✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na amince da kungiyar IFK Norrkoping na Sweden – Ishak Abdulrazak

dan wasan Najeriya na ’yan kasa da shekara 17 Ishak Abdulrazak ya shaida wa Aminiya cewa ya sanya hannu a takardar kwantiragi da kungiyar IFK…

dan wasan Najeriya na ’yan kasa da shekara 17 Ishak Abdulrazak ya shaida wa Aminiya cewa ya sanya hannu a takardar kwantiragi da kungiyar IFK Norrkoping ta kasar Sweden.

Abdulrazak wanda ake yi wa lakabi da Golden Boy a Kaduna yana cikin ’yan wasan kasa da shekara 17 da suka fafata a wasannin share-fage duk da cewa ba su samu nasarar tsallakawa zuwa gaba ba.

A tattaunwarsa da Aminiya ta tarho, Abdulrazak ya tabatar da cewa lallai ya sanya hannu a kwantiragin, inda ya ce “Da gaske ne, yadda abin ya faru shi ne mun yi wasa na musamman a Abuja inda masu neman ’yan wasa daga kasashe da dama suka halarta. Na yi kokari matuka shi ne wakilan kungiyar ta IFK Norrkoping suka nuna sha’awarsu a kaina. Duk da cewa akwai wasu wadanda suka nuna sha’awarsu a kan in je wajensu, amma yanayin yadda ’yan Swededn din suka doge a kaina, suka nuna cewa lallai fa suna bukatata, shi ya sa manajan da ke kula da harkokina ya amince da su. Ita kwallo, mutum na bukatar inda aka yarda da shi ne, idan ana son ka sosai za a fi ba ka dama ka nuna bajinta da iyawarka a fili.”

Da wakilinmu ya tambaye shi a kan me ya sa a gaba yanzu, dan shakara 16 din ya ce “Kasancewar na taba buga wa Najeriya ’yan kasa da shekara 17, ban san ko zan sake komawa in buga a wannan rukunin ba duk da cewa har yanzu shekarata 16 ne. Ke nan shekaruna ba su wuce ba. Amma dai ba ni da tabbaci a kan wannan. Abin da ke nan dai yanzu shi ne in ci gaba da kokari kamar yadda na saba domin gaba ta fi baya yawa.”