Rikicin da balle a Gidan Yarin Bauchi ya yi sanadiyyar jikkata fursunoni biyar da jami’an kula da gidan yarin biyu.
Kakain gidan yarin, Abubakar Adamu ya bayyana cewa rikicin ya barke ne sakamakon zargin wani daga cikin jami’an da yi wa fursunoni safarar miyagun kwayoyi da sauran haramtattun abubuwa.
- Ba wanda ya koya min tukin Keke Napep —Amina “Sai Mama”
- Ganin ’yan bindiga ya fi sauki a kan ganin Buhari – Sheik Ahmad Gumi
“Rikicin ya ne barke sakamakon wani jami’in gidan yari da ke wa fursunoni fataucin wayoyin salula, kwayoyi da dangoginsu a gidan yarin.
“Dubun jami’in ta cika bayan samun bayanan sirri, ana cikin gudanar da bincike ne sai fursunonin suka samu labarin abin da ya faru.
“Sai suka kutsa kai cikin dakin ajiyan kaya suka dauko shebura da diga da wukake.
“Daga nan suka fito suna rera wakoki suna fasa kayayyaki a cikin gidan yarin, wanda hakan ya tilasta jami’an gidan yarin suka fara harbi a iska don su tsorata su.
“A garin wannan yamutsin ne fursunoni biyar da jami’ai biyu suka ji rauni,” inji Adamu.
Kakakin gidan yarin ya ce an samu an shawo kan lamarin, kuma fursunonin sun koma dakunansu.
Daga nan ya shawarci jama’a da su kwantar da hankulansu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullun saboda kwanciyar hankali ya dawo a gidan yarin.
A halin yanzu an tsaurara matakan tsaro, tare da takaita zirga-zirgar ababen hawa da na mutane a yankin, an kuma toshe hanyoyin da ke zuwa gidan yarin.