Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yanki tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karskashin inuwar jam’iyyar NNPP.
Bayan sayen fom din a kan Naira miliyan 30 a ranar Talata, tsohon ministan tsaron, ya bukaci ’yan Najeriya musamman ’yan siyasa da ke son kawo sauyi da zuciya daya a kasar da su shiga jam’iyyar NNPP, domin karbe ragamar mulki a 2023.
- Hotunan matsahin hafsan sojin da ya rasu a hatsarin jirgin Kaduna
- Tashin bam a mashaya ya hallaka mutum 7 a Taraba
“Wannan jam’iyya ce ta neman kawo cigaba da kyakkyawan sauyi a siyarar kasar nan.
“Yanzu duk gundunar da ka je za ka samu babu wata jam’iyya da mutane ke maganar a kanta kamar NNPP.
“Saboda haka ya kamata duk masu neman kawo ci gaba mai ma’ana a kasar nan su shigo cikinta.
“Kasar nan ba ta taba samun rabuwar kai irin wannan lokaci ba, mu kuma mutane ne masu son a samu hadin kan kasa ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, tunda kasar tamu ci baki daya,” inji Kwankwanso.
Ya kara da cewa, “Ina kira ga kowane dan Najeriya da ya je ya yi rajista ya zama dan jam’iyyar NNPP.
“Kowa ya yi kokari ya je ya yi rajista a mazabarsa, saboda muna buga katin rajista sai karewa suke ta yi.
“Masu son yin takara a matakin kasa, ku zo nan hedikwatar jam’iyyar NNPP ku sayi fom dinku; na matakin jiha kuma za ku samu takardun a ofisoshin jam’iyya a jihohinku.”
Kawo yanzu dai Kwankwaso shi ne kadai wanda ya sayi fom din takarar shugaban kasa a sabuwar jam’iyyar ta NNPP.
Hakan na zuwa ne kasa da wata guda da ya dawo cikinta bayan ya yi watsi da tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.
Tun kafin nan sai da ya kafa tafiyar siyasa ta TNM, inda ya bayyana cewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, babu abin da za su iya tsinana wa Najeriya.