✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abba Gida-Gida ya daina riga malam masallaci —Ganduje

Har yanzu ni ne gwamna a Kano.

Gwamnatin Kano ta yi kira ga zababben gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi hakuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a.

A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa rudani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga ofishin zababben gwamnan a kan su guji janye daga filayen gwamnati.

Gwamnatin Kano ta ce abin da zababben gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokacin da gwamna mai ci har yanzu yake kan mulki, tamkar riga malam masallaci ne.

Ta kara da cewa kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba da zama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.

A Alhamis din da ta gabata ne, gwamnan mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wata sanarwa wadda ya bayyana a matsayin shawara, yana kira ga masu gine-gine a filaye da wuraren gwamnati, ciki har da masallatai da makabartu da makarantu da sauransu, su dakata.

Lamarin da ya janyo zazzafar muhawara da ka-ce-na-ce musamman a shafukan sada zumunta.