Wata kotu a Amurka ta daure dan Najeriyar nan da ya shahara a shafin sada zumunta na Instagram, Ramon Abbas sama da shekara 11 a gidan yari bayan samunsa da laifi a harkokin zamba a kasashen duniya.
Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi an kama shi ne a Dubai, yayin da ya ke kokarin tsallakawa kasar Amurkan a 2020, a nan ne kuma Alkalin wata Kotu da ke Los Angeles ya daure shi, tare da umartarsa ya biyan Dala 1,732,841 ga mutanen da ya dmafara.
Bayanai daga kotun California sun ce, tun a watan Afrilun shekarar 2021 ne dai ya amsa laifin aikata almundahanar kudi, da yunkurin kwashe fiye da Dala miliyan 1.1 daga wani da ke kokarin ba da tallafi ga wata sabuwar makarantar yara a Qatar.
Mataimakin Daraktan da ke kula da rundunar tsaron FBI ta Los Angeles Don Alway, ya ce Hushpuppi dai ya yi fi ce ne a damfarar mutanen da suka fito daga kasashen duniya daban-daban musamman Amurkan.
“Abbas ya yi amfani da shafukansa na sada zumunta domin tallata wa duniya dukiyar da ya tara ta hanyar damfara, inda yake tura wa mutane sakon imel na bogi, da sauran hanyoyin damfara ta yanar gizo.
Hushpuppi ya nemi afuwar Alkali Otis Wright a wasikar da ya rubuta, inda ya ce zai biya wadanda ya damfarar, duk da Dala 300,000 kawai ya samu a damfarar da a ke zarginsa da aikatawa.