Majalisar Kolin Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi feshin kashe kwayoyin cuta a wuraren ibada.
Kakakin Majalisar Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana bukatar yayin yaba matakin gwamnatin na sake bude wuraren ibada da aka rufe sakamakon cutar coronavirus.
“Muna maraba da matakin sannan muna shawartar masallatai su bi sharuddan da aka gindaya.
“Gwamnati ta tabbatar an kashe kwayoyin cuta a wuraren ibada,” inji shi.
- An sassauta dokar hana ibada a masallatai da coci-coci
- Malamai a Zariya sun koka da kwashe makonni 10 ba Sallar Juma’a
- Coronavirus: An shirya bude wuraren ibada da na shakatawa a Legas
Ita ma Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bakin kakakin shugabanta, Fasto Adebayo Oladeji ta yaba da matakin bude wuraren ibadan.
“Hakan ya yi daidai. Muna rokon Allah Ya amsa addu’o’inmu. Idan Musulmi da Kirista suka koma yin addu’o’i a wuraren ibada Allah zai kawo karshen cutar coronavirus.
A yau Litinin ne Sakatare Gwamantin Tarayya Boss Mustapha ya sanar da bude wuraren ibada bisa ka’idodin da kwamitin aiki da cikawa da shugaban kasa ya kafa domin yakar cutar coronavirus da amincewar gwamnatocin jihohi.