✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na ce Rahama ta ba Gwamna Ganduje da Sarkin Kano Hakuri

Dan wasan Kannywood da Nollywood Ali Nuhu ne ya yi sanadiyar hakurin da ‘yar wasa Rahama Sadau ta bai wa gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi…

Dan wasan Kannywood da Nollywood Ali Nuhu ne ya yi sanadiyar hakurin da ‘yar wasa Rahama Sadau ta bai wa gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu bisa abubuwan da suka jawo dakatarta da ita da aka yi daga masana’antar finafinan Hausa a shekarar da ta gabata.

Idan ba a manta ba, Qungiyar MOPPAN ta yanke shawarar dakatar da Rahama ne saboda shiga mara kyau da ta yi a wani bidiyon waka tare da mawaki dan Jos, wanda aka fi sani da ClassiQ

Ali Nuhu a tattaunawarsa da Daily Trust/Aminiya ta wayar tarho yayin da da yake kan hanyar barin qasa, ya bayyana cewa ‘yar wasan ta yanke shawarar bayar da hakuri ne bayan ta gano laifuffukanta, sannan ya kara da cewa dan Adam ajizi ne.

“A matsayinmu na dattawa a masana’antar, wajibi ne a kanmu mu nuna wa matasa hanya ta kwarai, hakan ya sa na ba Rahama shawara da bayar da hakurin.

“A rayuwa, yana da kyau mutum ya rika gyara da bayar da hakuri duk lokacin da ya yi laifi. Rahama ta dau wannan babban mataki na bayar da hakurin, kuma ta dauki alkawarin cewa ba za ta sake maimata abin da ta yi ba. kuma ta rubuta wasika zuwa ga qungiyar MOPPAN kuma ina kyautata zaton cewa mahukunta MOPPAN suna nan suna tattaunawa akan wasikar,” Inji Ali Nuhu

Yar wasan ta bayar da hakurin ne a shirin rediyo, “Ku Karkade Kunnuwanku” a fitaccen gidan rediyo a Kano, inda ta yi  alkawarin cewa “hakan ba zai sake faruwa ba”