✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya kawo tsaiko kan nada Rashida Mai Sa’a a sarautar Jakadiyar Kannywood

Masarautar Gusau da ke Jihar Zamfara ta ce halartar zaman Majalisar Tsaro ta Jihar da Mai martaba Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello ya yi a…

Masarautar Gusau da ke Jihar Zamfara ta ce halartar zaman Majalisar Tsaro ta Jihar da Mai martaba Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello ya yi a ranar Asabar da ta gabata ne ya kawo tsaiko wajen nada jaruma Rashida Adamu (Mai Sa’a) sarautar Jakadiyar Kannywood.
A ranar Asabar da ta gabata ne ’yan fim suka yi cikar farin dango a Gusau don halartar nadin fitacciyar jarumar, inda tsaikon da aka samu na batun nadin ya haifar da cece-kuce da yada jita-jitar cewa Sarki ya ki fitowa don ya nada ta ne saboda kasancewarta ’yar fim.
An yada cewa wadansu ’yan majalisar Sarkin da ke adawa da batun nadin ne suka rika shiga suna fita har Sarkin ya amince ba za a yi nadin ba saboda wadda za a nada din ’yar fim ce.
Masarautar Gusau ta shirya nada Rashida wadda fitacciyar jaruma ce kuma Mai ba Gwamnan Jihar Kano Shawara ta Musamman kan Harkokin Mata sarautar Jakadiyar Kannywood ce, bayan jarumar ta ziyarci Sarkin a fadarsa a watan jiya, sakamakon takardar sanar da nadin da ta samu daga kungiyar shirya fim ta Arewa Film Makers Association of Najeriya (AFMAN), reshen Jihar Zamfara.
Sakataren Masarautar Alhaji Sambo A. Sambo ya tabbatar da cewa masarautarsu na sane da batun nadin sai dai batun taron Majalisar Tsaro ta Jihar da ya taso bagatatan ne, ya sanya aka dakatar da nadin, inda kuma masarautar ta gana da jarumar har aka yi mata cikakken bayani ta gamsu.
Dangane da batun cewa majalisar Sarki ce ta yanke hukunci kan rashin dacewar nadin musamman yadda ake kallon ’yan fim wadanda ba su da kamun kai, sai ya ce, “Babu yadda masarautarmu za ta yarda ta nada wani ba tare da ta yi bincike a kansa ba, mun yi bincike a kan Rashida, mun kuma gamsu da halayenta, batun taron da Mai martaba ya je ne ya kawo tsaiko wajen nadin.”
Kan sake sanya ranar da za a yi nadin sai ya ce ba abu ba ne na gaggawa ba, domin masarauta za ta sake zama da Rashida da ’yan tawagarta kan ranar da za a sanya. Batun cewa ’yan fim sun watse ba tare da sanin ina aka dosa ba sai ya ce ba kowa za a yi wa bayani ba, wadda abin ya shafa an gana da ita da amintattunta, kuma ta gamsu da dalilin da ya kawo tsaikon.
Da Aminiya ta tuntubi jarumar ta bayyana cewa ta gamsu da dalilan da masarautar Gusau ta bayyana mata game da batun da ya kawo tsaikon nadin nata. Ta ce “Masarautar Gusau ba ta dakatar da nadina ba. A da an sanya za a yi nadin a ranar 23 zuwa 24 ga watan jiya, amma na nemi alfarma saboda batun zaben cike gurbin dan Majalisar Minjibir da ya taso. Hakan ya sanya na buga wa Sakataren Majalisar Sarki waya, na nemi alfarmar cewa a mayar da nadin nawa mako daya bayan zaben Minjibir. Mai martaba ya amince aka mayar da ranar nadin ranar 5 zuwa 6 ga wannan wata. Ina Gusau tun ranar 5 ga wata, mun kuma ci gaba da shirye-shirye, sannan mun rika yin waya lokaci zuwa lokaci don a tabbatar komai ya tafi daidai, kasancewar tuni aka kira ’yan jarida da za su watsa labarin nadin.”
Ta ce ta sanar da masarautar Gusau yawan mutanen da za su halarci nadin, kuma an ware musu mazauninsu, sannan karfe takwas na safe Sakataren Majalisar ya kira ta, ya tambaye ta manyan mutanen da za su halarci nadin, ta fada masa. “An kammala duk shirye-shirye, karfe 11:00 na ranar Sakataren ya sake kirana ya ce in yi sauri in zo, domin Sarki ba ya saba lokaci, mun iso an kammala shirye-shirye, wuri a cike da mutane. Kwatsam sai aka kira Sarki a kan matsalar tsaro, kamar yadda kowa ya san matsalar da ke faruwa a Zamfara ta ’yan fashi da barayin shanu inda bayan mun isa fada ne sai aka ce in shigo wani daki tare da amintattunna biyu, ina shigowa Sarkin yana fita, domin halartar zaman majalisar tsaro ta jihar,” inji ta.
Ta ce abin da ya yi mata dadi shi ne yadda Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello ya rika kiran sakataren majalisarsa don a ba ni hakuri, sannan bayanin da Sarkin Gabas wanda na hannun daman Sarki ne ya yi mata ya kwantar mata da hankali.
Ta ce abin alfahari shi ne duk wanda ya je Gusau ya ga irin abin da masarautar ta yi mata, zai tabbatar da lallai tana da kima da daraja a wurin Sarki, kasancewar an nuna mata kauna.
Ta ce dage nadin bai daga mata hankali ba, face yanayin yadda hankalin Sarki ya tashi a lokacin da aka kira shi don halartar taron, saboda an riga an ba ta sarauta, bikin nadin ne ya rage, a yanzu da “nake magana da kai na kai kwana 34 a kan wannan sarauta.”
Sannan ta ce tawagar da ta gayyata sun gamsu da bayanin da ta yi musu, domin sun ga yadda aka shirya wuri, sun tabbatar idan babu batun nadin babu yadda masarauta za ta gayyato mutane, ta shirya wurin duk a matsayin wasa, don haka wadanda ta gayyata sun gamsu.
Ta gode wa masarautar Gusau bisa ga karamcin da ta yi mata kuma ta gode wa masoyanta bisa ga addu’ar da suke yi mata, inda ta bukaci mutane su daina yada jita-jita ba tare da sun tantance labari ba.