✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yanke wa Abduljabbar hukunci ranar Alhamis

Kotun Shari'ar Musulunci za ta yanke hukunci kan kan zargin Sheikh Abduljabbar da yin batanci ga Annabi (SAW)

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano ta saka ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba 2022, domin yanke hukunci a Shari’ar zargin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) da ake wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Kakakin Manyan Kounan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano, Muzammil Ado Fagge ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Tun a watan Yuli na shekarar 2021 Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abduljabbar a gaban kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, bisa zargin sa da yin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da kuma tayar da hankalin jama’a.

Shari’ar dai ta dauki hankali sosai kafin wannan lokaci da aka tsayar da ranar yanke hukuncin da kotun za ta yi wa fitaccen malamin.