Barista Khadijat Abdullahi Adamu matan tsohon Gwamnan Jihar nasarawa ce. Lauyar ita ce shugabar babban cibiyar kare haqqin yara qanana da mata da ake kira Child Right Foundation a Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana ayyukan cibiyar inda ta kuma ba wa mata ’yan uwanta shawarwari da sauran batuttuwa da suka shafi rayuwansu. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me ya baki sha’awar kafa wannan cibiya?
Da farko dai bari in baka takaitaccen tarihin wannan cibiyarmu da ke da manufar kare yancin yara qanana da mata wato wadanda ake kira Child Right Foundation. Na qirqiro ko in ce na kafa cibiyar ne a shekarar 2002, a lokacin da maigidana ke riqe da matsayin gwamnan jihar nan. A lokacin kuma kamar yadda ka sani tsohon Shugaban Qasa Olusegun Obasanjo na kan mulki. Akwai wani taro na farko da matan gwamnonin jihohin qasar nan baki daya muka gudanar a lokacin wanda marigarya Misis Stella Obasanjo ta jagoranta. A lokacin taron Misis Stella ta shawarci kowace matan gwamna cewa ta je ta bincika ta gano matsaloli da al’ummominta musamman mata da qananan yara ke fuskanta ta ga wannan qungiya ko cibiya za ta kafa don magance matsalar. Da muka dawo gida sai na yi tunani cewa tun da dama kafin in samu wannan dama ina da burin taimakawa mata da yara a jihar nan saboda haka me zai sa bazan kafa cibiya da zan riqa tallafa tare da kare hakin mata da yara a jihar nan ba, kasancewa akwai matukan buqatan yin haka. Saboda haka ne ya sa banyi wata-wata ba na kafa cibiyar wanda ke cikin garin Lafiya fadar jihar nan.
Aminiya: Ko za ki bayyana wasu daga cikin ayyukan cibiyar?
Kamar yadda na bayyana da farko cibiya ce da ke kare hakin yara qanana da mata da masu nakasa da marayu da sauransu. Muna fafutukar kare hakin wadannan bayin Allah ne a cibiyar ta hanyan qirqiro tare da aiwatar da shirye-shirye da ke inganta rayuwansu. Misali mukan kai kuka ga gwamnatoti a dukan matakai a madadinsu don tabbatar an tallafa musu da abubuwa da za su inganta rayuwansu kamar ta fannin karatunsu da jari da kulawa da lafiyansu da sauransu. Haka kuma mukan tafi qauyuka don gudanar da tarurruka, inda muke wayar da kawunan al’umma musamman mata da yara game da mahimmancin ilimi da dogara da kai da sauransu. Babban aiki da zan ce muna yi kuma a cikin ayyukan cibiyar shi ne na yin magana da babbar murya a duk lokaci da aka taka ko ake so a take ’yancin wadannan mutane. Aikin mu ne mu nuna rashin amincewarmu da duk wata doka ko tozartawa ga wadannan bayin Allah. Muna kuma kai ziyara gidajen marayu da asibitoci muna tallafa wa marasa lafiya da sauransu da kayayyakin abinci da magunguna da sauransu. Wadannan dai su ne kadan daga cikin ayyuka da muke gudanarwa a cibiyar, don idan na ce zan bayyana duka zan dade ban kare ba don muna gudanar da ayyukan taimako da dama a wannan cibiya.
Aminiya: Kasancewa cibiya ce da ke zaman kanta. Ta ina kuke samun tallafi ko kudi da kuke gudanar da wadannan ayyuka?
Kamar yadda ka fada cibiya ce da ke zaman kanta ba ta gwamnati ba ce. A nan dai zance babban hanya daya tilo da muke samun tallafi muna gudanar da ayyukanmu shi ne mukan ba da gudumawa ne tsakaninmu shugabannin cibiyar, wato wadanda suka qunshi daraktoci da sakatarorin cibiyar. Ma’ana mu shugabannin wannan cibiya ne muke tallafawa kanmu wajen gudanar da harkokin cibiyar. Kuma muna yin haka ne ba tare da gunaguni ba, don musan mahimmancin yin haka. Allah yana kuma saka mana a kodayaushe sakamakon haka shi ya sa muke ci gaba da yi ba fashi.
Aminiya:Wadannan nasarori kuka cimma a cibiyar kawo yanzu?
A gaskiya mun cimma nasarori da dama a cibiyar da yardan Allah. Ka ga mitsali akwai wani shiri na musamman da muka tsara muka kuma aiwatar wa mata masu juna biyu da ke dauke da cutar qanjamau. Akwai wasu magungunan rigakafi na musamman da muke ba wadannan mata don kada jariran da ke cikinsu su kamu da cutar. Kuma Alhamdulillah shirin yana aifar da da mai ido don kawo yanzu mun samu gagarumar nasara a fannin kasancewa wadannan yara da mata masu dauke da qwayar cutar suke haifa ba su kamu da cutar bayan an haifesu ba. A gaskiya aguna wannan ma kawai babbar nasara ce. Kuma mukan za ga qananan hukumomin jihar nan muna fadakar da al’umma baki daya game da illar cutar qanjamau da hanyoyi da yakamata su bi don su kare kansu daga kamuwa da cutar da sauransu. Muna kuma fadakar da su game da mahimmancin ilimin zamani dana addini a rayuwansu. Har ila yau, muna ba da tallafin karatu wa ’ya’ya mata qanana da dama muna kuma saya musu takardu da biya musu kudin makaranta da sauransu. Hakazalika, mukan shawarce su cewa duk wanda bai samu damar karatuba sai ya kama sana’a don ya dogara da kansa. Har ila yau, zan ce wadannan marasa galihu musamman mata da qananan yara da marayu da sauransu kawo yanzu sun samu tallafi da dama a hanyoyi daban-daban daga gwamnatin jihar nan har ma da gwamnatin tarayya sakamakon kai kukansu da muke yi a kullun ta wannan cibiyarmu. Kuma su kansu da suke amfana damu suna nuna godiyarsu a kullum wa cibiyar. Saboda haka a taqaice dai zan iya cewa Alhamdulillah kawo yanzu cibiyar tana cika burin kafata wanda hakan ba shakka yana kara mini da sauran ma’aikatanmu baki daya kwarin gwiwa muna cigaba da sadaukar da komai wajen daukaka harkokinta kuma ba shakka ina samun farin ciki da annashuwa a rayuwata sosai game da haka.
Aminiya: Akwai wasu qalubale da kuke fuskanta a cibiyar?
A gaskiya kamar yadda ka sani ba a samun nasara a duk wani abu da mutum ke yi a rayuwa ba tare da fuskantar matsala ba. Anan zan ce babban matsalar da muke fuskanta a cibiyar ita ce ta kudi.