✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka gudanar da kididdigar masu kanjamau – Dokta Sani Aliyu

Dokta Sani Aliyu, shi ne Darakta Janar na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Najeriya (NACA). Babban jami’i kuma babban likita a Jami’ar Cambridge da…

Dokta Sani Aliyu, shi ne Darakta Janar na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Najeriya (NACA). Babban jami’i kuma babban likita a Jami’ar Cambridge da ke Ingila kafin Shugaban Kasa ya nada shi shugabancin hukumar, kwararre ne kan cututtuka masu yaduwa da kananan halittu. Ya shaida wa Aminiya halin da ake ciki kan kididdigar masu cutar kanjamau da hukumarsa ta gudanar a kasar nan da sauran batutuwa:

 

Mun samu labarin hukumarka ta gudanar da kididdigar masu cutar kanjamau a kasar nan yaya lamarin yake?

Ina jin kana magana ce kan Ma’aunin Kanjamau na Najeriya da kuma Kididdigar Illarta (NAIIS) da Shugaban Kasa ya kaddamar a bara a watan Yuli. Wannan shi ne abin da muke kira adadin kididdigar da ya ginu kan gidaje. Ma’ana muna daukar samfuri ne daga iyalan gida a tsakanin jama’a. Dalilin da muka yanke shawarar mu yi wannan tare da abokan hadin gwiwarmu shi ne domin muna da manyan matsaloli wajen gano hakikanin adadin mutanen da suke dauke da kanjamau a kasar nan.

Me ya sa kuka kaddamar da kididdigar?

Shirye-shiryen da aka dauki shekaru ana gudanarwa sun nuna akwai matukar wahala a gano masu dauke da cutar kanjamau da za a dora su a kan magani a Najeriya. Akasarin bayanan adadinsu da muke samu ko dai daga gwamnatin Amurka ko daga masu bayar da tallafin kudi na duniya. Duk shekara mukan gaza cimma mutanen da ake son kaiwa gare su. Sun shaida mana cewa suna so mu dora ’yan Najeriya dubu 150 a kan magani. Amma a karshen shekara sai su gaza samun mutum dubu 150 din. A yanzu inda muna cimma mutanen da muke son isa gare su a shekara hudu zuwa biyar da muna da mutum miliyan daya da rabi da suke karbar magani, amma sai dai muna da mutum miliyan daya da dubu 100 da suke karbar magani. Wannan ne ya sa muka yanke shawarar mu tunkari abokan hadin gwiwarmu musamman gwamnatin Amurka da masu ba da tallafi na duniya saboda ba mu da isassun kudin da za su kai Dala miliyan 91 kafin a gudanar da wannan kididdiga.

Yaya za ka kwatanta wannan kididdiga da wadanda suka gabace ta?

Wannan kididdiga ga alama ita ce mafi girma da aka gudanar gida-gida a kasa daya a duniya. Mun dauki wata shida muna kididdigar gwaji. An kammala a watan Disamban bara kuma a wannan wata na Maris ne Shugaban Kasa zai gabatar da sakamakon ga jama’a.

Za ta canja yadda ake daukar batun kanjamau gaba daya a kasar nan.  A karo na farko za mu iya fitowa fili mu ba ku abin da ya fi zamowa daidai kan adadin mutanen da suke dauke da cutar kanjamau, ina aka fi daukarta da ina ya fi kamata mu fi mayar da hankali, kuma ta yaya za mu iya shawo kan wannan annoba.

Ina matukar godiya ga ’yan Najeriya kan yadda suka taimaka mana da wannan, an gudanar da kididdigar ce ta hanyar da ta dace. Sauran kasashe sun yi irin wannan kididdiga, Najeriya ce ta 13. Sauran kasashe na Kudancin Afirka sukan dauki shekara suna tsara yadda za su gudanar da kididdigarsu shekara kafin su fitar da sakamakon rahoton. Amma sai muka tattakura komai a cikin wata tara. Shi ne ma’auni mafi inganci da muka samu mutanen da suka dace a Najeriya, mutanen da suke iya kawo ingantaccen aiki idan aka zo batun kididdigar cututtuka masu yaduwa.

Kididdigar kanta tana duba yanayin cututtuka uku ne, tana duba illar kanjamau da cutar hanta ta hepatitis B da C. Kanjamau tana ci gaba da zama babbar abar da ke jawo mace-mace a Najeriya. Amma a hakikanin gaskiya ciwon hanta ya fi jawo matsala ga kiwon lafiyar mutane. Adadin mutanen da suke mutuwa dalilin ciwon hanta na hepatitis B ko C a Najeriya ya fi na wadanda kanjamau ke kashewa. Kuma ba mu damu mu san irin illar da wannan matsala take jawowa ba.

Bambancin shi ne ciwon hanta na hepatitis B, za ka iya yin rigakafinsa ta hanyar allura. Misali idan kana da mace mai ciki da ta harbu da ciwon hanta na hepatitis B, za ka iya ba iyalan gida allurar rigakafi musamman yara, kuma idan ta zo haihuwa za ta samu allurar rigakafin ciwon hanta na hepatitis B, kuma a ba ta magani.

Dokta Sani Aliyu Darakta Janar na Hukumar NACA

Magungunan ciwon hanta na hepatitis B, iri daya ne da magungunan da ake bai wa mai kanjamau. Ga mai kanjamau muna bayar da magunguna uku ne a hade. Ciwon hanta na hepatitis B, kuma 2 daga cikin magungunan 3 da muke ba mai kanjamau su ake amfani da su wajen jinyar ciwon hanta na hepatitis B, abin da muke kira trobada. Shi kuma ciwon hanta na hepatitis C, warkar da shi ake yi, sai dai a yanzu maganinsa yana da matukar tsada. Kuma akwai bukatar mu san mutane nawa ne a Najeriya suke da ciwon hanta na hepatitis C ta yadda akalla za mu yanke shawara kan Naira nawa za mu zuba kuma yaya za mu kawo mu kuma aiwatar da shirinmu na warkarwar. Wasu kasashe kamar Masar suna da manyan tsare-tsare inda suke gwaje-gwaje ga mutanensu kan cutar hanta kuma suna dora kowa a kan tsarin magani don magance cutar ta zamo tarihi.

Kididdigar NAIIS tana da muhimmanci don sanin yadda za cimma nasarar aiwatar da shirin. Ba shakka NAIIS shi ne shaida mafi dacewa da muke da ita da ke nuna cewa idan ka tsara abu da kyau kuma ka san kididdigar masu cutar za ka iya magance ta, amma idan ba ka san adadin abin da kake da shi ba, to duk abin da za ka yi shaci-fadi ne kawai. Ayyukan da aka gudanar a baya a Najeriya ba ina cewa kuskure ba ne, amma ba su da tabbas, saboda girman samfurin ya gaza kuma hanyar da aka bi ta saba. Kuma an gudanar da su ne a gurguje kuma ba mu samu irin tallafin kwarewar da muke bukata ba don cimma nasara. Kuma kafin NAIIS ya fito ina shaida maka kididdigar da aka yi a baya ta nuna Najeriya tana da masu cutar kanjamau miliyan uku da dubu 200.Amma abin da muke kira tabbaci na tsaka-tsaki shi ne wane tabbaci nake da shi da miliyan 3.2. Yana iya zama tsakanin mutum miliyan 2.5 zuwa miliyan 3.6. Kuma yana iya zama daidai ne muna da mutum miliyan 2.5 amma mu ce miliyan 3.2. Amma ta hanyar NAIIS, idan na gaya maka wannan ne adadin, to hakikanin bambancin adadin zai ragu sosai ta kowane bangare zai fi zama adadi na gaskiya. Kuma muna bukatar wannan don tsare-tsaren kasa da zuba jari. Duk lokacin da na gana da wani gwamna nakan shaida musu cewa mun kiyasta cewa mutum dubu 100 suke dauke da cutar kanjamau a jiharka, kuma dubu 18 daga ciki mata ne masu juna biyu, kuma idan na iya bayar da hujja ga gwamnan da ke nuna kashi 99 cikin 100 gaskiya ne, akwai yiwuwar zan iya samun tallafi daga gwamnatin jihar don gabatar da shirin. Amma idan na je wajen gwamnatin wata jiha na ce mutum dubu 100 alhali suna iya kaiwa dubu 150 ko sun kasa haka da kamar dubu 40 ko dubu 60, ko kana da yara dubu shida ko jarirai dubu biyu ba abu ne mai kyau ba ga kowane shiri ya yi haka. Wannan ne ya sa a Hukumar NACA muka dauki shirin NAIIS a matsayin mafi muhimmancin kawo tallafi ga kiwon lafiyar jama’a musamman game da abin da ya shafi kanjamau a shekara 10 da suka gabata.

Babban daukin da aka kawo kan yaki da kanjamau shi ne na kaddamar da shirin bayar da magunguna. Amma wannan shi ne mafi muhimmanci na biyu, saboda shirin NAIIS zai gaya mana ina muka nufa. Sauran kasashen duniya suna kara gusawa gaba idan aka zo batun shawo kan kanjamau. Wasu kasashe sun cire ta daga cikin matsalolin kiwon lafiya da ke bukatar kular gaggawa. Ka je kasar Austireilya ba ta cikin matsalolin kiwon lafiya na gaggawa, matan kasar Kyuba masu dauke da kanjamau sun daina haihuwar ’ya’yan da suke harbuwa da cutar. Kasar Belarus ta magance matsalar kamuwa da cutar daga uwa zuwa dan tayinta. Ka je Ingila a karon farko sun magance matsalar uwa ta harbi tayinta da cutar.  Sauran kasashen na kara ci gaba, to me ake ciki a Najeriya, yaya za mu gusa gaba? Kanjamau tana da matukar tsada wajen magance ta saboda adadin mutanen da suke bukatar a rika ba su maganinta. Tana lashe Naira dubu 50 idan ka dora mutum daya a kan maganin cutar a shekara. Ta yiwu a ga ba kudi ne mai yawa ba, to amma idan kana da mutum miliyan daya da dubu 100 da suke karbar maganin yi jimilla za ka ga ya lashe akalla kashi 60 cikin 100 na daukacin kasafin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, kuma zai yiwu ka kashe kashi 60 cikin 100 na kasafin a kan ciwo guda ba, ba zai yiwu ba.

Shirin NAIIS zai shaida maka wannan shi ne nauyin da ke kanmu game da kanjamau, kuma ya shaida maka adadin mutanen da suke karbar magani da wadanda suka kamata a ce sun shiga tsarin karbar maganin. Wannan ne muke kira cimma kudiri na 90 90 90, yana nufin kashi 90 cikin 100 na masu dauke da kanjamau a kasar nan su yi gwaji su san matsayinsu, kashi 90 na biyu shi ne a cikin kowane mutum 10 a samu 9 na wadanda aka yi musu gwajin an dora su a kan magani suna samun sauki.

Ya zamo ba su da kwayar cutar a jininsu, kuma idan ba su da kwayar cutar a jininsu ka ga ba za su harbi wadansu da ita ba ke nan. Gwargwadon mutane da suke karbar  magani gwargwadon karancin masu harbuwa da cutar.

Hukumar Yaki da Kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya (UNaid) yanzu ta fadada zuwa kashi 95 95 95 domin tana ganin kashi 90 90 90 din ya gaza.

Hanyar da muka yi kididdigar gida-gida ita ce mun je Chibok wurin da yake da wuyar zuwa a Jihar Borno muka dauki samfuri. Wannan ne ya sa na ce ban taba ganin sadaukar da kai a tsakanin ma’aikatan jinya irin wannan ba. sakamakon da muka samu ya nuna mana kiyasin kanjamau a birane kamar Kano kuma ya nuna mana matsalolin kanjamau a kauyukan kewayen Kano ba kawai na alkaryu ba.

Wasu daga yankunan karkara suna neman wuce wasu alkaryu matsalar kanjamau. Idan ka je wurare kamar Benuwai da Nasarawa, matsalar kanjamau ta fi kamari a kauyuka fiye da alkaryu. Wato gwargwadon wayar da kan da ake da shi gwargwadon raguwar kanjamau, gwargwadon karancin ilimi gwargwadon karuwar kamuwa da kanjamau, saboda ba ka san yadda za ka kare kanka ba.

Karuwai aka fi tsoron suna yada cutar yaya lamarin yake yanzu?

An fi samun annobar kanjamau ce a wani rukunin jama’a, ina nufin wadanda suka fi hadarin saurin kamuwa; kamar karuwai wadanda suke saduwa da maza barkatai da masu yi wa kawunansu alluran miyagun kwayoyi, su ne manyan wadanda suka fi kamuwa da kanjamau.

Kanjamau tana da karanci a tsakanin sauran jama’a, amma idan ka dauki masu saurin yada cutar a kan titi za ka iske wasunsu suna da matsalar kamuwa da kanjamau da kashi 18 zuwa 20. A kokarinmu na cike gibi akwai bukatar mu iya isa ga manyan masu yada ta, mu iya gabatar musu da matakan yin rigakafi, mu kawar da kyamar da ake nuna wa wannan rukuni. Ina jin Najeriya mun kashe kimanin Dala biliyan biyar da aka samu daga gwamnatin Amurka kan kanjamau kadai a Najeriya. Ba kanjamau ce kadai matsalar kiwon lafiya ba, muna da sauran matsaloli. Kanjamau cuta ce kawai da take da illa mafi girma idan aka zo batun kudin shiga na kasa (GDP), don haka matsala ce ta ci gaban kasa ba ta kiwon lafiya kadai ba. Za ta iya kawo illa ga bangare mafi karsashi na matasan kasa wadanda suke samar da tattalin arziki ga kasa.

Dubi yadda annobar kanjamau ta gallabi kasashen Afirka Kudu da sahara an samu koma baya a fannin tsawon rai sosai, Afirka ta Kudu ta tagayyara, haka na iya shafar Najeriya.

A wasu sassa na Kudancin Afirka, an samu daukacin kauyen da cutar kanjamau ta shafe shi daga bayan kasa, amma yau mun samu magani. Gaskiya ce mutane suna ci gaba da mutuwa saboda kanjamau a Najeriya, amma adadin ya ragu sosai. Mun kiyasta kimanin ’yan Najeriya dubu 150 suke mutuwa dalilin kanjamau duk shekara, amma wannan adadi ya yi kasa a fiye da shekara goma da suka gabata saboda magungunan suna amfani sosai.

A baya masu kanjamau ana iya gane su, sun rarrame da kan gan su ba su da lafiya, ga kurarraji duk jikinsu. Mutane sun rika firgita, amma saboda wayar da kai da karbar magani yanzu mutane suna da cutar amma suna rayuwa cikin koshin lafiya, wannan kyakkyawan abu ne.

In ka tuna a baya babu isassun kwaroron roba. Sai ka boye za ka saya ko ka je cibiyoyin kiwon lafiya, amma yanzu ba haka ba ne. Sannan me zai sa ba za mu samu cibiyoyin gwaje-gwajen kanjamau na kasuwanci ba. Matukar za su yi aiki su zamo abin dogaro da mutum zai samu saukin auna matsayinsa ya kamata a same su. Kanjamau a kashin kanta ba ta kisa, ita kamar mutum ne ya shiga gidanka ya rika bin jami’an tsaronka daya bayan daya yana kashwae har ya iso kanka. Wannan haka kanjamau yake, idan garkuwar jikinka ya kassara ya rasa karfi sai barazanar kamuwa da cutar ta kankama, kuma ko da an gano kana da cutar daga baya an riga an makara.

Bisa kididdigar da kuka gudanar an samu wani gagarumin canji daga abin da kuka riga kuka nsani ne. Domin akwai jihohin da suke sahun gaba a jadawalin masu kanjamau, za ka ji an ambaci Nasarawa da Benuwai wani lokaci da Anambra, shin akwai wani gagarumin canji?

Ba zan gaya maka hakikanin adadin ba, amma ina shaida maka sakamakon da zai fito zai zamo mai ban sha’awa kuma mai matukar amfani gare mu don manufar tsare-tsare. Amma ba zan fadi zahirin yadda abin yake ciki a yanzu ba, Shugaban Kasa Buhari da kansa ne zai ba mu amsa nan da ’yan makonni.

Wani lokaci da ya gabata masu kanjamau sun yi zanga-zanga kan rashin magugunan cutar, mene ne hakikanin abin da ya faru? 

Ina shaida maka da karfin gwiwa cewa Najeriya ba mu da matsalar magungunan, bilhasali ma muna da magungunan fiye da kima ne idan aka kwatanta da sauran kasashe. Abin da muke fuskanta shi ne kalubalen sauran bangarorin kiwon lafiya. Misali mutanen da suke zuwa asibiti aka dora su a kan magani amma ta yiwu suna fuskantar matsalar kudin zuwa asibitin. Sannan akwai dimbin abubuwan da muke kira bin sawu. Akwai wsu caje-caje inda ake ce da mutane su biya kudin kati wanda kuskure ne. Muna aiki da abokan hadin gwiwarmu kan haka a yanzu, don magance matsalar. Abin da muka sani ba za ka biya kudi ba don a gwada jininka a abin da ya shafi gwajin kanjamau wanda muke kira CT4, da gano kwayoyin garkuwar jiki da kake da shi a jiknka ko nauyin kwayoyin anjamau. Amma wasu aibitocin suna yin haka, kuma muna duba zabin yadda za mu magance wannan batu. Wadannan kudade da ake biya haramtattu ne kuma laifi ne, kuma za mu dauki mataki sosai a kan asibitocin da suke ci gaba da karbar kudi a kan haka.