✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ayaba take arha a Abuja

Ayaba tana daya daga cikin kayan marmarin da ta fi kowane arha a Babban Birnin Tarayya Abuja. Aminiya ta yi rahoton musamman kan dalilin hakan.…

Ayaba tana daya daga cikin kayan marmarin da ta fi kowane arha a Babban Birnin Tarayya Abuja. Aminiya ta yi rahoton musamman kan dalilin hakan.

Wani abu da yake ba jama’a mazauna Abuja da dama mamaki shi ne yadda ayaba take da arha kuma kusan kowane lokaci ana samunta wato lokacin damina da rani da sauransu.
Galibin masu wannan kasuwanci na saye da sayar  ayaba da ke Abuja sun ce dalilin da ya sa ayaba take da arha a birnin shi ne ana da fadamu da ke noman ayaba da yawa a kyauyukan da ke gefen birnin da jihohin Kaduna da Nasarawa da Kogi da Binuwai.
Hakan ya sa masu sari suke bulaguro har gonakin don yin sarin ayaba su zo da su Abuja su sayar wa ’yan sari wadanda ke nikawa na ’yan kwanaki har ya nuna sannan su sayar wa masu talla don neman riba da biyan bukatun yau da kullum.
Wannan harka ta tallar ayaba ya sa tun da hantsi ake tallarta har zuwa dare a kullun a kasuwannin da gefen tituna har ma a unguwar ihunka-banza na masu hannu da shuni da ake ce wa Maitama a Abuja, inda aka kebe wuri don sayar da kayan marmari wato Maitama Fruit Market.
 Yawan ayaban ya sa farashinta ke kasa a duk tsawon shekara a Abuja, domin ta ko ina za ka ga ana tallar ayaba.
Wata mai kasuwancin ayaba mai suna Agnes Ojeh wacce aka fi sani da suna ‘Madam Banana’ ta ce ta jima tana wannan sana’a kuma tana sayowa ne ta nika sannan ta sayar. Ta kara da cewa sayo ta da yawa ya fi, domin rage tsadar kudin mota, kuma ba zai yiwu kullum mutum ya yi ta zarya don zuwa sayen “kaya gutsul-gutsul ba.”
Sai dai Madam Agnes ta kara da cewa su masu wannan kasuwanci suna da kalubale guda uku da suke ci musu tuwo a kwarya. Na farko shi ne kasuwar kayan marmarin tana cabewa matuka da tabo lokacin damina domin ba a zamanantar da ita ba.  Na biyu shi ne yadda hukumar tsaftace garin Abuja wato ‘AEPB’ da ke kama su da kayansu da laifin yin talla, don ba a yin talla a Abuja. Inda ta ce mutum nawa keda kukin kama shago? Kuma ta ce da yin rigima ko sata ai gara mutum ya nemi na kansa duk kankantar ribar. Na uku kuma shi ne “yadda masu hali masu kudi ba sa jin tausayinmu don idan sun zo sayan ayaba sai su yi ta ciniki da neman ragi kamar talakawa.”
Daga nan ta ce yakamata a ringa tausaya musu “a rage dogon ciniki tsakanin talakawa masu tallar ayaba da masu hannu da shuni.”