✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A yi wa Najeriya addu’a —Aisha Buhari

Allah Shi ne mafificin duk wani mai bayar da taimako.

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta bukaci da a yi wa Najeriya addu’a tana mai tunatar da cewa Allah ne kadai Mai iya jibintar lamarin dukkan halittunSa.

Aisha ta yi wannan kiran ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Lahadi, kwana daya bayan gudanar da Babban Taron jam’iyyar APC wanda tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam’iyyar mai mulki a kasar.

Cikin hotunan da uwargidan ta wallafa — wanda daya take sanye da mayafi da kuma alamar nuna damuwa a fuskarta— dayan kuma yana kunshe da sakon tunartarwa cewa “Allah Ya isar mana a dukkan komai, kuma Shi ne mafificin masu jibintar duk wani lamari.

“Allah Shi ne mafificin duk wani mai bayar da taimako kuma Shi ne mafificin dukkan wani mai bayar da kariya,” a cewar sakon.

Aisha wadda a kwanan nan rahotanni suk bulla cewa ta shafe kusan watanni shida a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa gabanin dawowarta Najeriya a watan Maris, a wasu lokutan baya ta sha fitowa karara tana sukar gwamnatin da mai gidanta ke jagoranta.

A watan Afrilun 2021 ne gwamnan Jihar Ekiti kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Fayemi Kayode Fayemi, ya bayyana Aisha Buhari a matsayin muryar wadanda ba a iya jin muryoyinsu.

Sakon da Aisha ta wallafa a ranar Lahadin na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da sukar tsarin yadda aka samar da sabon shugaban jami’yyar APC, wanda ake cece-kucen cewa babu maslaha kuma ba a iya sauran wadanda suka nemi kujerar adalci ba.