Yanzu kimanin wata biyu rabon Aisha Buhari, Matar Shugaban Kasa da Najeriya tun bayan barinta Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Aisha Buhari ta fice daga Najeriya ne a sirrance zuwa birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) domin duba lafiyarta.
- Aisha Buhari ba ta ce komai kan Daliban Kanakara ba
- An kara lokacin rajisatar lambar waya da layin waya
- Mutumin da ya kera kofar Dakin Ka’aba ya rasu
- Sojoji ne suka ceto Daliban Kankara —Fadar Shugaban Kasa
Majiyarmu ta gano cewa Matar Shugaban Kasar ta fice ta bar Najeriya ne ba da jimawa ba bayan kammala bikin diyarta Hanan.
’Yan makonni kadan da dawowarta daga Dubai a watan Agusta tare da Hanan ne aka yi bikin daurin auren diyar tata.
Aihsa Buhari ta yi batar dabo
A karshen makon jiya ne wani hadimanta, Kabiru Dodo, ya tabbatar da cewa ba ta Najeriya.
Sai dai duk kokarinmu na jin ta bakin kakakin mai dakin Shugaban Kasar, Barista Aliyu Abdullahi, haka ba ta cimma ruwa ba.
An dauki tsawon lokaci babu duriyar Aisha Buhari, musamman a shafukan zumunta, inda ta saba tsokaci kan abubuwa da suka shafi mata, matasa, kananan yara da ma al’umma.
Bugu da kari, a tsawon watannin, hadimanta ne ke wakiltan ta a wurin rabon kayan tallafi da gidauniyarta, Aisha Buhari Foundation ke yi a sassan Najeriya.
Shin rashin tsaro ne ya sa ta bar Najeriya?
Dodo ya tabbatar da cewa Aisha ba ta Najeriya ne a lokacin rabon kayan tallafin Aisha Buhari Foundation a garin Jalingo, Jihar Taraba.
Ya karyata rahotannin da ke cewa ta fice daga Fadar Shugaban Kasa ne saboda karuwar matsalar tsaro.
“Matar Shugaban Kasa ta yi tafiya ne domin kula da lafiyarta, ba barin kasar ta yi saboda rashin tsaro ba.
“Labarin da ake yadawa ba shi da tushe.
“Ina tabbatar wa duniya cewa kullum sai mun yi magana da ita kuma a shirye take ta dawo kasar nan da zarar an kammala jinyar ta,” inji shi.
Ana iya tunawa a ranar 22 ga Agustan 2020, Aisha Buhari ta yi godiya ga daukacin ’yan Najeriya bisa addu’o’i da fatar alherin da suka yi mata a lokacin da ta je Dubai duba lafiyarta.
A 2019 ma ta taba shafe sama da wata biyu a birnin London na kasar Birtaniya, a ziyarar da ta kai bayan ta kammala aikin Umraha a kasar Saudiyya.