✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A zabge mabarnatan ’yan siyasa

A ‘yan kwanakin nan mafi yawan mutanen da muka yi gwagwarmayar kawo sauyi a karkashin tutar jam’iyyar APC, muna korafi kan yadda ’yan PDP da…

A ‘yan kwanakin nan mafi yawan mutanen da muka yi gwagwarmayar kawo sauyi a karkashin tutar jam’iyyar APC, muna korafi kan yadda ’yan PDP da suka kasa cin zabe suka sake zagayowa ta bayan gida suka mamaye mu. Wannan lamari da ya yi kamari domin uwar gidan shugaban kasa ta koka kan yadda wadanda ba su yi wa jam’iyya wahala ba su aka bai wa mukamai a gwamnati; sannan shugaban hukumar Kwastam Hamid Ali ya fito karara ya nuna cewa ’yan jam’iyyar PDP sun mamaye gwamnati.

Duk da cewa muna goyon bayan kalaman da wadannan jiga-jigai a cikin al’umma suka furta, amma ya kamata mu sani cewa, ‘idan aka samu dan PDP ko mai zakara ko wata jam’iyya da ta sha bamban da APC ya nuna kokarinsa da kyawawan dabi’u na ki da cin hanci da rashawa da bunkasa noma da ilimi, ina ganin bai dace mu hantare shi ba. Domin akwai ’yan Najeriya da suka fahimci irin sauyin da Shugaba Muhammadu Buhari ke fafutikar kawo wa domin inganta rayuwar al’umma da dawo da martabar kasar a idon duniya. Bisa la’akari da wwacdannan al’amura ya kamata mu lalubo mafita cikin masalaha.

Muma ’yan jam’iyyar APC sai mu duba dabi’unmu, inda aka samu baragurbi to mu nuna musu yadda za su gyara. Mutane da kuwa a tabbatar suna yi wa al’umma abin da ya dace in dai har ’yan kasar nan ne wajibi ne a karfifi gwiwarsu su kara himma da kwazo. Mun dai san wasu rikida suka yi daga wacccan jam’iyya zuwa wannan.

Abin damuwar anan shi ne mutane su rage tunanin cewa kowa ya yi wa jam’iyya hidima dole nee a saka masa, a’a. Haka kuma suma shugabanni ba ta kamat aa ce sun yi watsi da wadanda suka yi fafutikar kawo sauyi ba. Saboda haka nike ganin idan mutum kwararre ne a wani fanni na rayuwa, sai a duba kwarewarsa gwargwadon yadda zai iya bayar da gudunmuwa wajen ci gaban al’umma, wato likitan da ke da ra’ayin siyasa ba laifi ba ne a kai shi maakatar lafiya don amfani da kwarewarsa wajen inganta kiwon lafiyar al’umma; injiniyan da yake da kwarewa kan harkokin kere-kere ko gyaran na’urori, sai a tarairaye su yadda za su taimaka wajen bunsa masana’antu da samar da wutar lantarki da gine-gine. Idan aka yi wannan, wato amfani da basirar kwararru a fannonin ilimi, to kada a yi kasa agwiwa wajen waiwayar talaka, tunda daukacin al’umma su ake jan ragamarsu a kowane irin mulki.

Talakawan kasa dai babu abin da suke bukata da ya wuce a inganta hanyar neman abincinsu; a gyara hanyoyin sufurri, a samar da ruwa da wutar lantarki, uwa-uba a inganta noma da kiwo a wadata asibitoci da magunguna. Idan talaka ya samu kyautatuwar harkokin rayuwa ba lalali ne ka ji irin wadannan korafe-korafen ba. Don haka babbar manufar gwamnati dai kada ta wuce inganta rayuwar al’umma da cusa musu kishin kasa, ta yadda za su bi dokokin da aka shimfida. Na hani da umarni. Sannan a bai wa manoma taki, musamman a daidai wannan lokaci da akalar tattalin arziki kee karkata ga noma.

Ni dai a ra’ayina korar ‘’yan PDP daga gwamnati ba zai warware mana matsalolin kasar nan ga baki daya ba. Baya ma ga haka ina ganin akwai buktar jam’iyya ta nuna cewa duk wanda bai tabuka komai ba, wajen kyautata rayuwar al’umma a duk matakin wakilcin al’umma da aka zabe shi kada a kuskura a bashi tikitin takara kai tsaye; su ma jam’iyya ya kamata su yi kansu kiyamullaili su fitar da ma’auni kan al’amuran da suka shafi kyautata zamantakewa da bunkasa tattalin arziki da siyasa mai tsafta. Domin ta haka ne kawai za mu daina kyarar juna, mu rika ganin kyawawan dabi’un al’umma ta yadda za mu iya auna kimar mutuntakar da za ta bai wa mutum damar jan ragamar al’umma.

Al’ummmar kasar nan sun san wadanda suka sace kudin sayen makamai; sun san wadanda suka kwashi kudin gyaran filayen saukar jiragen sama; uwa-uba matar da ta kwashe kudin kasar nan lokacin da ta rike ministar albarkatun man fetur. Tunda daukacin wadannan mutane ’yan jm’iyyar PDP ne ko PDP ta ba su dama ai idan al’umma za ta yi wa kanta adalci sun san wadanda suka haifar mana da matsalolin da muke ciki a halin yanzu.

Koda shugaba Buhari zai tsame ’yan PDP wadanda suka tafka barna daga gwamantinsa, to ina ganin kada ta tsaya kansu tunda nufi ne na gyaran kasa, don ’ya’yanmu da jikokinmu su samu natsuwa. Saboda haka idan Baba ya kwararo ruwan tsaftace kasar nan, akwai bukatar ya umarci gwamnoni su ma su kwarara ruwan ya tsaftace mana duk wani dagwalon barna da aka jibge mana. Kai idan ta kama a yi doka duk wanda ya cutar da kasar nan kada a bari ya yi takarar kowane irin mukami. Idan kuwa hakan ba ta samu ba, to a umarci Hukumar Wayar da kan Al’umma ta kasa, wato NOA ta wayar da kan al’umma kan mutane da suka cancanta a zabe ssu saboda kishin kasa da kyawawan dabi’u a bin koyi ga al’umma. A zabge kowane mabarnaci ba tare da la’akari da jam’iyyarsa ba.

Ishak Hadeja Dutse, Jihar jigawa 08063638362