kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedikwata a garin Jos ta shirya musabaka na karatun al-kur’ani a tsakanin makarantun Islamiyya na karamar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna wanda ta gudanar a garin Tafa (da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja), inda ta raba kyaututtukka ga wadanda suka zama zakaru a rukunonin izufi daban-daban, kwanakin baya.
A jawabin da ya yi a yayin rufe musabakar Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar reshen karamar Hukumar Malam Haruna Ahmad Bunkau ya bayyana cewa sun zabi shirya musabakar a garin Tafa ne don nunawa duniya cewa garin Tafa na da abubuwan alheri wanda ya hada da koyawa ’ya’yansu karatun addini sabanin al’amuran badala da a ke danganta garin da shi. Dagacin Tafa Malam Shehu Sulaiman godewa kungiyar ya yi na shirya musabakan kur’ani duk shekara a garin Tafa tare da gayyato baki daga nesa da kusa, ya ce hakan zai kankare kaurin suna da garin ya yi da ya ce ba gaskiya ne ba.
Sakataren ilimi na karamar hukumar Kagarko wanda ya wakilci shugaban yankin Malam Shehu Musa kira ya yi ga iyaye da su kara azama wajen sanya ’ya’yansu a makarantun addinin da na boko ya ce ilimi shi ne jari kadai da ba a raba mutum da shi sabanin mulki ko dukiya. Sauran wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun hada da ko’odineta na musabakan alkur’ani na kungiyar a Jihar Kaduna, da kuma takwaransa na yankin birnin tarayya Abuja. Wadanda suka zo na daya a rukunoni daban-daban a yayin gasar, za su wakilci karamar hukumar a musabaka na matakin jiha da za a yi zuwa gaba.
Abin da ya sa muka shirya musabakar al-kur’ani a garin Tafa – kungiyar JIBWIS
kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) mai hedikwata a garin Jos ta shirya musabaka na karatun al-kur’ani a tsakanin makarantun Islamiyya na karamar…