✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka sanya wa unguwarmu Sabo dangote – Hausawan Ile-Ife

Al’ummar Hausawan Ile Ife da aka lalata wa gidaje da kadarori a lokacin rikicin kabilanci na ranar 8 ga watan Maris, sun rada wa Unguwar…

Al’ummar Hausawan Ile Ife da aka lalata wa gidaje da kadarori a lokacin rikicin kabilanci na ranar 8 ga watan Maris, sun rada wa Unguwar da suke zaune sunan Sabo dangote. Sun dauki wannan mataki ne domin nuna jin dadi da samun tallafin kudi daga Gidauniyar dangote da suka fara aikin sake gina gidajensu.

Mako uku da wucewa ke nan da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi  da Shugabar Gidauniyar dangote Uwargida Zuwaira Yusuf suka jagoranci raba kudi Naira miliyan 50 da Gidauniyar ta bayar ga mutane 220 Hausawa da Yarbawa da rikicin ya shafa.

Wasu daga cikin Hausawan da suka fara gudanar da ayyukan sake gina gidajensu bayan samun tallafin, sun yi godiya ga Allah (TWT) da ya aika musu da wannan mutumi Alhaji Aliko dangote da Gidauniyarsa ta bayar da tallafin kudi Naira miliyan 50 domin rabawa ga wadanda suka yi hasarar kadarori a lokacin rikicin.

 “Murna da farin ciki ne ya sa muka rada wa sunan Unguwarmu Sabo dangote. Kuma mun yi haka ne da amincewar shugabanninmu da sauran jama’a” inji su.

Sun mika irin wannan godiya ga Sultan na Sakkwato Alhaji Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, wanda ya yi tattaki zuwa garin Ile-Ife a lokacin da aka yi rikicin domin jajanta musu tare da yi musu alkawarin mika bukatar tallafi ga Aliko dangote, wanda aka cika. Su ma tsofaffin Gwamnonin Jihohin Kano da Sakkwato Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa da suka kai ziyarar jaje sun samu irin wannan godiya daga al’ummar Hausawan Ile-Ife.

Wakilinmu da ya kai ziyarar ganin irin yadda ayyukan sake gina gidajen ke gudana ya ce, a yayin da irin wadannan mutane suke farin ciki akwai wasu ’yan uwansu da suka yi hasarar kadarori ba tare da samun irin wannan tallafi ba. Alhaji Salisu Adamu Mai Takalmi yana daga cikin wadanda ba su samu tallafin ba. 

Ya ce, “gaskiya ne an lalata mini motoci da kadarori masu yawa, amma ban samu tallafin ba. A maimakon bakin ciki ma wallahi farin ciki nake yi da ‘yan uwa na suka samu, domin ka san cewa duk abin da ba ka samu ba to daga Allah ne. Muna da yawa da ba mu samu tallafin ba, bayan barnar da aka yi mana. Muna mika kukanmu ga Allah da Gwamnati da wannan Gidauniya ta dangote da su duba matsalarmu.”

Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali shi ne ya umarci wasu Hakimansa guda biyu wato Tafidan Ile Ife Alhaji Husaini Salisu Muhammed da Makaman Ile Ife Alhaji Awalu Abubakar da su zagaya da wakilinmu domin gane wa idanunsa irin ayyukan sake ginin gidajen da ake kan yi a Unguwar ta Sabo.

Muhimman abubuwan da wakilinmu ya gani a lokacin ziyarar sun hada da wasu jami’an ‘yan sanda dauke da bindigogi da motocin aiki da aka girke su domin tsaron lafiya a unguwar ta Sabo. A bangaren irin ayyukan da ake yi kuwa, akwai tarin tubalin bulo da yashi da kwanukan rufi da katakai masu yawa tare da ma’aikatan birkiloli da leburori da kafintoci da suke gudanar da ayyukansu a gidaje daban-daban. Wasu masu gidajen da aka yi wa kwaskwarima an kammala aikinsu a yayin da masu rusassun gidaje suke shirin fara aikin a nan gaba.

Da yake bayani a kan wadanda ba su samu irin wannan tallafi na Gidauniyar dangote ba, Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali, wanda fadar shi tana daga cikin gidajen da aka lalata cewa Ya yi  “kuskure aka samu wajen rubuta sunaye da aka tsallake sunayen gidajen wadannan mutane da irin kadarori da suka yi hasararsu. Kamar yadda wadannan mutane suka dogara da Allah suka jajirce ba tare da nuna damuwar rashin samun tallafin ba, muna fatan Gidauniyar ta dangote za ta sake duba lamarinsu.”

Dangane da hada sunan dangote da sunan unguwar ta su, sai Sarkin Hausawan ya ce, “idan akwai abin da ya fi haka to za mu yi, domin ya cancanta ya samu fiye da haka daga gare mu. Akwai gidaje masu yawa da aka rusa su da kona su kurmus, wanda mazauna cikinsu suka koma a rakube cikin gidajen makwabta a cunkushe. Wasu kuma sun yi kaura zuwa wasu garuruwa daban, amma wannan tallafi da Alhaji Aliko dangote ya bayar ya taimaka wajen sake gina wadannan gidaje da jama’a suka fara komawa cikin gidajensu.” inji  shi.

Sarkin Hausawan ya mika godiyarsa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da dukkan Sarakuna Arewacin kasa da tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa da kungiyoyin Musulmi da dukkansu suka taimaka da kudi da kayan aiki da shawarar yadda za a yi maganin aukuwar irin wannan rikici a nan gaba.