✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa ake mana kagen zame kafar Buhari – Sanata Ali Wakili

Sanata Ali Wakili shi ne yake wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu daga Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC, bayan ya kada tsohon Gwamnan Jihar Malam…

Sanata Ali Wakili shi ne yake wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu daga Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC, bayan ya kada tsohon Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana irin ayyukan da Majalisar Dattawa ta gudanar a cikin kwana 100 duk da dambarwar shugabanci da ta yi fama da ita. Kuma ya musanta zargin da ake yi cewa yana cikin sanatocin APC masu zame kafar Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafa, inda ya ce hakan yarfe ne na siyasa kawai:

Aminiya: Yallabai, nan da ’yan kwanaki majalisa za ta cika kwana 100 da kaddamar da ita. Yaya za ka bayyana yadda kuka tafiyar da harkokinku a dan wannan lokaci?
Sanata Wakili:  Alhamdulillah, ba yabo ba fallasa, tun ranar da aka kaddamar da majalisar nan ranar 9 ga Yuni, majalisar nan ta yi iyakar kokarinta wajen ganin ta bayar da gudunmawarta ta wajen kyautata rayuwar al’umma a bangaren tattalin arziki ko tabarbarewar tsaro ko kan lalacewar kayan inganta rayuwa, kamar hanyoyi da sauransu ko yaki da cin hanci da rashawa, wadanda su ne suka kawo koma-baya ga wannan kasa. Duk da dai ana rade-radin cewa ana cece-kuce ko ana zaman dar-dar a majalisar, wannan bai hana majalisar nan zama don tunanin mene ne wannan kasa tamu take ciki ba. Idan ka duba a cikin zama da aka yi an yi magana a kan wannan ukuba ta Boko Haram. Mun tattauna ta, kuma bisa wannan ne Majalisar Dattawa ta aika da tawaga karkashin shugabanta da mataimakinsa suka tafi Maiduguri da Yola don su yi jaje ga gwamnatoci da al’ummar wadannan jihohi, kuma su gane wa idonsu irin yadda abubuwa suka tabarbare suka lalace, su ga mutanen da lamarin ya shafa, ta yadda idan banagren zartarwa ya kawo wasu batutuwa ko dokoki kan yadda za a kyautata rayuwar wadancan jama’a za a samu muhawara a yanke hukunci a kai ba tare da an samu wata tangarda ba. Idan aka duba a lokacin da muke kamfe a Jam’iyyar APC mun ce harkar tsaro ita za mu bai wa muhimmanci, kuma in aka duba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo sauyi na shugabannin rundunar mayakan kasar nan, kuma doka ta ce idan ya nada su sai majalisa ta tantance ta amince kafin a tabbatar musu. Kuma cikin karamin lokaci da aka aiko da sunayensu an zauna an tantance an amince. An yi maganar tabarbarewar tattalin arziki idan darajar kudinmu ta fadi, idan aka kwatanta da Dalar Amurka wadda da ita ake cinikayya a kasashen duniya, za a ga tamu ta fadi warwas. To an yi muhawara an fito da shawarwari aka aika wa bangaren zartarwa, kuma gwamnati ta dauki matakai, musamman Babban Bankin Najeriya da huruminsa ne ya tabbatar an daidaita batun kudin. Kuma mun yi magana a kan yaya aka yi tallafi ko rangwamen da ake kira da Ingilishi waibers da ake yi don a taimaka wa kasa, amma namu sai ya kawo koma-baya, masana’antunmu suka mutu, ana ganin ma’aikata na tagayyara da sauransu, sai muka gano ba a amfani da shi ta hanyar da ta dace. Ana taimakon mutane ne wadanda ba sa taimaka wa kasa, muka ga bai dace muka fitar da kudiri muka bukaci Hukumar Kwastam da bankuna da sauran hukumomin da abin ya shafa su bi kan wadannan mutane su tattaro dukiyar nan da aka yi musu rangwame ba su yi amfani da ita ta hanyar da ta dace ba. Wannan kudin ya kai kamar biliyan 32, in aka duba zai taimaka gaya wajen kyautata rayuwar al’umma. Kuma mun yi magana a kan hanyoyi, in aka duba kusan duk hanyoyi a Najeriya sun lalace ko ta ina, ba a san ta inda za a kama ba. An kafa kwamiti wanda zai dubi wannan al’amari a san yadda za a bullo masa a karkashin Injiniya Sanata Gemade. Kuma uwa-uba saboda wutar lantarki, wutar lantakri ita ce kashin bayan cin gaban kowace kasa, in akwai ta ne masana’antu za su tsaya da kafafunsu, to in ka duba a Najeriya har muka hau wannan mulki na APC ba mu wuce megawatt 4,500, yanzu sanadiyyar wannan mulki na Buhari ne aka ce an kai megawatt 5800. Abin takaici Haramin Makka kadai an kebe masa megawatt 4800, wanda kusan a da shi ne karfin wutar Najeriya. kasar da muke tafiyar kunnen-doki wato Afirka ta Kudu tana da wuta mai karfin megawatt dubu 35 zuwa dubu 40, to mun duba wannan batu. Kuma mun duba cewa da aka sayar da wutar lantarkinmu me ya sa maimakon ya gyaru sai ya tabarbare? Sai ya zamo mutum yana zaune masu harkar wutar nan sun kawo masa takardar biyan kudin wutar lantarki da bai sha ba, bai ma ganta ba. To mun tattauna a majalisa har muka nemi Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa (NERC) ta dauki mataki, inda ta da sanarwar cewa kamfanonin da aka ba su hurumin sayar da wutar suna zaluntar ’yan Najeriya ba za a amince ba. Kuma mita a kyauta ya kamata a ba da ita, kuma kudin da ake cirewa da sunan kamasho bai dace ba. To majalisa ta yi kokari gaya. Kuma muna magana a kan wannan yaki da cin hanci da rashawa, duk da cewa ana ganin kamar akwai kutunguila ana ganin matar shugaban wannan majalisa ana tuhumarta kamar ana kumbiya-kumbiya. Amma ina so in tabbatar maka cewa dukkanmu mun daura aniyar mu ba Shugaban kasa Buhari goyon baya kan wannan yaki da cin hanci da rashawa.
Aminiya: Galibi mutane suna ganin kamar majalisar ma ba ta kafu ba, kullum kuna rikici. Kuma bayan rikicinku na cikin-gida akwai rikici tsakaninku da bangaren zartarwa, wasu na yi muku kallon kamar masu zame wa Shugaban kasa kafa, me za ka ce a kan wannan?
Sanata Wakili: Ah, wannan yarfe ne na siyasa wanda ba ka isa ka hana shi ba. In ka duba bangaren zartarwa da bangaren shari’a da bangaren majalisa, mun ta’allaka ne a kan kundin tsarin mulki na kasa. In da ake ganin kamar an sha bamban a kan zaben shugabannin majalisa ne. Shugaban kasa Muhammadu Buhari kowa ya san shi mutum ne kaifi daya, mutum ne mai fadar magana daya. Kuma kafin a zo zaben nan ya riga ya fadi cewa kamar yadda tsarin mulki ya shirya hurumin ’yan Majalisar Dattawa da na Wakilai ne su zabi shugabanninsu, kuma a kan haka ya zauna da aka zabi Sanata Bukola Saraki ya taya shi murna. Ba wata matsala a tsakanin bangaren Shugaban kasa da mu sanatoci musamman. Na  sha fadi cewa wasu mutane ne daga waje suke aikewa da yarfen siyasa. Idan ka duba wadanda ake cewa ana sa-in-sa da su kullum suna majalisa, kullum za ka ga Kabiru Marafa ya shiga majalisa ko Ahmad Lawan ko Gemade, za ka ga suna da ’yancinsu su fadi abin da za su fada, mai yiwuwa sauran su amince ko su ki in suna da sabanin ra’ayi. korafin nan da ake gani wata jarida ce ta yi kutunguila ta yi sharri, kuma mun riga mun yi taro da ’yan jarida mun nuna bacin ranmu mun kafa kwamiti saboda sun tauye mana ’yancinmu da suka yi mana wannan kazafi saboda son su hada mu da al’umma saboda sun san mutane sun dauki Shugaba Buhari tamkar Mahdi ne da zai kai mu mafita. Kuma ana ganin duk wanda ya saba masa ya saba wa al’umma ne. Don haka yaya za a yi su lalata sunan mutum, shi ne sai su yi masa yarfe. Ba wata jarida ba ce The Nation ce, ta buga wannan abu, kowa ya san mai wannan jarida, kowa ya san burinsa da inda ya nufa. Kowa ya san matsalolin da yake da su shi da wasu shugabannin majalisa, saboda haka ya kawo yakin yake yaba mana don ta haka mai yiwuwa ya karya karfin shugaban majalisar. Amma ni ina son in tabbatar babu matsala a tsakanin bangaren mulki (Shugaban kasa) da mu majalisa, saboda kullum Shugaban kasa Buhari yana aiko da wasika da sunan Bukola Saraki a matsayinsa na shugabanta, shi da kansa yake hannu a kan takardar. Na yi maka maganar yadda muka tantance shugabannin askarawan Najeriya, haka bashin da gwamnatin Jihar Edo take nema da kansa ya sanya hannu ya aiko mana. Don haka in akwai takaddama zai rubuta wadannan ne, wannan yarfe ne na siyasa, mutane da gaggawa da ma Allah Ya fada mutane sun fara tunanin zaben shekarar 2019, alhali ba wanda ya san yau balle gobe balle 2016 ko 2019.
Aminiya: Yaya maganar cewa kun saba wa jam’iyya ta ce a zabi Lawan kuka ki, ta zo ta ce a raba sauran mukamai da bangarensa kuka ki, ba ka ganin shi ne har yanzu yake bin ku?
Sanata Wakili: Wannan magana da ake zagayawa da ita sharri ne na dan Adam, babu wani mahaluki da zai kawo wata shaida cewa ni Ali Wakili Shugaba Buhari ya gayyace ni taro ban je ba. Babu wanda zai kawo shaida cewa an yi zama da Shugaba Buhari ya ce ga bukatarsa ni Ali Wakili ban bi ba. Kamar yadda na gaya maka wanna yarfe ne da kutunguila na siyasa yadda za a baci mutane. Kuma abin da nake so a gane masu amfani da wannan suna daukar alhakin mutane ne da sunan Shugaba Buhari ne. Shugaba Buhari bai yi magana da kowa ba, bai fadi magana akan kowa ba, wasunmu da ake cewa muna yi wa Shugaba Buhari zangon kasa, kwana uku ba zai yi ba, sai sun je sun yi magana da Buhari sun zauna kan yadda za a ceto kasar nan, in dai muna yi masa zagon kasa ai ba zai amince ba. Ban san mene ne zagon kasa da ake cewa ana yi masa ba, har yanzu ba a taba kawo kudirin Shugaban kasa ba, ko wata doka da yake so a zauna a kai balle a zauna a ce an yi fatali da shi ba. Bai kawo gyaran kasafi ba don ya dace da tafiyarsa, balle a ce an ki, bait aba kawo wani abu majalisa ba aka yi kumbiya-kumbiya ko aka yi jinkirin amincewa da shi ba. Mutane ne kawai in bace ka, ka bace ni kana ganin za ka tsere min a wajen gudu shi ke nan.
Aminiya: Ka yarda cewa hadakar APC ya taimaka wajen samun irin wannan matsalar?
Sanata Wakili: An riga an gama batun hadaka tuntuni, ana maganar Jam’iyyar APC ne kuma mutane ne a jam’iyyar kowa yana da buri. Saboda haka in burina zai shafe ka sai ka ga za ka yi min illa ko ni zan yi maka illa.
Aminiya: A mazabarka ta Bauchi ta Kudu ana hayaniya cewa kai da Sanatan Bauchi ta Tsakiya kuna cikin masu yi wa Buhari zagon kasa, me za ka ce?
Sanata Wakili: Ka san kamar yadda na gaya maka ba za a fasa yarfe siyasa ba, har karshen rayuwa, dan Adam da ka gan shi akwai hassada. Na biyu wasu dillallan siyasa sun saba sai sun saka ga a gaba, mai yiwuwa su samu abin da suke so a wurinka. Wadanda suke wannan kai-kawo ban san yadda suka fi ni son Shugaba Buhari ba, saboda tun hada kar da aka samu gudunmawar da na bayar wasu ba su bayar ba. Wasunsu ma ana ana amfani da su ne wajen ingiza mai kantu ruwa ana yi wa Buhari zagon kasa. Allah Ya sani, sun sani ni na sani lokacin zaben fidda-gwani wasu sun karbi kudi a wurin Kwankwaso, wasu sun tafi wurin Atiku. Wannan cece-ku-ce da suke yi bai dame nib a, wadannan mutane su ne aka yi amfani da su suka baci Ali Wakili a lokacin zabe. Babu wani dan siyasa da aka zo zaben bana da aka fi tozarta shi aka ci mutuncinsa kamar Ali Wakili, amma wannan abin bai yi tasirin ba. Wadanda suke wannan abu suna amfani da sunan Buhari ne, wadanda tunda aka rantsar da Buhari ba su taba ganinsa ba, a ina suka ga Buhari har suke wadannan fade-fade? Babu abin da za mu ce musu sai Allah Ya isa kan wannan bata suna da suke yi mana.