Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya ce karancin gas din da ake samarwa a Najeriya ne ya sa farashinsa gas din girki tashin gwauron zabo a kasar.
Shugaban NNPC, Mele Kyari, ne ya bayyana haka, yana mai cewa kamfanin na yin iya kokarinsa domin ganin farashin gas din girki ya sauka.
- Fina-Finan Hausa: Gina Al’umma Ko Ruguza Tarbiya?
- GAP: Gwamnati ta bullo da sabon shiri ga masu digiri marasa aikin yi
“A halin yanzu kasar nan ba ta da isasshen iskar gas da zai wadatar da cibiyoyinmu na iskar gas a fadin kasar; Kullum fadi-tashi muke yi don samar da gas; Ga shi duk lokacin da wani abu ya yi karanci, farashin tashi yake yi”, inji shi.
Da yake bayyana hakan a lokacin ziyarsa ga ofishin Hukumar Kula da Albarkatun Mai ta Kasa (DPR) a ranar Talata, Mele ya kuma danganta matsalar da raunin hanyoyin samar da gas din girki a kasar suka yi.
A cewarsa, hakan ya sa yanzu NNPC take aiki tare da sauran hukumomi masu alaka da ita don ganin ana samar da isasshen gas din girki saboda masu amfani da shi a gida da ’yan kasuwa su rika samun sa cikin sauki kuma a kusa da su.
“Shi ya sa muke yin hadin gwiwa domin mu rika samar da gas din girki daga abin da muke da shi a ida har ya wadata a kasuwanni; Saboda idan abu ya wadata dole farashin ya sauka,” inji shugaban na NNPC.
Mele, ya ce matakan za su fadada hanyoyin samar da gas din ta yadda za a isar da su zuwa gidaje.
Ya bayyana cewa samar da wadatacciyar iskar gas zai taimaka wajen samun ingantacciyar wutar lantarki mai dorewa, wadda kuma ta fi sauki.
“Idan hakan ta samu, amfani da tukwanen gas zai zama tarihi kamar yadda a kasashen da suka ci gaba aka daina amfani da su.
“Idan muka samar da iskar gas mai dorewa ga tashoshin lantarki a fadin kasa kuma kusa da masu amfani, gidaje za su koma yin girki da wutar lantarki don haka bukatar amfani da tukunyar gas zai ragu.
“Ana samun sauye-sauye kuma za mu ci gaba da kara yawan gas din da ake samarwa a kasuwanni don ganin farashin ya ragu,” inji Mele.
Da yake jawabi, Shugaban hukumar DPR, Injiniya Sarki Auwalu, ya ce samun wadatacciyar iskar gas zai samar da ayyukan yi tare da kawo daidaito a bangaren makamashi na Najeriya.
Ya yi aklawarin yin aiki kafada da kafada tare da NNPC domin kawo cigaba a a bangaren man.