Yau shekara 27 cif da gudanar da babban zaben da ‘yan Najeriya da dama suka yi ittifaki shi ne mafi inganci a tarihin kasar.
Hakan ce ta sa bayan shekara 25 da zaben na 1993, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta ayyana ranar da aka yi zaben—12 ga watan Yuni (June 12), a matsayin Ranar Domokradiyya, maimakon 29 ga watan Mayu da aka saba bikin tun daga shekarar 2000 zuwa 2018, bayan kafuwar Jamhuriyya ta Hudu a kasar a 1999.
Ko da yake akwai masu ganin ranar 1 ga watan Oktoba da kasar ta samu ‘yanci ce ta fi cancanta ta zama Ranar Damokradiyya. Wanin bangaren kuma ya fi gamsuwa a yi bikin a 15 ga watan Janairu —ranar da aka hambarar da zababbiyar gwamnati ta farko a kasar a 1966. Wasu kuma na ganin da an bar shi a 29 ga watan Mayun da aka saba.
Kyakkyawar shaida
Ko ma mene ne, zaben 12 ga watan Yuni ya samu kyakkyawar shaida a Najeriya game da yadda ya gudana kama daga yakin neman zaben da ma zaben kansa.
Duk da cewa ba a kai ga sanar da sakamakon zaben a hukumance ba gwamnatin wancan lokaci ta tsohon Shugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke shi saboda abin da ta kira saba doka, babu shakka waiwaye da kuma amfani da darussa daga yadda aka yi wancan zabe za su saukaka shawo kan matsaloli su kuma kawo tsafta a tsarin zabe a Najeriya.
Ko da yake tsawon lokaci ana ta tsokaci tare da nuna yatsa a kan soke zaben, alkaluman da ka samu kafin soke zaben sun nuna Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola na jam’iyyar SDP na gaba da gagarumin rinjaye a kan abokin karawarsa, Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC.
Darussa daga zaben ‘June 12’
Ana tunanin zaben 1993 shi ne na farko a tarihi wanda masu addini daya (Musulmai) suka tsaya takara kuma ‘yan kasar suka zabe su ba tare da la’akari da batun addini ba.
A wancan lokacin, Marigayi Abiola ya dauki Babagana Kingibe, Musulmi daga jihar Borno a matsayin mataimakinsa, ko da yake Tofa ya dauki Kirista, Sylvester Ugoh daga Kudu.
Bashir Tofa dan Arewa ne daga Kano —amma Kanuri dan asalin jihar Borno, Abiola kuma Bayarabe ne daga kudu, amma batun kabila ko yanki bai yi tasiri ba zaben. ‘Yan Najeriya sun yi zabi cancantar da suka gamsu da ita ba tare da la’akari da banmbancin kabila ko yankunan ‘yan takara ba.
Hakan ce ma ta sa ake ganin alkaluma da aka riga aka tattara suka nuna Abiola ya samu rinjaye a kan Tofa ba a yankin Arewa ba kawai, a’a hatta a jihar da Bashir Tofan ya taso (wato Kano).
Duk da cewa an yi zaben 1993 shekaru da dama da suka wuce, kuma ba shi ne na farko a Najeriya ba, fadi tashin da aka yi da tsarin gudanar da zaben abin koyi ne ga zabuka da ma tsarin damokradiyya a Najeria.
A iya cewa babban darasin shi ne yadda aka tsara aka kuma gudanar zaben 1993 har ya samu karbuwa sosai ya kuma yi zarra a Najeriya.
Waiwaye adon tafiya
Shekaru 27 bayan zaben da aka gudanar a lokacin da babu ci gaban zamani na tabbatar da sahihancin zabe, amma har yanzu ana ganin ba a taba samun karbabben zabe kamar na ‘June 12’ din ba.
A iya cewa ma yawan korafe-korafen da kan dabaibaye zabuka a yanzu sun dama na zaben June 12 sun shanye, duk da cewa an gudanar da zabuka shida a jere, kuma a kowane karo kara zuba kudade da fasaha da gyare-gyare ake yi domin samun sahihin zabe.
Wani abin mamaki shi ne yadda a zabukan da suka biyo bayan na 1993 ake kara zargin ‘yan siyasa da yin ka’in da na’in, wani lokaci har da turawan zabe, wajen tadiye tsarin tabbatar da gaskiya kuma sai kara fito da sabbin salo suke yi. A wasu lokutan ma tun daga matakin nema tsayawa takara ake saba ka’idoji.
Kazalika bayan shekaru ana mu’amalar siyasa da sauransu tare tsakanin ‘yan yankuna da mabiya addinai a kasar ga kuma wayewar kai da zamani, akwai daure kai ganin yadda a wannan zamani ne kuma batun yanki ko kabila ko addini kan yi tasiri a tsarin siyasar.
Ranar 12 ga watan Yuni wadda yanzu yanzu ta zama Ranar Damokradiyya a Najeriya, tabbas ta kafa wani ginshikin tarihi da zai yi wuya a manta da shi a nan kusa.