Aminiya ta zanta da Sanata Ali Ndume, inda ya bayyana ra’ayinsa kan tura sakamakon zabe ta intanet da matslar tsaro da zamansa a kurukuku da sauransu:
A matsayinka na Sanata a Jam’iyyar APC me za ka ce a kan zaben shugabannin jam’iyya na APC da aka yi inda samu hayaniya da matsaloli a wurare da dama?
- Abin da ya jawo rikicin shugabanci a Majalisar Malaman Kano —Sheikh Ibrahim Khalil
- Jami’an tsaro sun cafke malamin ’yan bindiga a Kaduna
Ka san dimokuradiyya ta gaji haka, musamman a zamanin nan da muke ciki, mutane sun sa ido, kowa ya sa burinsa a siyasa, to dole irin wannan rigingimun su rika biyo baya.
Alhamdulillahi abin bai baci da yawa kamar yadda ake tsammani ba, wanda hakan ta wani bangaren alheri ne, don shi yake nuna abu mai kyau ake yi, don abu mara kyau ba mai fada a kai.
A wasu wuraren an zabi shugabanni biyu wasu wuraren uku zuwa hudu, ba ka ganin wadanda aka yi wa ba daidai ba za su iya raunata jam’iyyar?
To sanin gaibu sai Allah, ni dai a jiharmu, Jihar Borno mun je mun yi mun gama, kuma ba wai kowa ya ji dadin abin da aka yi ba ne, mutane sun yi imanin cewa kananan korafe-korafe an gyara.
Kuma mu a Borno gaba dayanmu mun yarda kuma muna da dalili a kan cewa wadanda ke rike da shugabancin su ci gaba, duk da wasu wuraren wadanda ke rike da kujerun sun dade, to, amma muna ganin tunda wadanda ke rike da mukaman ba su ci moriyar mukamin ba saboda yanayi na tsaro da wuraren namu ke fuskanta ya sa muka yarda kawai su koma in da wasu wurare ’yan tsiraru aka canja.
Majalisar Dokoki na kokarin a koma zaben fitar-da-gwani ta hanyar ’yar tinke maimakon wakilai. Mene ne ra’ayinka?
Na yarda da hakan, saboda ni dan siyasa ne, jama’a ne ya kamata su yi zabi wanda zai shugabance su.
Kuma bari in gyara maka ba ’yar tinke muka ce a yi ba, a’a, yadda ake gudanar da babban zabe na kasa kowa ya zo da katin zabensa haka shi ma wannan za a yi, kowane dan jam’iyya ya zo da katinsa ya yi zabe, a kirga maimakon a zabo wadansu mutane su zo su wakilci jama’a.
Idan za a yi zabe ana tura jami’an tsaro da dama domin samar da zaman lafiya. Kana ganin idan aka yi zaben fid-dagwani haka, jami’an tsaro za su iya bayar da tsaro?
Babban zaben da ake yi na kasa ba duk kasar ake yi ba, kuma haka ake tura jami’an ko’ina? Ya kamata a komai a rika kyautata zato musamman ku ’yan jarida, duk lokacin da aka fadi abu kamata ya yi ku kyautata masa zato ba wai ku dube shi da wata manufa ba.
Idan akwai gyara a abin da aka fada sai ku gyara amma ba wai ku rika munana zato a kai ba.
Sau nawa ana zabe a kasar nan, ni nan sau biyar ana zabe na a cikin zabbubuka shida da aka yi a kasar nan.
A rana daya ake yi gaba daya, to, ka ga in har an yi hakan lafiya me zai hana yanzu?
Kamata ya yi ku mai da hankali kan a yi lafiya a gama lafiya.
’Yan jam’iyya kowa ya zo da katinsa ya yi zabe ’yan takara na tsaye a kidaya a ga wanda ya ci zabe, wakilin INEC yana nan ya ga abin da ke faruwa.
Majalisa ta ce ta yarda INEC ta fara watsa sakamakon zabe ta intanet amma wasu sassa na kasar nan ba intanet, yaya kake ganin lamarin?
Matsayina a kai bai canja ba har yanzu, na fada cewa abu ne mai kyau amma kuma lokacinsa bai yi ba kuma ina ba da misali da cewa ni ina wakiltar mutanen Kudancin Borno, to na san abin da yake faruwa a yankina, na san cewa yau idan aka ce za a yi amfani da na’ura wajen tattara sakamakon zaben a wajenmu ba zai yiwu ba, kuma dole za mu yi zabe tunda mu ma ’yan Najeriya ne.
Shi ya sa lokacin da aka yi dokar a kan dole bayan doguwar muhawara kuma INEC ta ce za ta iya, muka ce to shi ke nan; sun ce in dai ba zai yiwu ba kuma za a yi kamar yadda aka saba a baya daga nan sai a je a tattara gaba daya biyun da wanda aka yi da na’urar sai su hada su fitar da sakamakon.
A bayan nan an samu labarin mutuwar Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da takwaransa na ISWAP Al-Barnawi, kuma a baya ka nuna rashin gamsuwarka game da tubabbun ’yan Boko Haram su dawo cikin mutane da zama, mece ce matsayarka a yanzu?
Alhamdulillahi da rokon Allah da kuma abubuwan da jami’an tsaro suke yi, musamman sojojin sama da na kasa da kuma abin da yake faruwa a junansu su da kansu na rashin jituwa da kuma kiran da gwamnati take ga wannan ’yan ta’adda su aje makamansu ya sa ake samun wadannan nasarori.
Da yawa daga cikinsu suna tuba, kuma ka san akwai wadanda dama tilasta su aka yi.
Wadansu ma tun suna yara kanana aka dauke su tare da iyayensu, to, ka ga irin wadannan dole ne a tace su a ga abin da ya kamata gwamnati ta yi masu.
A matsayinka na Shugaban Kwamitin Sojin Kasa a Majalisar Dattawa, ana ganin cewa ana kashe makudan kudi a harkar tsaro. Shin kwalliya tana biya kudin sabulu?
Sosai kuwa, dama ni na dade ina fafutikar ganin an inganta harkar sojoji a kasar nan kuma har yanzu ina fada maka akwai abubuwa da yawa da ba a taba ba.
Kuma idan ka dubi halin da ake ciki yanzu a kasar nan, ba abin da ya kamata a ba wa muhimmanci kamar tsaro, saboda kai yanzu idan ba tsaron za mu yi wannan tattaunawar da kai?
Kuma ina tabbatar maka cewa matsalar tsaron nan ta wuce duk yadda ake tunani, abin sai wanda ya sani zai iya yanke hukunci, kuma har a yanzu ina mai tabbatar maka cewa zan iya sadaukar da albashina wajen ganin an tabbatar da tsaron don ba abin da ya kai zaman lafiya.
Ko yanzu ina tabbatar maka har yanzu idan ka je ka ga yanayin da sojojin suke ciki za ka tausaya musu.
Yanzu fa a kasar nan sojoji ke sayen kaki da kudinsu shi ya sa za ka ga kakin yana yawo ko’ina, a da akan ba sojojin sabon kayan duk bayan wata uku.
Mahaifina soja ne ina ganin duk yadda ake.
Saboda haka har yanzu kudin da ya kamata a ware wa sojojin ya yi kadan.
Idan za a bi tawa rabin kasafin kudin kasar nan na bana sama da Naira tiriliyan takwas duk a sa a tsaron in dai har za a samu zaman lafiya.
Kuma kai ma na san za ka yarda da hakan ai babu abin da ya fi zaman lafiya.
Matsalar tsaro kamar ta kusa ta cim-ma Abuja, me za ka ce a kan haka?
To Allah ne kadai Ya san gaibu, amma Abuja ta fi karfinsu, kuma yanzu haka ba za ka ce sojojin Najeriya ma suna tsoron wadannan ’yan ta’adda ba, saboda abin da yake faruwa yanzu shi ne sojojin ke bin su sabanin a baya da sai dai su jira su.
To shi wannan yaki ne na sunkuru sai a hankali ake gama shi.
Da a ce da wata kasa muke yakin nan da yanzu mun gama da su, wannan kuwa a cikinmu suke sai a hankali za mu iya maganinsu.
Mutanen da ake tsare da su ana tuhumar su da Boko Haram ba tare da wata shari’a ba me za ka ce a kansu?
Gaskiya ce akwai su da yawa suna tsare, amma kamar yadda na fada a baya dole ne alkalai su kara kaimi wajen shawo matsalolin, akwai matsaloli ne da yawa, amma dai yanzu Allah Yana taimakonmu tunda yanzu dukkan mutane suna ba da gudummawarsu wajen ganin an kawo karshen matsalar.
Mutane yanzu suna ba da bayanan sirri ana bi kuma ana samun nasara, kuma jami’an tsaronmu sun hada kansu wajen tabbbatar da tsaron.
A kwanakin baya ka tsaya wa Abdulrasheed Maina, tsohon Shuagaban Kwamitin Sake Fasalin Fansho domin ya samu beli, inda aka samu matsala har ta kai ga an tura ka gidan yari, a wane hali ka tsinci kanka a gidan yarin?
Alhamdu lillahi an kai ni gidan yari har sau biyu, kuma duka siyasa ta kai ni ba komai ba, ba wani dalili na sata ko kisa ko wani laifi ba.
Na farko an kai ni bisa tuhumar ni nake daukar nauyin Boko Haram, don lokacin ina fada a kan abin kuma muna sukan gwamnati a kan abin sai aka makala min cewa ni nake daukar nauyin yaran.
Haka muka yi ta shari’a har tsawon shekara shida.
Na biyu kuma akwai wani dan mazabata da ake tuhuma, wanda kotu ta ce dole sanatansa ya tsaya masa a bayar da belinsa a kotu, inda na tsaya masa shi kuma daga baya ya tsere saboda yarinta.
Wannan ya sa kotu ta kama ni amma Allah Ya rufa min asiri mako daya kawai na yi.
Ina gode wa Allah da Ya yi min irin wannan jarrabawar, don ba kowa yake samun irin wannan jarrrabawa ba.
Annabawa ma Allah Ya jarabe su duk da cewa su zababbu ne a wurinSa kamar Annabi Musa da Annabi Yusuf, da Annabi Ibrahim (AS) da sauransu.
Na je can alhamdulillahi na samu wadanda ma sun fi ni a can din kamar su tsofaffin gwamnoni Joly Nyame da Joshua Dariye, duk na same su a can.
Ai dama in dai kana dan siyasa yana da kyau a ce ka je ka ga abin da yake faruwa a can duk da ba a son zuwa.
Wane yanayi ka tsinci gidan yarin da ka je?
Gaskiya ni gidan yari daya na je kuma shi ne na Kuje.
Duk da yake dama gidan yari ba wurin jin dadi ba ne, amma akwai cinkoso a gidan, yawan mutanen da suke gidan ya fi karfin gidan yarin.
Ban san yanzu ba, amma a wancan lokaci akwai cinkoso, kuma yanayin abincin da ake ci akwai bukatar a dan kara inganta shi, tun da gidan yari ba gidan horo ba ne gidan gyaran hali ne.
Kuma gaskiya abu daya da nake son yin kira a kai shi ne da dama wadanda suke cikin gidan yari ba a riga an yanke musu hukunci ba, sun fi wadanda aka yanke wa hukunci yawa.
Ya kamata alkalai su rika kokari wajen ganin sun yanke hukunci saboda kin yanke hukuncin da wuri kamar tauye musu hakki ne.