✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da Hushpuppi ya yi na karshe kafin Alkali ya aike da shi kurkuku a Amurka

Hushpuppi ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da wani abokinsa ya yada

Dan Najeriyar nan da ya shahara a shafin sada zumunta na Instagram wajen yin damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi ya ce gyara lebbansa ne abin da ya fara yi kafin ya bayyana a gaban kotu.

Ranar Litinin ce dai wata Kotu a Amurka ta yanke masa hukuncin daurin sama da shekara 11 a gidan yari, bayan samunsa da laifin damfara a kasashen duniya.

Sai dai a wani bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta, wanda abokin Hushpuppin din da ba a bayyanan wane ne ba ya dauka, babu alamar nadama a tare da shi.

A cikin bidiyon, an ga Hushpuppi yana dariya yana bayyana wa abokin cewa abin da ya fara yi kafin bayyana gaban Alkalin shi ne shafa man da zai sauya launin lebensa zuwa ruwan hoda.

Ya ci gaba da cewa dalilinsa na yin hakan shi ne don kada kamanninsa su bata wa Alkalin rai.

“Eh mana. Alkalin zai yi tunanin ina da kyau ne? Yaya kumatuna suke? Don haka ban son bata masa rai ko kadan.

“Gashi kuwa yanzu hankali kwance ina kwance abina ina latsa wayata”, in ji Hushpuppi a bidiyon yana dariya.

Wannan dai na zuwa ne bayan mutane da dama sun fara tunanin Hushpuppi ya saduda bayan yanke masa wancan hukunci.

%d bloggers like this: