✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdulmalik ya aiko min da sakonnin ‘tes’ 17 —Mahaifiyar Hanifa

Ya turo min sakonni 17 yana neman kudin fansar Hanifa.

Mahaifiyar yarinyar nan Hanifa Abubakar da ake zargin malaminta Abdulmalik Tanko da kisanta, ta shaida wa Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako cewa Abdulmalik din ya tura mata sakon kar ta kwana na text har sau 17 yana neman kudin fansa daga wajenta.

A yayin zaman kotun na ranar Laraba, masu shigar da kara karkashin jagorancin Barista Musa Abdullahi Lawan, sun gabatar wa kotun mahaifiyar Hanifa mai suna Binta Sulaiman a matsayin shaida ta bakwai.

Bayan da aka nuna mata kayan makarantar Hanifa, Binta Sulaiman ta bayyana cewa ta gane wanda ta ce ita da kanta ta dinka su, lamarin da ya kai ga ta fashe da kuka har ya sa kotun ta dakatar da zaman na tsawon lokaci.

Haka kuma yayin da aka nuna mata wayarta da ke hannun ’yan sanda, ta bayyana cewa ta gane wayar inda ta kara shaida wa kotun cewa akwai sakonnin tes guda 17 da Abdulmalik Tanko ya aike mata a lokacin da yake neman kudin fansar Hanifa.

Sai dai fadin haka ke da wuya muhawara ta barke kuma masu gabatar da kara suka nemi a karanto ire-iren sakonnin tes din da Abdulmalik ya aike mata, inda Lauyoyin da ke kalubalantar karar suka yi suka a kan hakan.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa hakan ce ta sanya alkalin kotun Mai shari’a Usman Na’abba ya bayar da umarnin karanta sakonnin a gaban kotun wanda kuma hakan aka yi.

Daga bisani dai Alkali Usman Na’abba ya dage zaman kotun zuwa ranakun 12 da 14 ga watan Afrilun 2022 kamar yadda bangaren masu kariya suka nemi a sanya wata rana da za a dawo da mahaifiyar Hanifa don su yi mata tambayoyi.