Abdullahi Danbaba Hayatudeen wanda ake kira da Abdullahi Kwamanda shi ne Shugaban Kungiyar Gyara Kayanka na Tudun Jukun Zariya, mutum ne da za a ce ya yi nisan kwana, bayan da ya tsira daga hannun masu satar mutane da suka yi yunkurin hallaka shi har sau biyu. Yunkuri na baya-bayan nan shi ne wanda sai da aka kwara masa fetur za a banka masa wuta Allah Ya kwato shi daga hannun makasan.
Yanzu haka al’ummar Tudun Jukun da ke Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna suna ta turruruwa zuwa jajanta wa Shugaban na Gyara Kayanka wata kungiya mai taimaka wa ’yan sanda a kan tsaro.
A ranar Asabar din makon jiya ne wadansu mutane da ake zargin makasa ne suka sake sace Shugaban na Gyara Kayanka, kungiyar da al’ummar Tudun Jukun suka kafa, inda su yi yunkurin hallaka shi amma Allah Ya kubutar da shi kamar yadda ya bayyana wa Aminiya.
“Kamar yadda ka sami labari sau biyu ina shiga hannun makasa Allah Yana kubutar da ni, sai dai na farkon ya sha bamban da na biyu domin na farko muna zargi ’yan kungiyar matsafa ne suka sace ni shekara 13 da suka wuce bayan kwana tara da aurena. A lokaci na tashi daga Zariya za ni Kaduna ne domin in yi ban-gajiya ga wadanda suka zo daurin aurena. Bayan na sauka a garin Kaduna na hau motar zuwa Bakin Ruwa, Rigasa, daga wannan lokaci ban san abin da yafaru da ni ba, sai na tsinci kaina ne a wani gari wai Anacha ni da wani wanda tare aka dauko mu daga garin Kaduna amma ban san shi ba bai san ni ba, aka shigar damu wani gida aka hada mu da wadansu mutum uku wadanda ga dukkan alamu kamo su aka yi,” inji shi.
Ya kara da cewa “A lokacin da aka kai mu, su ’ya’yan kungiyar asirin sun mana cewa suna matukar bukatarmu wannan ya sa aka zo aka fara jawo ni saboda gardamar da suka ga ina yi musu don an umarce ni in tube kayan jikina na ki. Sun ce in tube wando na ce ba zan tube in yi tsirara a gaban mutane ba.”
Abdullahi Hayatuddeen ya ce daga nan sai suka kamashni da karfi suka cire masa sutura suka kada shi, suka dauko wuka suka fara yanka shi.
Ya ce ban taba shan maganin tauri ba, amma da suka yanka suka kara yanka wuyansa Allah bai kaddara wukar za ta yanka shi ba. “Bayan sun yanka ban yanku ba, sai suka dauko wata wuka mai ruwan zinari daga cikin wani ruwan magani suka kara yanka ni a kasar cibiyata, Allah bai kaddara zan yanku ba, daga nan sai suka sake ni aka kamo wanda aka kawo mu tare aka yanka shi.To ana yanka na ga jini na zuba yana kwarara a jikinsa, sai hankalina ya tashi na fara salati da addu’o’i da karfi, sai mai gidan ya z, ya ce a fitar da ni daga gidan,” inji shi.
Malam Abdullahi Kwamanda ya ci gaba da cewa daga nan sai suka dauko shi suka kai wani gari wanda aka shaida masa cewa sunan garin Asaba a nan suka yar da shi sai mutanen garin suka fito suka tsince shi aka nemi ’yan uwansa Hausawa aka kawo shi gida a wancan lokaci.
Game da sace shi na baya-bayan ne Abdullahi Kwamnda ya shaida wa Aminiya cewa “Na sha samun kiran waya cewa za a kashe ni ko za a yi mini kaza kasacewa dama duk mai aiki na jama’a irin wannan sai ya gamu da jarrabawa. Don haka wannan bai taba ta da min da hakali ba.”
Ya ce a ranar da lamarin ya faru yana tafiya za shi wani bincike a kan aikinsu sai “Wadansu masu mota suka biyo ni suka buge ni da mota, to suka ga na fadi a kasa sai suka fito don su dauke ni, na dauka za su taimake ni saboda sun kade ni, sai na ga abin ya sha bamban da haka. Sai muka kama kokuwa da su sai daya daga cikinsu ya samu wani abu mai jijjiga jikin mutum kamar wutar lantarki sai jikina ya mutu suka kashe min jiki suka dauke ni da karfi suka tafi da ni wani daji mai nisa ba zan iya gane wuri ba a yanzu,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Na samu wadansu da nake zargin an sato su ne da kuma wani mutumin Funtuwa wanda aka hada ni da shi aka daure wuri daya shi da na samu a wurin yana fada min cewa shi ma an kamo shi ne kuma sun harharbe shi amma bindigar ta ki kama shi kuma sun sassare shi wukar ta ki kama shi don haka suka ce kona shi za su yi. Ya nuna mini tokar gawar wadansu da aka kona a daren da suka dauko ni. Don haka da babbansu ya zo ya ce ina mutumin garin Zariya an zo da shi suka ce eh an kawo shi ya dauko hotuna ya duba ya ce eh shi ne don haka kashe su za a yi.”
“Bayan ya bar wurin ne sai na roki masu kula da mu cewa don Allah su ba ni waya in kira gida domin in yi musu wasiyya. Suka ba ni na kira wani daga cikin wadanda muke aiki tare na fada masa cewa ko an kira an ce aba da kudi kada a bayar domin ko kun bayar da kudin fansa mu kashe mu za su yi,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa ana haka sai aka zo aka kwance su shi da wanda aka hada su aka kwara wa shi na farko man fetur “Ni ma za a kwara min sai na buge jarkar na kai wa daya daga cikin wadanda za su kona mu naushi na fita a guje. Ina ta gudu suna bi na da harbi har Allah Ya tserar da ni na kwana ina tafiya har na zo kusa da wani dutse na fadi. Da gari ya waye sai na ji motsin mutane, sai na ga Fulani suna kiwo sai na daga musu hannu domin su kawo min dauki, kuma Allah Ya sa suka kira wadansu mutane da suke kusa da wani kauye wanda ban san kauyen ba da haka Allah Ya kubutar da ni,” inji shi.
Sai ya gode wa masu zuwa yi masa jaje kan wannan al’amari da ya faru da shi.
Mahaifiyar Abdullahi mai suna Hasana Mustafa ta nuna godiyarta ga Allah da ya kwato danta daga hannun miyagun mutanen.
A ofishin’ yan sanda na Danmagaji inda aka kai rahoton sace Abdullahi Danbaba, wata majiyar ’yan sanda ta shaida wa Aminiya cewa, sai da suka yi amfani da na’ura inda aka gano wurin da aka kai shi. Babban Jami’in ’Yan sandan yankin Daniel Moses Pam ya ce duk da Allah Ya kubutar da Abdullahi za su ci gaba da bincike sai sun kamo wadanda suka sace hi tare da gurfanar da su a gaban kotu.