✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa almajiran makarantun allo ba su yawon bara a yankin Yarbawa

Al’ummar Hausawan da ke manyan garuruwan sashen Kudu maso Yamma wato yankin Yarbawa ma ba su manta da dadaddiyar al’adar nan ta koyar da ’ya’yansu…

Al’ummar Hausawan da ke manyan garuruwan sashen Kudu maso Yamma wato yankin Yarbawa ma ba su manta da dadaddiyar al’adar nan ta koyar da ’ya’yansu karatun Alkur’ani a makarantun allo ba, inda har yanzu akwai makarantun allon. Sai dai sabanin Arewa almajiran wadannan makarantu ba su yawon bara, saboda kowane yaro yana kwana ne a gidan iyayensa yana zuwa makarantar safe da yamma. Sai dai babban abin takaici shi ne akasarin masu yawon bara a yankin manya ne maza da mata wadanda wadansusu babu ko nakasa a jikinsu.

Lokacin da wakilin Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ghali Dikko yake yi wa Aminiya bayani kan yadda suke tafiyar da makarantun allo da ake kira da tsangaya ya ce, “Fiye da shekara 100 ke nan da al’ummar Hausawa suka fara bude makarantun allo domin koyar da ’ya’yansu karatun Alkur’ani a yankin Kudu maso Yamma. Bayanan da muka samu daga magabata sun nuna cewa irin karatun da ake yi a wancan lokaci a wannan sashe ya sha bamban da irin wanda ake yi a Arewa domin kananan yaran da ake koyarwa suna tare ne da iyayensu a cikin unguwannin da suke zaune ba daga wajen gari ake aikowa da su kamar yadda ake yi a Arewa ba. A yanzu Makarantun Islamiyya sun maye gurbin makarantun allo amma har yanzu akwai sauran makarantun allon.”

Ya ce idan ka ga yara sun fita yawon bara a sashin kudu to sha’awar koyon al’ada ce ta sanya su suka fita a kashin kansu a wancan lokaci da suke fita na ranakun Alhamis da Juma’a kawai.

Malam Usman Ashiru mahaddacin Alkur’ani ne kuma Na’ibin Babban Masallacin Sabo Ibadan wanda ya yi gadon koyar da yara karatun allo a Makarantar Malam Bukar Machina ya ce, “Akwai yara maza da mata fiye da 500 da muke koya musu karatun Alkur’ani da ilimin addinin Musulunci a wannan makaranta. Sai dai yaran ba sa yin bara domin suna zaune ne tare da iyayensu a cikin gidajeNsu. Yaran ba sa kwana a cikin makaranta kuma ba sa biyan ko kwabo a matsayin kudin makaranta amma iyaye suna taimaka mana da kudi kalilan domin jin dadin irin karantarwar da muke yi wa ’ya’yansu. Don haka zan goyi bayan gwamnati idan za ta sanya irin wadannan makarantu cikin makarantun tsangaya irin na

Arewacin kasa,” inji shi.

Kan matsalar mabarata, Ghali Dikko ya ce, “A wani lokaci Gwamnatin Jihar Oyo ta taba kiran mu Shugabannin Hausawa da ke zaune a Ibadan ta nemi shawararmu kan yunkurin kama mabarata domin komawa da su garuruwansu na asali a Arewa. Duk da yake ba mu goyi bayan kama nakasassu kamar makafi da guragu da kutare ba, amma mun goyi bayan kama mabarata maza da mata da babu nakasa a jikinsu da suke bata mana suna a idon duniya. Mahukunta sun sha kama su suna kullewa da komawa da su garuruwansu amma sai su sake dawowa.”

A Jihar Ogun, Sarkin Hausawan Shagamu Alhaji Inuwa Garba Sarki ya shaida wa Aminiya cewa “Muna da makarantun allo a nan Shagamu amma babu makarantar tsangaya irin ta Arewa, kuma almajiran makarantun ba sa yawon bara. Iyaye ne suke tura ’ya’yansu zuwa makarantun sau biyu a rana wato safe da yamma. Kuma har yanzu ana amfani da allo ne wajen koyar da yara karatun Alkur’ani a wadannan makarantu da suka shafe fiye da shekara 80 da budewa a Unguwar Sabo Shagamu.”

Dangane da matsalar mabarata kuwa sai Alhaji Inuwa Garba Sarki ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa da aka fi samun mutanen da suke dauko kananan yara suna yawon bara tare da su kan su hanzarta daukar tsauraran matakan hana su fitowa zuwa wannan sashe. Ya ce “Irin wadannan yara da suke tashi ba tare da kyakkyawar tarbiyya ta addini ba, sai koyon hulda da kudi a kuruciyarsu barazana ne ga harkokin tsaron kasa a nan gaba.”

Shi ma Sarkin Hausawan Ile Ife a Jihar Osun, Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali ya shaida wa Aminiya cewa: “Tun kafuwar wannan gari shekara fiye da 100 aka bude irin makarantun allo da ake dauko mahaddata daga Arewa domin koyar da yara karatun Alkur’ani. Ya ce yanzu haka akwai irin wadannan yara da aka koyar a wancan lokaci da suka zama shaihunan malaman da suka yi fice a fannin ilimin addinin Musulunci a ciki da wajen Najeriya. Kuma wadannan makarantu suna nan har yanzu suna koyar da yara karatun Alkur’ani. Amma yaran ba sa yawon bara. Game da manyan mutane maza da mata masu yawon bara ba tare da wata nakasa ba, muna rokon Allah Ya sama mana hanyar maganin wannan al’amari saboda ya zama ruwan dare da ya fi karfinmu.”

Aminiya ta ziyarci wasu masallatai da tashoshin mota da kasuwanni inda wadannan mabarata da babu nakasa a jikinsu suke kai-kawo a kullum a garin Ibadan. Yunkurin zantawa da su a kan halin da suke ciki ya ci tura inda suka rufe fuskokinsu domin kada a dauki hotonsu. Wadansu daga cikinsu ma sun yi ta fadin kalaman batunci ne ga wakilinmu.

Wani mai suna Kabiru mai lalurar shanyewar kafa daya ya ce “Ban yi karatun boko ba, amma na yi karatun Muhammadiya kadan. A can garinmu ba a yin komai da ni kuma ba na aikin komai sai wani abokina ya taho da ni nan Ibadan inda nake fita yawon bara a kullum ina samun dan abin da zan ci. Ina yin wata biyu a kowane lokaci na fito yawon bara daga garinmu kuma a ina tara kudi daga Naira dubu 20 zuwa 25 a wannan lokaci. Idan har na samu abin da zan yi a garinmu babu abin da zai kawo ni nan.”

Wata mai suna Malka mai kimanin shekara 60 ta ce, “Wadansu ’yan uwana mata da muke zaune tare a garinmu ne suka je ci-rani daga garinmu zuwa nan Ibadan da suka koma ne na gansu dauke da suturu da kudi a hannunsu. Shi ne ya sa ni ma na biyo su muka zo tare domin in samu nawa rabon saboda babu abin da nake yi a gida.”

Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa mutanen da suke yawon bara da babu wata nakasa a jikinsu akwai tsofaffi maza da mata da matan aure goye da ’ya’yansu da ’yan mata da kananan yara wadanda suke fita da sanyin safiyar kowace rana suna komawa harabobin masallatai da gidaje a cikin unguwannin ’yan uwansu Hausawa inda suke rakubewa suna kwana. Akwai da yawa daga cikin mata mabarata da suke dauko kananan yara daga garuruwansu suna yawon bara tare da su a wannan sashe. Sukan tura yaran da suke yawon bara suna samun kudi da kayan abinci da sutura da suke kai wa iyayen gijin nasu. Kuma akwai wadansu mutane da suke amfani da wannan dama wajen yin lalata da irin wadannan ’yan mata da ba su yi aure ba da ake samun shigar ciki suna haihuwa a wasu lokuta.

A bara, Ma’aikatar Tsabtace Muhalli ta Jihar Oyo ta bayar da sanarwar kama sama da mutum 50 da suka hada da mabarata Hausawa maza da mata da masu tabin hankali da aka yi bincike don gano wuraren da suka fito aka koma da su garuruwa da gidajensu.

Kwamishina Ma’aikatar Mista Isaac Ishola ya ce, wannan aiki ne da aka fara shekara 4 da suka gabata kuma za a ci gaba da aiwatarwa domin tsabtace muhalli a manyan garuruwan jihar. Sai dai har yanzu irin wadannan mabarata suna can suna kai-kawo a manyan kasuwanni da masallatai da tashoshin mota inda ake raba musu ’yan kudade da suturu da kayan abinci.