✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan zaben Kano hakkokinsu ba – KANSIEC

Hakan na zuwa ne duk kuwa da cewa an ware wa hukumar Naira biliyan biyu da miliyan 300 domin shirya zaben.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta ce yanayin matsin tattalin arzikin da kasa ta shiga ne ya sa ta gaza biyan ma’aikatanta na wucin gadi da suka yi aikin zaben Kananan Hukumomi a jihar hakkokinsu.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kusan makonni bakwai da kammala zaben, duk kuwa da cewa an ware wa hukumar Naira biliyan biyu da miliyan 300 domin shirya zaben.

Shegaban hukumar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa a cikin wani shiri mai suna Barka da Hantsi a gidan Rediyon Freedom dake Kano ranar Alhamis.

Farfesa Sheka ya ce KANSIEC ta damu matuka kan tsaikon da aka samu kan biyan ma’aikatan hakkokin nasu, inda ya ce sun fara biyan wasu daga cikinsu kuma za su kammala na ragowar ma nan ba da jimawa ba.

Da aka tambaye shi kan tabbacin da ya sha bayarwa a baya cewa Gwamnatin Jihar ta samar da isassun kudade domin gudanar da zaben sai ya musanta hakan, inda ya ce amincewa kawai gwamnatin ta yi ba wai fitar da dukkan kudaden ba.

Idan za a iya tunawa, a ranar 16 ga watan Janairun da ya gabata ne dai hukumar ta gudanar da zabukan na Kananan Hukumomi a jihar.

Jami’iyyar APC mai mulki ce dai hukumar ta ayyana a matsayin wacce ta lashe dukkan kujerun Ciyamomi 44 da na Kansiloli 484 dake jihar.

Sai dai tun wancan lokacin ne ma’aikatan wucin gadin da suka yi wa hukumar aiki yayin zaben suke ta korafin cewa ta ki biyansu hakkokinsu.

%d bloggers like this: