✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muka tattauna a kan Ijtihadi da kiyas a Turkiyya – Sheikh Nasidi

Sheikh Nasidi Abubakar Muhammad, babban malami ne da ke zaune a Gwauron Dutse cikin birnin Kano, kuma yana daga cikin wakilan Najeriya da suka halarci…

Sheikh Nasidi Abubakar MuhammadSheikh Nasidi Abubakar Muhammad, babban malami ne da ke zaune a Gwauron Dutse cikin birnin Kano, kuma yana daga cikin wakilan Najeriya da suka halarci taron Musulunci a kan Ijtihadi da kiyasi da kungiyar Hizmet Mobement ta Sheikh Fethullah Gullen ta shirya a ranakun 9 da 10 na Mayu 2014, a Istanbul da ke kasar Turkiyya. Ya shaida wa Aminiya abubuwan da suka tattauna a wurin taron:

Nasir Imam, wanda ya dawo daga Istanbul
 
To ga shi an zo Istanbul domin yin muhawara a kan Ijtihad da kiyasi ko za ka iya mana bayani a kansu?
To wannan taro da wannan kungiya ta Hizmet ta shirya dama tana yin sa kowace shekara, kuma tana gayyatar mutane daga ko’ina a duniya, kamar shi wannan taron sama da kasa 95 aka gayyato, kuma an gayyato malamai da daliban ilimi.
Wato Ijtihadi da kiyasi wasu rukunai ne na addinin Musulunci da shari’a take dogara da su wajen yanke hukunci kan al’amuran da suke tasowa. Abu na farko da ake dogaro da shi, shi ne Alkur’ani, na biyu Sunnah, na uku Ijma’i, abu na hudu shi ne Ijtihad da kiyasi, su biyu kusan abu daya ne. Wato ma’anar Ijtihadi da kiyasi ita ce akwai wasu abubuwa da ba su auku a baya ba ballantana a samu hukuncinsu a nassin kur’ani da Sunnah, a lokutanmu na yanzu ne suke aukuwa, kuma ana bukatar lallai a san mene ne hukuncinsu a addinin Musulunci saboda Allah ya tabbatar.
To, idan bai bayyana a cikin kuráni ko Sunnah ba, akwai mutanen da suka koshi da sanin kur’ani da Sunnah sun tabbata a kan dukkan wani fanni na ilimi irin wannan abin da ya faru sabo, sai su duba su ga akwai abin da ya faru kamarsa a baya wanda za su iya riskar da wannan da wancan domin ya zama hukunci. Idan kuma babu sai su yi kokari su ga lallai sun ajiye wani hukuncin da suka ga ya dace da shi a wannan lokaci.
Misali kamar abin da ya shafi dashen zuciya, wanda ba a baya ba, ana so asan halinsa yanzu sai a duba kiyasi da Ijtihadi a ga wannan abu akwai wata kafa da addini ya yarda a yi amfani da ita? Misali a dauki jinin wani a sa wa wani, wannan jini za a iya saida shi ko sai kyauta? To wasu malamai suna ganin ya halatta, wasu ko sun ce a’a. To duk wadannan su ne Ijtihad da kiyasi suke hawa a kansu, wato rai amana ce ta Allah wa ya halatta maka wannan domin ko kai kanka ba a so ka cuci kanka ba.
Wane ne zai zartar da wannan hukunci, malamai ko alkalai?
Malamai ne ya kamata su duba su ga zai iya yiwuwa a addinance, saboda haka malamai ne sai su duba su gani. Allah Ya ce kada ku tura kanku cikin halaka. Wanda zai ba da jininsa sannan shi ya zama cikin halaka haramun ne.
To bayan da aka kammala wannan taro wace gamsuwa ka samu daga halartarsa?
Gaskiya a wannan taro malamai sun tattauna sosai wadda ta ba da fa’idoji kuma yana daga cikin fa’idojin da wannan taro ya bayar musamman a kan wannan abu guda biyu kiyasi da Ijtihadi. An rufe kofarsa tun a baya ba wani mujtahidi da zai iya bayani a kansa yanzu sai dai malamai na baya wadanda da iliminsu ne za a iya haskakawa a samu mafita.
Malamai sun yi muhawara a kan wadannan, wasu suna ganin a’a yanzu ma za a iya yin Ijtihadi a kan wasu ababe, saboda haka akwai fa’idoji da dama. Akwai tambaya iri nawa ne kiyasin kuma yaya za a yi shi? Kuma an tabo abubuwa wadanda ba kawai Ijtihadi da kiyasi ba, misali a kan hada kan Musulmi gaba daya a duniyar nan, su jefar da son kai, su zama yadda Allah Yake so Ya gan su wato tsintsiya madaurinki daya.
Wanda suka shirya wannan taro muhimmiyar manufarsu ke nan.
 Idan akwai bambannce-bambance, musamman a kasarmu Najeriya wane kira za ka yi ga malamai da al’ummar Musulmi kan yadda za su amfana daga wannan taro?
 Gaskiya ne, musamman kirana ga malamai ne, don jahili sai abin da aka dora masa, amma malamai ya kamata su duba domin suke da magoya baya. Malamai suna gaya wa mutane ku rike kanku da igiyar Allah kada ku rarraba, to wadannan malamai suna fassara wa mutane amma kamar su ba sa fassara wa kansu wannan aya. A lokacin Annabi (SAW) babu wani sabani sai bayan da ya rasu, a lokacin shi ma sabani ya yi karanci domin suna kusa da zamaninsa, amma wannan sabanin fahimta ba ta sa su kin junansu.
Abdullahi dan Abbas, a zamanin Usman na Khalifa aka samu Usman bai hada Sallah ba a filin Arfa bayan hadawa ake yi, sai Abdullahi dan Abbas ya yi shiru bayan an gama sai sahabbai suka ce yaya ka yi shiru a kan wannan? Sai ya ce baya so a kawo abin da zai raba kan Musulmi ne, to ka gani. Amma mu yanzu dan kankanen abu da bai kai ya kawo ba, sai a nemi raba kan Musulmi, wannan ba shi zai kai mu ga ci gaba ba. kalubalen da ke gabanmu shi ne sauran duniya suna kallonmu a kan Musulmi ne koma wace kungiya kake, wannan wa’azi ne a fayyace, ganin so ake a rusa mu, wannan wa’azi ne Allah Yake nuna mana a fili, fatarmu Allah Ya sa mu kara hada kai.
Su magoya bayan malaman fa wane kira za ka yi musu?
Musulmi su duba su gani ko malaminka ne yake neman raba kan jama’a ka rabu da shi domin ba a ce ka bi duk abin da ya ce ba, sai dai abin da ka ga shi ne daidai. Kada ka bari wani malami ya sa maka kiyayyar dan uwanka Musulmi. Allah Ya ce kowa za a yi masa hisabi ne daidai gwargwadon aikinsa, saboda haka ka tsaya ka yi ibadar da ta wajaba a kanka. Su kuma malamai in ka cancanta ka yi wa’azi ka yi wa’azin da ya kamata.
Wata rana Abdullahi bin Zubair ya shiga wurin Amiril Muminina a wancan lokacin Umar bin Abdul’aziz ne, sai ya samu ya jinkirta Sallar La’asar bai yi ta a kan lokaci ba, sai ya tambaye shi cewa ka san Jibrilu ya sauka ya nuna lokutan Sallah, amma yanzu ka jinkirta bayan ka sani, me ya sa?
Ka ga nan ya kawo masa misali ne bai ce ya yi bidi’a ba ko haramun, to wannan ka ga fadakarwa ce. Haka nan Annabi (SAW) an taba kawo masa karar wani ya aikata wani laifi, sai ya hau mumbari yana jan kunnen Musulmi bai ambaci sunan ko wane ne ba.
Shi wa’azi fa dutse ne kada ka sake shi a kan mutane sai ya rotse su, Saboda haka wa’azi da lallami ake yin sa, saboda abin da kai mai wa’azi kake ganin suna yi na laifin su, suna jin dadin yinsa. Zuciyarsu ta amince masu da su yi haka kuma kai kana so ka raba su da shi, to yaya za a yi ka zo da tsawa da fada? Sai dai ka lallaba ka kwace wannan abu, sannan ka musanya masa da abin da bai saba da shi ba.