Daliget su ne wakilan jam’iyyun siyasa kuma mutanen da ke da hurimin zabar mutanen da za a su zama ’yan takara a karkashin inuwar jam’iyya.
Daliget din jam’iyyar PDP kashi biyu ne; zababbun daliget da kuma daliget na alfarma.
Bayan Shugaba Buhari ya ki sanya hannu a kan gyaran da aka yi wa Dokar Zabe ta 2022, jam’iyyar ta sanar da mambobinta cewa da zababbun daliget za ta yi amfani wajen zaben dan takararta na shugaban kasa.
Sakataren Tsare-tsaren PDP na Kasa, Umar Bature, ya sanar cewa Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar (NWC) ya yi ittifaki cewa zababbun daliget ne kadai za su yi zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyar a dukkan matakai.
Aminiya ta gano cewa jam’iyyar na da jimillar zababbun daliget 811, wadanda suka hada da mutum daya daga kowacce daga cikin kananan hukumomin Najeriya 774.
Akwai kuma daliget na musamman guda daya, wanda dole ya kasance nakasasshe, daga kowacce daga jihohin Najeriya 36 da kuma Abuja.
Sharuddan zababbun daliget
A bisa tsarin jam’iyyar, wajibi ne kowane zababben daliget ya kasance dan jam’iyyar, ya sayi fom din shiga takara, kuma aka zabe shi a matsayin zababbun daliget.
Su wane ne Daliget na alfarma?
Amma da Shugaba Buhari ya sanya hannu kan gyaran da Majalisar Dokoki ta Kasa ta yi wa sashe na 84 (8) na dokar zaben, to da daliget na alfarma sun samu damar jefa kuri’a a zaben fitar ta ’yan takara.
Sashe na 33(1) na kundin tsarin mulkin PDD, ya bayyana cewa daliget din alfarma daga cikin ’yan jam’iyyar sun hada da shugaban jam’iyya na kasa da tsofaffin shugaban kasa da masu ci tare da mataimakansu da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa masu ci da tsofaffin shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa da kuma gwamnoni masu ci da mataimakansu.
Sauran sun hada da ’yan takarar gwamna a jam’iyyar da mataimakansu da tsoffin mambobin kwamitin amintattu da mambobin kwamitocin gudanarwa na yanki da na jihohi da ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Kasa da kuma shugabannin kananan hukumomi masu ci da tsofaffi da tsoffin mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa.
Dukkansu dai dole su kasance mambonin jam’iyyar har yanzu.