Shekara ta 2022 kamar sauran shekaru ta zo wa Najeriya da abubuwa da dama wadanda za a jima ba a manta da su ba a tarihi.
Sai dai daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a shekarar, Najeriya ta yi rashin wasu fitattun mutane, kama daga ’yan siyasa zuwa ’yan kasuwa, malaman addini da ’yan boko da ma sauransu.
A yayin da muke bankwana da shekarar, Aminiya ta yi nazarin wasu daga cikin fitattun mutanen da suka rasu a Najeriya a cikin shekarar.
Bashir Othman Tofa
Attajirin dan kasuwa, marubuci kuma dan siyaya. Ya taba tsayawa takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NRC a shekarar 1993, inda ya fafata da marigayi MKO Abiola na jam’iyyar SDP.
Ya rasu yana mai shekaru 73 a Kano a ranar 3 ga watan Janairun 2022, a gidansa da ke Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.
Dokta Ahmad BUK
Dokta Ahmad Ibrahim (Bamba), wanda aka fi sani da Dokta Ahmad BUK, ko kuma Kala Haddasana, fitaccen malamin addinin Musulunci ne kuma masani a fannin Hadisi. Marigayin har ila yau malami ne a Sashen Koyar da Addinin Musuluncin a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Ya kuma yi fice ne a sakamakon karatuttukansa na Hadisi da ake sakawa a kafafen yada labarai. Ya rasu a ranar bakwai ga watan Janairu yana mai shekaru 82 a Kano bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya.
Sheikh Goni Aisami
Malamin addinin Musulunci mai kuma wa’azi. Malamin ya rasu ne sakamakon harbe shi da wani soja da ya rage wa hanya a motarsa ya yi.
Sojan, shi da abokinsa sun kashe malamin ne da niyyar guduwa da motarsa, Allah kuma ya tona musu asiri. Sheik Goni ya rasu ne a ranar 19 ga watan Agusta.
Farfesa Abdullahi Mahadi
Shi ne tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ana tuna shehun malamin ne da irin yadda ya tafiyar da jami’ar, musamman yadda ya kawata ta da shuke-shuke da itatuwa.
Ya rasu ne a ranar 16 ga watan Disamba yana da shekara 77 da haihuwa a Kaduna.
Shehu Malami
Shi ne mai rike da sarautar Sarkin Sudan na Wurno, kuma daya daga cikin manyan ’yan Majalisar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato.
Marigayin Babban attajiri ne, kuma dan kasuwa. Sannan ya taba zama Jakadan Najeriya a Kasar Afirka ta Kudu. Ya rasu ya na mai shekara 85 da haihuwa a Sakkwato, a ranar 19 ga watan Disamba bayan rashin lafiya.
Cif Earnest Shonekan
Tsohon Shugaban gwamnatin rikon kwarya da Ibrahim Babangida ya mika wa mulki a lokacin da zai sauka a shekarar 1993, kafin daga bisani Marigayi Janar Sani Abacha ya yi masa juyin mulki. Ya rasu yana da shekara 85 a jihar Ogun, a ranar 11 ga watan Janairu.
Tafa Balogun
Tsohon Babban Sifetpon ’yan sandan Najeriya, ya yi suna a sakamakon yaki da cin hanci da rashaw ne da ya ce ya na yi, a inda ya kama wasu ’yan sanda a shingen bincike a hanya ya kuma kore su, sai ga shi an same da makudan kudade da ake zargin na na rahsawa ne. Ya rasu ya na mai shekara 74 a garin Legas, a ranar 4 ga watan Agusta.
Sarkin Jama’are
Sarkin Jama’are da ke Jihar Bauchi, Ahmadu Muhammad Wabi II, ya rasu ranar biyar ga watan Fabrairun 2022.
Marigayin, wanda daya ne daga cikin manyan Sarakunan Jihar Bauchi, ya rasu ne yana da shekara 92 a fadarsa da ke garin na Jama’are.
Alhaji Hassan Ahmad Danbaba
Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Ahmad Danbaba, jika ne ga marigayi Sardaunan Sakkwato, kuma Firimiyan Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello. Ya rasu yana da shekara 50 a Sakkwato, ranar 12 ga watan Fabarairu.
Farfesa Gidado Tahir
Shi ne tsohon Shugaban Hukumar Samar da Ilimi Bai-daya ta Kasa (UBEC). Shehun ya malamin ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ilimi a matakin Firamare a Najeriya.
Farfesan ya rasu yana da shekara 72 a duniya a gidansa da ke Yola a Jihar Adamawa, ranar 13 ga watan Janairu.