuwar jama’a.
Sai dai a cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Juma’a, Misis Bianca ta bayyana hakikanin abin da ya faru.
Ta ce, “Lokacin da aka fara bikin rantsar da Farfesa Charles Soludo da Mataimakinsa, matar tsohon Gwamna, Misis Ebelechukwu Obiano, ba ta wajen.
“Ta zo ne bayan kamar awa daya da rabi da fara taron. Ni ban ma lura da zuwan nata ba.
“Cike da mamaki, sai ta taso ta taho wajena, kamar za ta gaisheni. Amma a maimakon haka, sai ta tsaya a kaina ta fara daga murya tana fada min bakaken maganganu wadanda ko kare ba zai ci ba, tana cewa wai me ya kawo ni wajen.
“Ta tambayeni ko na zo taya su murnar barin ofis ne, amma na yi banza da ita. Amma sai ta ci gaba da dora hannunta a kan kafadata, tana fada min maganganu.
“Sai na bi shawarar wadanda suke zaune a kusa da ni cewa na yi watsi da ita, amma na ce ta daina taba kafadata.
“Amma sai ta ci gaba, har tana kokarin cire min kallabi amma ba ta yi nasara ba. Wannan ba karamin raini ba ne a al’adar Ibo.
“A daidai nan ne na tashi na kare kaina, inda na wanka mata mari sannan na cire mata hular gashin kanta.
“Abin da ya fi kona min rai shi ne a mankas take, don ko numfashinta ya nuna hakan. Ta yaya za a yi matar Gwamna ta yi mankas da giya sannan ta fito wajen taro a haka? Wannan ba karamin abin kunya ba ne musamman ga tsohon Gwamnan, wanda janye ta suka bar wurin nan take.
“Cikin ikon Allah lamarin bai kawo cikar ga bikin rantsuwar ba, haka na tsaya har aka kammala, kafin daga bisani mu wuce Gidan Gwamnati don wata gagarumar walima,” inji Misis Bianca Ojukwu.