✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muke yi don shawo kan matsalar tsaro a Jihar Bauchi – Kwamishinan ’Yan Sanda

Jihar Bauchi kamar sauran jihohin Arewa na fama da irin nata matsalolin tsaro, inda a kwanakin baya aka samu matsalolin ’yan kwanta-kwanta da satar shanu…

Jihar Bauchi kamar sauran jihohin Arewa na fama da irin nata matsalolin tsaro, inda a kwanakin baya aka samu matsalolin ’yan kwanta-kwanta da satar shanu da garkuwa da mutane da fashi da makami har ma da fashi da rana-tsaka inda ’yan fashi suka bi mutane suka kwace musu kudi, daya a kan Titin Makera daya a Titin Aminu Street, fashin da ya jawo kisan mutum guda. Rundunar ’Yan sandan Jihar ta sanya motocin sitiri a manyan titunan birnin. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Habu Ahmadu Sani ya yi zama da shugabannin Fulani don nemo hanyoyin zama lafiya, bayan zaman ne ya amsa tambayoyin manema labarai ciki har da wakilinmu kamar haka:

Bayan wannan tattaunawa me kake tunanin zai auku ?

Alhamdulillahi muna da shugabannin kungiyoyin Fulani biyar da suka halarci wannan taro, kuma manufar wannan taro shi ne mu tattauna kan matsalolin tsaro wadanda saninku ne a wasu jihohi da suke makwabtaka da mu da wasu da nan Arewa akwai matsalolin tsaro da suke addabar wuraren. Sai muka ga ya dace tun kafin wadannan matsaloli su zo wannan jiha, mu dakile su. Wannan dalili ne ya sa muka kira shugabannin kungiyoyin Fulani muka tattauna muka fito da hanyoyind a za su inganta tsaro a jihar kuma mu dauki matakan tabbatar da tsaro a Jihar Bauchi don taimaka wa wannan yanki da kasa baki daya.

Wasu lokuta za a ga wadansu Fulani suna  cewa kungiyoyin da suka bayyana a nan ba su ne wakilansu ba. Idan aka samu irin wannan yaya kuke yi?

Kamar yadda kuka ji lokacin da aka fara gabatarwa akwai wadanda suke cikin kungiyoyi akwai wadanda kuma shugabanni ne na Fulani, wadanda ba a cikin kungiyoyin suke ba. Suna matsayin shugabanni ne na gargajiya (sarakuna), saboda haka idan ba ka cikin wannan kungiyar kila kana cikin wata, idan ba ka ciki akwai sarakuna da ka aminta da su da suke yankunanku za su kai wannan sako. Kamar yadda na fada a jawabina kafin fara wannan taro na yi rangadin kananan hukumomin jihar, kuma na tattauna da shugabanninsu na gargajiya da na kungiyoyinsu da sauran kungiyoyin da suke cikin jihar baki daya. Kowane mun tattauna kan harkokin tsaro don ganin an inganta tsaro a jihar.

Ko akwai wata yarjejeniya da za ku sa hannu a kai ta zaman lafiya a tsakanin makiyaya da manoma ganin yawan tashin tashina da ake samu tsakaninsu?

A yanzu wannan mataki ne na farko, kuma za mu rika yin sa lokaci-lokaci. A halin yanzu muna tattaunawa ce mu ji shawarwarin da za su iya ba mu don ganin an inganta tsaro a wannan jiha. Daga nan za mu sake daukar mataki na biyu, bayan nan mu sake kiran wani taro mu ga shin abin da muka cimma a taron shin an samu aiwatar da shi ko akwai gyare- gyaren da suka kamata sannan mu sake kira mu tattauna a kai.

Akwai matsalar rashin isassun ’yan sanda a nan jihar, musamman a yankunan kananan hukumomi da kauyuka da hakan ke kawo yawan sata da garkuwa da mutane da ake samu. Wane mataki kuke dauka don ganin ans amu isassun jami’an tsaro?

Ganin ba mu da isassun ’yan sanda ya sa muka dauki matakan samun mutanen da suke cikin kungiyoyi daban-daban don hada kai da ’yan sanda wajen tabbatar da tsaro. Kamar yadda na fadi a jawabina na baya, kowane yanki mun raba shi gida-gida akwai wadanda suke taimaka mana a cikin mutanen gari ko unguwa wadanda suka sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaro a yankunan. Yanzu muna da mutum sama da 1,500 da suka sa kansu aikin tabbatar da tsaro a cikin garin Bauchi.  Akwai ire-irensu da yawa a kananan hukumomi da su suke taimaka mana idan za mu fita aiki. Kamar yadda kuka gani kwanan nan akwai hadin gwiwa da muka yi da sauran jam’ian tsaro, muka kafa jami’anmu na tsaro da suke fita aiki da mutanen wadannan yankuna ko kauyukan da suke iyaka da jihohi makwabta. Kauyuka 60 ne za su ci ribar wannan tsaro da ake samu a yankunan da muke makwabtaka da jihohi.

Matsalar ’Yan Ba Beli ita ce babbar matsalar da take faruwa a kauyuka inda mutane ke yanke hukunci kafin su kawo gare ku wane mataki kuke dauka don shawo kan wannan matsala?

Alhamdulillahi cikin matsalolin da muke ganin suna damun jama’ar jihar, bayan na dubi kundin tattara bayanai na jiha na fitar da wasu abubuwa da suke addabar jama’a kusan biyar ko shida na daya daga ciki shi ne zancen sara-suka wanda yanzu ya zama tarihi a Bauchi. Sannan akwai matsalar ’Yan Ba Beli wanda a yanzu ba a jin su kamar da. Yanzu muna daukar mataki yanzu haka akwai wadanda muka samu suna tsare sun kai mutum bakwai muna bincike kansu kan irin wadannan matakai da suka dauka, ko mun kai su kotu, kuma Allah da ikonSa mun samu saukin ire-iren wadannan abubuwa a yanzu. Sannan garkuwa da mutane ne ta sa muka rika daukar matakan tsaro, ita harkar tsaro aba ce da kullum ake dubawa a yi kwaskwarima a sake fito da wani tsari. Yadda barna ke canjawa haka mu ma muke kokari mu yi canji don mu sha gaban masu aikata laifuffuka.

Galibin ’yan sanda sun tare a jikin manyan jami’an gwamnati ba za ku rage yawansu a jikin manyan ku tura su kananan hukumomi ko karkara domin tabbatar da tsaro ba?

Muna da abin da ake kira SPU wato sashe na musamman aikinsu ne wanda duk ya cancanta a ba shi tsaro, kuma akwai tsare- tsaren Gwamnatin Tarayya da sunan duk wanda ya cancanta a ba shi tsaro. Suna cikin wani kundi, saboda haka duk wanda bai kamata ba zai zama cewa an ba shi ba sai yana kan tsari sannan ake turashi nan.