Assalamu alaikum masu karatu tare da fata nana lafiya? Bari in yi muku wata tambaya. Shin mene ne wadannan abubuwan da ke magance matsalolin fata? Lallai wadannan abubuwa ne, wanda a kullum mukan yi amfani da su a dakin girki ko kuma amfani da su a abinci. Idan aka koyi yadda ake amfani da su a fata, domin magance matsalolin fata, lallai ba sai an kashe kudi da dama ba wajen sayen magani. Ina son in gargadi masu karatu da su gane cewa a cikin abubuwan da zan lissafo, daya kawai ake so a riqa amfani da shi wanda ta dace da fatar mutum. Amfani da su gaba daya na qara haifar da wata matsalar fata. Yana da kyau a gwada amfani da su tsawon watanni biyu zuwa uku.
• Domin magance matsalar fata mai yawan saba ko masu samun barewar fata daga fuskarsu ko wata bangare a fatar jiki, sai a samu suga mai launin qasa da zuma da madara kadan yadda sugan ba zai narke ba, sai a shiga dirzawa a fuska ko wani bangaren da matsalar ta shafa.
• Qarin haske: idan fuska ta kasance tana yin baqi a sakamakon yawan fita rana ko kuma canjin yanayi, yana da kyau a kwaba ayaba, sannan a hada da zuma da kuma lemun tsami sai a riqa shafawa a qalla sau biyu a rana na tsawon mintuna ashirin kafin a kwanta barci.
• Sheqin fata: samin fatar fuska mai sheqi, sai an dage da cin kankana da kuma kwabata da cokali sannan a riqa shafawa a fuska ko jiki na tsawon mintuna talatin a qalla sau biyu a rana sannan a wanke.
• Tsagewar lebe: Iidan lebe na yawan tsagewa ko kuma bushewa, sai a samu man kwakwa da siga sai a dan diga man kwakwa da sukari kadan, sannan a shiga dirza sukari a lebe na tsawon mintuna biyu zuwa uku, sannan a wanke. A kasance yawan shafa man kwakwa a leben.
• Gautsin fata: gautsin fata na hana fata sheqi. Don haka, yana da kyau a kasance amfani da fiya da ruwan lemun zaqi. A kwabasu waje daya sannan a riqa shafawa a waje mai gautsin domin magance matsalar.
• Fesowar quraje: a kasance amfani da ruwan qwai ban da gunduwar sannan a riqa shafawa a fatar fuska a kullum na tsawon mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar kafin a wanke sau biyu a rana domin samun biyan buqata.